← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 237

Sashe 75

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rana ma kina ganin lokacin Allah zai shiga ya fice baki yita ba. Wata rana ma sai dai ki rama sallolin cikin dare a kulle a ɗakin da aka baki a matsayinki na ƴar aiki." Jikinmu na rawa cike da tsoro da tsinkewar zuchiya muka fice a ɗakin, kayanmu da jika. Haka aka turbutsamu a mota, wasu akan cinyar wasu. Duk wanda na kalla sai inga tana share hawaye, imma da mayafinta, imma da gefen zaninta. Zukata sun shiga damuwa da ruɗu. Wani gida aka kaimu, akaita mana aune, aune, bamu muka gama ba sai yamma lis. Basu bamu abinci ba, an dai raba mana ruwa munsha. Ɗakinmu muka tura muka shiga. Babu kowa a ɗakin, katifun dukka suna jingine a bango. Durƙushewa nayi ƙasa na sau kuka mai tsuma zuchiya da gangar jiki. Uwani na jan majina tasa hannu bibbiyu ta ɗago ni. "Iyabo tun a itofiya jikina ya mutu. Amman sai ƙara sama mana ƙarfin guiwa nake yi. Hankalina bai kai ƙololuwar tashi ba sai da muka shigo ɗakinnan mai kama da kabari. Muna cikin tsaka mai wuya a ƙasar da ba uwa ba uba, ba dangi." Kukane yaci ƙarfinta. Uwani mu dokara ga Allah. Allah ya ga xuchiyarmu mu neman kuɗi muka zo yi. Amman na fahimci kamar bayi haka aka ɗauke mu. Shawarar da zan baki, mu kai kukanmu ga Allah kawai. Da zamu samu hanyar komawa gida Najeriya ma da mun koma" Taraliya ce ta turo ƙofa, hannunta riƙe da gurasa kamar dai irin wadda aka saukemu da'ita. "To Wallahi kar ku sake ku sake ambaton Najeriya ma. In kuka kuskura wannan kalmar ta shiga kunne abokan zamanku, zasu isarma da Hajiya Babba. Ba zaku ji da daɗi ba. Sannan ku dena damun kan ku, ku da za'a tura gidan aiki. A can ɗaki sukutum za'a baku ku kaɗai a ciki. Kuma sai abinda kuke son ci zaku ci. Wannan zaman na ɗan lokaci ne. Ku dai Allah ya taimakeku ku samu shigewa da wuri. Dan naji Hajiya Babba na maganar gobe za'a soma raba ƴan aiki. Ku zauna kuci abincinku." Godiya Uwani tayi mata, har zata fita uwani tace. "Wai irin abincinnan kullum ake ci ne? Sannan wannan yayi mana kaɗan mu biyu" Dariya tayi bata ce uffan ba ta fice ta barmu a tsaye jigum. Jiki a saɓule muka rama sallolin da ake binmu. Muka lasa wannan abinci dan sai dai a kirashi da lasawa kawai. Muna zaune kowa dai da tunanin daya addabi zuchiyarshi. Yaya Hamma ne ya faɗo mun, dole na ɗan murmusa harma naji kwaranyar wani ruwa mai sanyi a zuchiyata. "Uwani ya kamata mu tambayi land line ɗin da akace akwai a ko wanne ɗakin ai. Ko dan ki samu ki kira mijinki ki sanar mishi isowarmu ko? Nima inason in kira Burodami in sanar musu da saukarmu" "Hmmm Iyabo mu nutsa mu gane kan gidan tukunna, kinganni yanzu haka yinwa kamar zata kasheni wallahi, gashi jikina ko ina ciwo yake yi mun kwanciya zanyi ko zan iya runtsawa a wannan halin da muke" Katifarta ta yar, ta ɗaura jakar kayanmu a katifarta, dan babu waje, kowa da kayanshi yake matashin kai. Ni dai ina zaune in tuno Dada, in Tuno Gwadabe, in tuno Ƴaƴana, in tuno Yaya Hamma da kuma Daso data haɗa zuchiyata da fargaba. A wajen a zaune bacci ya kwasheni ban sani ba kasancewar jikinmu a nune yake sosai, ga yinwa sai ta galabaitar dani. Allah cikin ikonshi sai da Asuba na farka, a ƙasa na kwana abina. Matan ɗakin namu wasu na kwance sunata baccinsu, yayinda wasu kuma suke Sallah, cikin masu Sallah harda Ƴar Ɗas, abunda ya bani mamaki shine banga Ƴar Ɗas da mayafi ko hijabin Sallah ba, banga kuma wannan yala_yalan gashin dana gani a kanta jiya ba, sai suma irin ta maza. Da Ɗan daudu muka kwana muka tashi ni Iyabo?" Na furta a zuchiyata ina mamaki, raɓewa nayi ta bayanshi na wuce zuwa toilet na ɗauro alwala. Ni dai har na idar da sallah ban dena mamakin Ƴar Ɗas ba. Sai hirarta take yi da mata ana tafawa, gata da barkwanci sosai. Ni dai naga matan ɗakin daga wannan mu ganta ta shigo da tea da biredinta, sai muga masu kaza gashasshiya, da masu wata doguwar shinkafa wacce ni tunda uwata ta haifeni banga shinkafa da kyau da tsarin wannan shinkafa ba, gashi taji naman kaza, ƙila itace shinkafa kaza da muke jin labari. "Bayin Allah ni ban gane ba tambaya ce dani dan Allah" Cewar Uwani data tashi tsaye. Ƴar Ɗas ta mike ƙugu a hannu yace. "Na taɓoki da alheri wai kishiya ta taɓa kishiya da bakin wuta. Faɗi tambayarki in rabtaɓo miki amsa, dan dana ɗumama cikina da kaza da laban kwanciya zanyi sai azahar kuma" Uwani tace. "Mu tunda muka zo wata bushasshiyar gurasace ake bamu, da wani romo da bamu san na meye ba. Bugu da ƙari ma ba isarmu yake yi ba. To sai kuma naga ku ko wacce da abinda ta saka a gaba tana ci, muna son ƙarin bayani." Ni kaina da Uwani bata yi musu wannan tambayarba, da ni zanyi musu. Yinwa tana addabarmu ainun, har ƙirjina ya soma nauyi. Ƴar Ɗas ya doki cinyarshi yayi juyi da ihu kafin yace. "Wannan gurasa da romo duk muma mun cita kafin mu yage rigar bauta, mu sa ta ƴanci. Duk wannan kayan ci na albarka da kike ji da gani, ko wacce da guminta na halak ta siya. In baki da kuɗi cin gurasa dole, batun ƙoshi kuwa kima fita zancan wannan. Kuma anan ba mai taimako wani, ko wacce ƙasarta ta baro ta fito biɗar kuɗin halak" Ɗayar matar mai Suna Madina ta dubemu ta ɗaura mana da cewa. "Idan kuka ƙara haƙuri da sannu komai zai wuce muku. Wuyarta ku soma aiki, kuɗi kam sai dai ku tura gida ma, abinci sai kun ture. Kunga irin baƙar azabar ni dana sha kafin in samu gidan aiki? Hmm abun yana da munin da ina faɗa muku zai karya muku zuchiya. Ku dai kuyi ta yin adda'a shine kawai" Taraliya ce ta miƙo mana wannan gurasa ta masifa. Sai dai yau matan ɗakinmu sun taimaka mana anyi mana karo_karo na abinci shine muka samu muka ji dama_dama. A taƙaice dai munfi kwana goma muna zaman jiran a kaimu gidan aiki. Anata ɗauki ɗaɗɗaya. Uwani da ƙyar ta samu lambar hajiyarsu ta shiga ta sanar da'ita isowarmu, sai ranar hankulansu suka kwanta da suka ji muna cikin ƙoshin lafiya,. A ranar aka tafi da Uwani gidan aiki, ranar nayi kuka kamar raina zai fita. Itama tana wannan kukan aka fita da'ita. Ni kaɗai na wuni ƙwalam a ɗaki, sai da nayi la'asar ne na shiga ɗakin dake jikin namu na tarad da su Hadiza suna ɗaki suma a zaune suna ɗan taɓa hira a tsakaninsu. "Iyabo kin leƙo ne, ina Uwani na ganoki ke kaɗai?" Cewar Hadiza. Tare da'ita muka tawo daga Kano. Sai da na zauna kana nace. Uwani ta tafi gidan aiki Hadiza" "To nayi mata barka wallahi muma nan duk zaman jiran hakan muke yi. Duk da ance aikin gidan larabawa ba ƙaramin aiki bane na azaba. Wasu fa wai har dukansu akeyi a gidan aikin." Idanu na zaro nace. "Yanzu Hadiza da girmanmu sai a kamamu da duka?" Dariya ma maganata taba ƴan dakin. Hadiza tace. "Hmmm Dattijuwar da take bamu wannan labarin kinga fa katifarta" Ta nuna mun katifarta a jingine" "Har bayanta ta nuna mana duk shatin bulala. Wannan dalilin ne yasa ta baro gidan aiki tana buƙatar a sauya mata gidan aiki. Duk matan dake cikin ɗakin ku fa da yawansu matsala suka samu a gidan aiki shi yasa kika gansu, za a nema musu gidan aikine" Ni dai jikina du yayi sanyi sosai. Na dubi Hadiza nace. In babu damuwa zan dawo ɗakinku Hadiza, can ɗakin namu basa zama, in suka fita sai dare, wasu ma sai su kwana biyu basu dawo ba" "Jeki maza ki ɗakko kayanki kinji, ai sai abun yayi miki yawa." A ɗakin su Hadiza kwanana biyar. Naji labarai masu tayar da hankali, da irin matsalolin da baƙaƙenmu suke fuskanta a gidajen aiki iri daban_daban kuma masu haɗarin gaske. Nifa tun daga Itofiya na soma ɗan daka ce ban baro ƙasara Najeriya ba. A ranar dana cika kwana goma a ɗakin su Hadiza nima akace in haɗo kayana waɗanda zasu ɗaukeni aiki zasu tafi dani. Hawaye na soma zubarwa da girmana, na suri ledar kayana, duban su Hadiza nayi da muka shaƙu a kwanaki gomannan nace. Allah ya sake sada fuskokinmu da Alkhairi, ni na tafi, ku taya ni da adda'a nima zan dinga yi muku" Ina kaiwa nan Taraliya ta figi hannuna zuwa wajen mota. Wata balarabiya da mijinta na gani a gaban mota, ni kuma Taraliya ta dannani a gidan baya. Motarnan na soma tafiya na runtse idanuna hawaye sai kwaranya yake yi a idanuna. Tafiya muka yi mai yawan gaske zuwa wani garin kuma. A cikin katafen wani ƙerarren gida motar ta tsaya. Ni dai ganin sun fito, nima saina ɓalle murfin motar na fito. Balarabiyar ta dubeni tace dani. "Yalla" Zungui_zungui dai haka naita binta a baya. Muka shiga wani ƙatoton falon da ko a mafarki ban taɓa ganin irinshi ba. Garjejen falone jere da wasu jajayen kujeru marasa ƙafa, duk da na kasa tantance kujerune ko fululluka manya aka jejjera oho. Duk girman falonnan kafet ne mamala a ciki, ga taushi, falon sanyi da ƙamshi yake fitarwa, ga matattakalar hawa bene daga can gefe, ga ɗakuna kusan goma a cikin falon. Ni dai ina biye da'ita zuwa wani ƙaramin ɗaki dage jikin matattakalar hawa bene daga ƙarƙashi haka. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin tayi, da sauri wata dattijuwa baƙar fata ta buɗe, sai na ganta da atampa a jikinta, kuma tayi mun kama da Bahaushiya. Da larabci wannan balarabiyar tayi mata magana tana nunani halamar dai bayani take yi mata a kaina. Tana gamawa ta haura sama abinta. Wannan Dattijuwar tace.."Sannu baiwar Allah, da ganinki ƴar ƙasata Najeriya ce ko?" Tana faɗar haka saina fashe da kuka. Hannu tasa ta jawo ni cikin ƙaramin ɗakin. Mai ɗauke da gado mai hawa biyu, da katifa a jingine a gefe, sai tulin kayan sawa. A bakin gado ta zaunar
Chapter 75 · 0% Book details