← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 237

Sashe 150

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

tafi rakashi yace mun daga nan zai je yaba Yafendo haƙuri akan laifin da ya aikata. Kuma ya bata haƙuri Hama ta dawo ɗakinta. Ruwan tea Uwani ta dafo mana muka baje tsirannan. "Iyabo naga akwatin aurenki a mugun yashe. Nace kyautar da kayan kika yi, kome kikayi ke ko da su?" Nadai san kala huɗu kika bani in dinko miki, kuma na tawo dasu ma an daɗe da ɗinkawa. Mamaki dam fuskata na dubeta. Bance komai ba na miƙe naje na buɗe akwatunan kusan rabin kayan babu. Da hanzari na buɗe sib na ɗakko akwatin ƙarfen da kuɗina suke ciki. Dama tunda na ɗakko naga kwaɗon a ɓalle gabana ya faɗi. Babu ko ficika a ciki. Salati kawai na shiga jejjerowa ina jijjiga kai Hama naga halama so take ta sabauta mun rayuwata. Uwani ce ta iso inda nake da sauri. Uwani harda kuɗaɗena masu yawa duk kinga an kwashe mun. Wallahi nasan kuma Hama ce zata yi mun wannan aikin. Har kayan akwatinma itace zata kwashe. Illar rashin ƙofa kenan. Dole Yaya Hamma yaimun ƙofa gaskiya. Yanzu Shikenan fa ta kassarani gabaki ɗaya jarina ya ruguje murus" munfi minti talatin a Zazzaune muna jimami. A cikin wannan halin Yaya Hamma yazo ya samemu, cikin tashin hankali yake tambayar meke faruwa. Uwani ta miƙe ta nufi hanyar waje. "Matarka zata maka bayanin abinda ke faruwa. Ni kam saida safenku." Tana fita ya dawo kusa dani, ganin duk ya ruɗe na fashe mishi da kukan baƙin ciki wanda ya sake sukurkutashi. Sai kuma ya mugun bani tausayi har sauya launi idonshi yayi. "Jabu kiyi haƙuri in akan abinda nayi miki ne. In akwai wani abun ki sanar dani dan Allah" Nan cikin kuka na faɗa mishi satar da akaimun. Kai tsaye ban halaƙanta satar da matarshi ba. Kai ya girgiza yace. "In dan akan wannan ne kike wannan kukan gashi ke ba cikakkiyar lafiya ba. Kiyi shiru ni zan biyaki kuɗin da aka sace miki, da kuɗin kayan da aka sace mikin Shikenan in anyi hakan kukan zai ƙare? Ko nawa aka sace miki kuɗinki bazai yi ciwon kai ba zan biyaki" Faɗawa nayi ƙirjinshi ina share hawayena tare da kuma shigewa jikinshi. Danna lura saifa nayi da gaske zan iya zaman aure a ƙauyannan. Jibi yarinya ƴar ƙauye duk ta hautsina mun lissafi, ta kwance mun notukan kayina. A wannan daren ni naga soyayya da tattali ra'ayul aini. To anan nake cewa sai Allah ya kaimu ranar Talata kuma dan ranar monday akwai hutun maulidi oga na gida ba zaku samu posting ba sai ya koma aiki talata. MRS BUKHARI
Chapter 150 · 0% Book details