Sashe 169
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hama irin kishiyoyinnane marasa dadin kishi. Gata da masifar bin bokaye. Duk tabi ta tashi hankalinta akan cikin dake jikina. Wata rana da rikici ya haɗamu har cewa tayi in sha Allah sai cikin ya zama ajalina in mutu uban kowa ya huta. Wannan furucin nata ya haifar mata da fishin Yafendo da Hamma daya ƙwallafa ranshi akan cikin. Yaya Hamma ya fi sati yana fishi da'ita. Ni ko ko a jikina domin da Allah kaɗai na dogara. Kuma Hamma na zuwa wannan ƙauye wajen wannan malami yana karɓomun tofi ina sha ina shafewa a jikina duk daren Allah. Kasuwancin saida magungunan mata ya amsheni sosai a gaskiya. Sai kwana biyunnan dana lodo kaya sai naga yaƙi tafiya an barni da tulin kaya abinda bai taɓa faruwa ba. Abu kamar wasa ya zamana duk abinda na siyo saidai in yi asararshi. Hatta dilar kaya dana sake kuncewa wallahi sai kano na mayar ma Uwani da kayan banda asarar da nayi, ku har man shanu nake tarawa ranar kasuwa in kai ko za'a siya. Ba'a siya sai kace wacce ta kaɗe baƙar karya da baƙar mota. Sau biyu naje, zuwa na biyu harda kindirmon Nono naje mai kyau samanshi harda fatar mai kwance. Yaya Hamma bai ma fa san naje ba. Allah cikin ikonshi yadda na kai haka na jawo tsumman ƙafafuwana na dawo gida, abun bana lafiya bane A cikin watanni biyu da rabi saida na dawo nera biyar tawa wallahi bani da'ita babu da abinda na tsira sai shanu da awakaina wanda su kansu Amaduyal yace du basu da lafiya. Tunkiyata ma kasawa ta kusan yi aka saidata nera dubu takwas. Duka kuɗin na danƙama Dada nace ta ɗan dinga zara tana kashewa. Abinci dai suna samu tunda dama bani ke siya ba, ƙannena nice na zame musu makwafin Dada, dan sai ayi abu a cinye ma bamu faɗa mata ba, kanmu a mugun haɗe yake ga soyayyar juna. Abincin garata ya ƙare, zara bata barin dami. abincin mu kuma a ɗakin Hama yake kullum naje diba saita farfaɗamun maganganu da gorin abincin da nake bawa su Dada. Bana ko tankata ni takaina nake yi kuma da Allah na dogara. Yaya Hamma na roƙa ya gina mana rumbun da za'a dinga ajjiye abincin a ciki, banda rumbun iri da suke ajjiyewa, da buhunhunan masara. Allah ya taimakeni kuwa ya gina, sai na huta da hayagagar Hama. Sai dai tamun akan abinci da nake dafawa in kai gida. Da cikina ya kai wata huɗu ranar talata ranar awo kenan saina tambayi Yaya Hamma inaso in soma zuwa awo tunda cikina ya soma motsi, dake a ɗakina yake ranar, yana shirin zuwa gonane damina ta soma har an soma share gonakai ana jiran ruwa ya tsaya a soma zuba iri. Ya ɗakko nera ɗari biyar ya bani. "Kin ganta ita kaɗai ce a hannuna kiyi maneji dashi har kije ki dawo. Kudin cefanen da zan baki ma wallahi bani dashi dama ɗari biyar ɗince kaɗai ta rage mun." Murmushi nayi mishi nace. Dukkan tsanani yana tare da sauƙi. In sha Allah da zaran na haihu nima sai in dinga ɗaukar tallar nonon ina bin Baɗɗo muna tafiya. Babu komai" Wasu hawayene suka gangaromun da gudu, a hakan ma ina fatan inna ɗauki nonon a siya. Duk abinda na taɓa lalacewa yake yi. Hatta koyar da ɗalibai na sauke ma kaina, da ɗaya da ɗaya suka dena zuwa. Ashe camfani akayi a ƙauyen kunsan ƙauya da camfe camfe wai ni mai rariyar hannu ce. Da naji ragowar ɗaliban da basu dena zuwa ba saina sallamesu. "Ki dena kuka Jabu. Ba zata kai ga haka ba. Akwai alƙawarin dana ɗaukar miki da kikace mun kina da sharaɗi ke ba zaki yi tallar Nono ba. Ni kuma na ɗauki wannan alƙawarin. Daga gona zan shiga gari neman abunyi in sha Allah za'a dace ko na cefanan kwananki ake samu ina laifi" Kafin in tafi awonnan nayi kukan da har saida idanuna suka kumbura. Yafendo naima sallama na fita. Kai tsaye gidan Dada na zarce naje ɗaukar Hassana tai mun rakiya. Dada ta ɗakko ɗari uku ta miƙo mun" A'a Dada ni ban baki ba sai kece zaki ban in karɓa" Kallon tausayi tai mun tace. "Babu komai Jabu karɓi" Godiya nayi mata. Har munje ƙofar gida tace. "Jabu. Amaduyal ya sanar dake halin da ake ciki kuwa akan kiwonki kuwa?" Gabana ya faɗi, a raunace nace. A'a Dada wani abune" "Kuje in kunje kafin ki wuce gida kizo ina nemanki zamu yi wata magana" To Kawai nace mata muka kama hanyar asibiti. Mun sha gwajab_gwalab haka dai muka isa. Layin mata masu awo har bakin babban asibitin Girei mai suna. Girei teaching hospital. A lokacin kyauta ake raba kati komai ma daya shafi awo kyauta akeyi. Domin a hakanma ba wani zuwa asibitin daga cikin ƙauyuka akeyi ba. Sun gwammaci mace taita nakudarta har ta mutu ma akan su kawota asibiti. Ni dai ina zaune akan layi na yi tagumi ina tunanin rayuwa da irin halin da nake ciki. Sauƙina ɗaya babu abinda har yanzu ya canja daga so da kulawar da Yaya Hamma yake mun. Saima abinda yaci gaba, kullum a cikin rarrashina da ban baki yake. Ga rai daya ɗauka yasa akan wannan cikin nawa. Ɗan murmushi nayi na shafi cikin nawa daya fito sosai kamar wanda ya kai wata shida. Yanayin yana mun kama da yanayin cikinsu Taye da Kahinde. Sai wajen azahar aka kira sunana na bi matar data kira sunana a baya, ta bani roba naje nayo fitsari na dawo mata dashi. "Malama Jabu ai babu ciki a tattare dake. A text ɗin da mu ka yi miki na fitsari bai nuna mana kina da juna biyu ba. Amman bari mu miki text ɗin jini." Take jikina ya soma rawa zufa na keto mun. Ga motsin ɗa a cikina amman ace bani da ciki, ga ciki ƙato? Allah cikin ikonshi wallahi anyi text ɗin jini maganar ɗaya ce ciki dai babu shi. Sai janaral asibiti Adamawa suka turani jibi inje za'aimun sikainin. Ta yi rubutu a wata takadda ta bani. Da ƙyar na tashi na fito, cike nake da mamaki, fargaba da tsoro duka dai. Amman in naji motsin rai a cikina sai inga kamar dai basu iya aikinsu bane. Anan Girai na sai kayan miya, da kuka, da maggi. Muka hau akori kura zuwa Jabbi lamba. Gidan Dada muka shiga da sallama Amaduyal ma yana ciki da kuɗi a hannunshi yana ƙirgawa ga wasu ma a hannun Dada. "Adda kun dawo" Cewar Amaduyal. Wani yawo mai kauri na hadiya, da ƙyar nace. Mun dawo Amaduyal yau baka je kiwon ba?" Shiru yayi baice komai ba. Hassana ɗebo mun ruwa in sha ƙishi nake ji" Hassana ta kawo mun ruwa mai sanyi cikin kofi na shanye, Dada sai kallona take a mugun firgice nake. "Lafiya Jabu akwai wata matsalar ne?" A'a Dada gajiyace da rashin kyan hanya ya galabaitar dani" Yanayinta bai nuna ta aminta da abinda nace ba,ta dai mun sannu, kafin tace. "Jabu kinga wannan kuɗaɗe dubu ɗari biyu da sittin gasu. Kuɗin shanunki da awakanki ne. Kinga ga kaji can a bawo guda huɗu nasa an yanka su dan ko ba'a yanka ba mutuwa zasu yi. Ungo wannan kuɗin riƙe" Hannu nasa na amshi kuɗin ina murmushi kawai. "Jabu kisan kadarar da zaki siya ki ajjiye kar ki bari kuɗinnan ya lalace su kaɗai suka rage miki. Sannan inaso ki zama mace mai juriya da jajircewa, ki yarda Allah shi kaɗai yake iya ɗaurama bawa kaddara me kyau da marar kyau. Wata rana zaki huta. Kamar yadda kika sha wahala ni kika fitar dani a matsala. Kema in sha Allah zaki haifi waɗanda zasu fitar dake a matsala. Duk runtsi kar ki rabu da Hamma. Hamma yana sonki kuma zai iya zame miki garkuwa ko bayan raina. Kiyi haƙuri kar ki zargi kishiyarki hakan kar yasa ko bayan raina ki aikata mata wani abun a matsayin ramuwar gayya. Da sannu zata gurbe duk abinda ta shuka. Akan Hamma duk take wannan burinta ta fitar dake a ɗakinki. Ke kuma ki nuna mata kina ma Hamma son da sai dai mutuwa ta rabaku" Hawayen dake zuba a idona na share. Babu komai Dada, na kuma gode da wannan shawarar. Amman inaso zan ba Amaduyal ko da jari ne ya nemi wata sana'ar a cikin wannan kuɗin." "A.a riƙe kuɗinki ki nemi kadara ki siya. Zai yi noma kuma ya samu aikin tuƙa babur zai dinga jigilar shigar da mutane ƙauyuka" Kuɗin na raba Uku na miƙa ma Dada fur taƙi karɓa, haka dole na haƙura na saka kuɗin a jakata. Na zari wasu daga ciki na ba Hassana tamun cefanan tumaturi ta auno mun shinkafar Hausa da Maggi. Suma su Dada nai musu cefane nace su yi girki na basu kaji biyu. Hassana ta rakani har gida da kayan cefanan. Ina tafe kamar mahaukaciya har gidan namu na wuce tafiya fa kawai nake yi, sai da Hassana tace. "Adda kin wuce gidan fa" Kana na juyo naga zahiri na wuce gidan. Da Sallama a bakina na shiga gidan. Yafendo tana tsakar gida, ita da Yafendo A'i. "Jabu kin dawo" Cewar Yafendo A'i. Wajensu na nufa na zube a gabansu muka gaisa. "Ai ɗazu mun shiga wajen Adda Daso ma take sanar mana siyar da dabbobinki da akayi basu da lafiya. Allah yasa da abinda suka tare. Kinsan ba kowa kiwo ya karɓaba shi yasa. Naji kuma sana'ar taki ma jarin duk ya karye miki shima. Jabu kiyi haƙuri jarabawace. Allah daya baki shi zai kuma baki wani, ki ɗau dangana." Suka haɗu sukaita ƙarfafani sai na ji sanyi a raina. A ɗakin Yafendo ma nayi Sallah na kwanta a ƙasa sanyin na mun daɗi. "Ga madarar shanu ɗazu na tatso miki" Yafendo ta miƙo mun na karba ina sha suna hirarsu da fullanci. Allah yayi mun ƙwaƙwalwar saurin jin yare gaskiya. A halin yanzu abu ɗaɗɗayane suke faɗa wanda bana ganewa. Mayarwar ma inayi amman ba sosai ba dai. Sai da nayi la'asar na shiga ɗakina na gyara tas na fito. Kara naje nayo na hura wuta na wanke kajinnan tas na ɗaura a wuta. Na ɗakko dutsen niƙa na gwafe naita niƙa tumaurinnan dasu attaruhu nafi