Sashe 207
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajja Mama ina zan bar yarana to?" "Zaki iya tafiya da kayanki. Zaki iya bama su Hauwa ruƙonsu sai wanda kika zaɓa amman zaki je dole. Hmmm yarinya baki san waye Dr bane, ni wallahi dama naji yace wai takanas wajenki zaizo sai da na girgiza. Zaki iya komawa bakin aikin ki. Kije shagon Bala ki karɓo doguwar riga mai mayafi ƴar kanti da takalmi kice nina aikoki. In kika dawo zaki ƙirga kuɗinshi ki bani. Ki san inda zaki nemi kuɗin da zaki yi mishi girki bette iya bette" Ni dai sukuku na fita na nemi waje sharab na zauna a gefen Hauwa dake ba biyu abinci a baki. "Lafiya Iyabo naga jikinki a mace?" Labari na kwashe na basu ita da Batula yadda mu ka yi da Hajja Mama. Sai naga sunyi dariya harda shewa. Hauwa tace. "To shine duk jikinki ya mace. Ke baki san babban kamu kikayi ba indai Dr na Hajja Mama wanda na sani ne. Harga Allah banyi tunanin a cikin irin wannan layin zai iya ganin mace har yayi tattakin zuwa takanas ba. In dai kuɗin abincine faɗi me kike son girka mishi sai in rakaki mami market mu siyo zan ara miki. Daga nan mu biya wajen Bala mai shago." Hotel fa Hauwa, da yarana kawai sai aga na shige zangon baƙi?" "Ke dallah baƙauya ku wai me kuka ɗauki hotel ne wajen buɗala kaɗai kome? Ke da bakinki kikace zangon baƙi ba zangon buɗala ba. In ba zaki ba sai kije ki sanar mata ai" A_a Hauwa to naji muje mu yi cefanan." Murmushi tayi tace. "Koke fa Iyabo. Da kinata zaune kin ƙi ba kowa dama. Dubi wancan bazawarin na ɗakinsu Habu yadda yake maitar kallonki da son shiga shirginki ke ko ko a jikinki ma. Kasuwa muka shiga muka sai kaza, mai, maggi, shinkafa, sai kayan miya, da kayan lambu. Jallof ɗin shinkafar data wadatu da kayan lambu nayi mishi. Kazar kuma na soyata na sakata a jajjagen attaruhu da albasa. Hauwa ta rakani wajen Bala, ita ta tayani zaɓar rigar ni dai gabana sai faɗuwa yakeyi. Kafin magriba na shirya tsab Hajja Mama ta bani wasu kuloli masu kyau na zuba abincin, na jera duk abinda ake buƙata a 🧺 basket. Ina yin sallar magriba naji Hajja Mama na waya dashi akan ya iso yana hotel ɗin daya sauka. Ga Alhaji Ghali yana ƙofar gida zai kawo ni. Wallahi da ƙyar na idar da sallar, ina idarwa na shige banɗaki a guje sai gudawa. Ina jiyo Hajja Mama na zage_zagenta ni dai jikina na rawa na fito. Ina ji ina gani na fita na bar yarana. Hauwa ce ta biyoni da gudu. "Iyabo kifa saki jikinki meye haka tun a gida kinga yadda jikinki ya mutu kuwa?" Ni dai bance da'ita komai ba nayi ficewata a bakin motar Alhaji Ghali na tadda Batula sunata hira da dariya. "Yauwa matarmu masha Allah. Muje ko? Batula mu sai mun dawo" "Iyabo sai kun dawo, kya gaishe da Dr ɗin" Kai na ɗaga mata kawai, na shiga bayan mota tare da basket ɗin. Muna tafe gabana na tsananta bugu har Allah yasa muka isa HOTEL ɗin. Get ɗinshi a wangale dama yake. Ni dai ina biye da Alhaji Ghali a baya. Basket ɗin abincin na hannunshi har muka tsaya a daidai room 11. Ƙofar ya ƙwanƙwasa daga ciki muka jiyo ance. "Ghali shigo mana, ai tun isowarku na hangoku ta taga" Ghali na gaba ina biye dashi kaina a sauke" "Madam ga bakin gado yi zamanki bari in watso ruwa in fito. Alhaji Ghali zaka jirani ne?" "A_a na cika aikina sai mun haɗu gobe kawai" "To ni gobe jirgina 7 na safe zai tashi kasan sabida inga gimbiyane nazo ai.' Ni dai ina ɗofane a bakin gadonnan kaina a ƙasa ina jinsu, amman wallahi har lokacin bansan kalarshi ba dan ban yarda na kalleshi ba. "Gimbiya bari in sallami Ghali in ba haka ba bazai barni ba kinji?" Yayi magana cikin taushi. To babu damuwa " Kaɗai na iya cewa suka sa kai suka fice. Sai lokacin na sauke ajjiyar zuchiya na ƙarema haɗaɗɗen ɗakin kallo. Wayarshi aketa kira tunda suka fita wayar na gefena naga an rubuta lovi_lovi matarshi ce kenan take kira. Da sallama ya shigo ɗakin ya zauna akan ƙaramar kujera. "Gimbiya bani wayarnan yara sai damuna da kira suke yi" Wayar na ɗakko na miƙo mishi sai naga hannunshi fari sol sosai. Ni dai inaji yana waya da matarshi sai lokacin na samu zarafin satar kallonshi. Dattijone ba sosai ba, gashin ƙasumbarshi, da gemunshi rabi fari rabi baƙi, haka ma sumar kanshi. Saye yake da shadda waganbari mai ruwan makuba ta amsheshi sosai. Yana gama wayar yace. "Kin ƙi ɗagowa ki kalleni ma. Wai a haka zamu yi zancan kenan uhm Iyabo" Ni dai nayi murmushi sai na ɗago muka haɗa idanu, nayi saurin kawar da kaina. "Masha Allah. Ina godiya da Allah yasa banyi fatali da zaɓin Ghali ba. Da farko sunana Dr Usman bin Usman. Shekaruna Hamsin da shida. Matana biyu yarana huɗu biyu maza biyu mata. Ni likitane ɓangaren masu matsalar ƙwaƙwalwa. Ni ɗan garin Gombe ne bafulatanin usil. Zan so ji daga gareki. Meya fito dake a gidan mijinki ke? Kaina na sauke ƙasa kawai. Sai ya jawo baske ya zuba abinci, ya yi loma ɗaya kafin yace. "Ke nake saurare" Komai a nutse yake yi sosai. Yana magana yana lumshe idanunshi. "Sunana Iyabo kamar yadda yazo maka. Ina da yara biyu Hassan da Usaini shayar dasu nake yi. Abinda ya shafi rayuwa ta baya kuma babu abinda zan iya sanar maka kayi haƙuri dan Allah" "No kar ki bani haƙuri babu komai ai. Koma dai menene ina sonki a hakan. Ni kuma aurenki zanyi mu ba yara bane balle mu tsaya wani zance ko waye_waye. Bama ni da lokacin hakan sam. Ɗan Lokacin nawa iyalina nake bama suma su ji daɗinsu. Da fatan nayi miki an amshi tayina, in kuma kina da wanda kike so kar ki ɓoye mun komai Iyabo danni ban iya son abuba in ina so" A_a banda kowa. Kuma na amshi tayinka Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi. Sai dai yarana ƙanane sosai Mama suke sha" Dubana yayi yana murmushi yace. "Hakan matsalane a wajenki? Ni a wajena babu wata matsala. Amman bansan mai kike tunani ba uhm?" Numfashi naja nace. Dama naso in yayesu ne tukunna dai. Sannan ina da tambaya" Dariya yayi, sai da ya cinye abincin bakinshi kana yace. "Yi tambayar tukunna' Me yasa kake sona, sannan mai yasa har abokinka yasan irin macen da kake so?" Dariya yayi sosai. Ni kuma saina shagala da kallonshi. Dattijantaka tayi mai kyau, nutsuwa ya ƙara haskashi. "Iyabo kenan. Ghali abokinane sosai. Yanayin aikine yasa bamu fiye haɗuwa ba. Ɗakinmu ɗaya a makarantar bording da muka yi. Tun muna wannan matakin yasan inason mace mai jiki, kuma ƙabila. Matana kab babu bahaushiya. Sai dai basu da ƙiba su gaskiya, yanzu ne dai na samu cikar burina Kar kiyi tunanin ko sha'awar jikin nake yi. A_a Allah ne shaidata halittatace mai son mace mai ƙiba. Zancan son mace ƙabila ya ɗakko asaline babba wanda na miki alƙawarin haɗuwa ta gaba zan faɗa miki. Nagode da abinci. Muje in kai ki gida gobe zan koma Gombe. Miƙewa nayi da sauri damar kamar a ƙaya nake. Muna fita na sauke wawuyar ajjiyar zuchiya. Muna tafe a jere ga basket ɗin abinci a hannunshi har gaban wata baƙar mota. Da kanshi ya buɗe mun murfin ƙofar har saida na shiga ya kulle kana ya zagayo ɓangaren matuƙi ya shiga ya ja motar. "Ina wayarki in saka miki lambata?" Ƴar ƙaramar posar dake hannuna na zaro wayar na miƙo mishi. Wayar yaita jujjuyawa dai, bai bani ba bai saka number ba har muka iso wani shopping moll babba. "Ki jirani ina zuwa, ko kina so ki bini?" A_a zan jiraka" murmushi yayi mun kawai ya tafi ya barni. Idanuna na lumshe. Indai miji nake nema to Usman bin Usman yayi. Allah yasa ba yaudarata zaiyi ba. Duk da dai bai taɓa jikina ba sam. Ina wannan taɗin zuchin na hangoshi da ledoji riƙi_riƙi ya jibgesu a bayan mota ya shigo. "Aimun afuwa inna daɗe" Dariya kawai nayi ni dai muka kama hanyar gida motarshi har ƙofar gidan. "Bana so mu rabu, inaga zan ɗaga tafiyar sai jibi, gobe zan zo in ɗaukeki da yaran muje yawo ko?" Idanuna na lumshe. A zahiri Usman yana da baiwar nutsuwa, sannan ni dai lokaci ɗaya na kamu da sonshi, kundai san halin zuchiyata itance ba'a canjata ba. To Allah ya nuna mana goben. "Goben zan sake sanar dake abubbuwan daya dace ki sani a kaina ko?" Kasa magana nayi dan sai kallona yake yi. Wayarshi ya ciro ya cire sim ɗin ya mayar da sim ɗina ciki. Da wayar tashi da tawa wayar, da katinshi duk ya miƙo mun. "Ga katina akwai lambata a jiki. Ga wayata kiyi amfani da'ita, ni nayi amfani da ɗayar." Hannu yasa a aljihu ya ciro rafar ƴan ɗari bibbiyu sababbi ya miƙo mun rafa ɗaya. "Wannan kuma sai ki loda kati. Ga tsarabar ƴan biyu a bayan mota bari in tayaki fitowa dashi. Amsar kuɗin nayi nayi godiya sosai. Har ƙofar gidan ya rakoni da ledojinnan. Hannu nasa na amsa nace. Allah ya tsare hanya, saida safe nagode " Ban jira amsarshi ba na wuce harna kusan ƙulewa saina juyo. Usman na tsaye ya nannaɗe hannayenshi a kirjinshi yana ta aikin kallona. Baka tafi ba?" "Sonki ya hanani tafiya. Bazan ɓoye miki ba kin samu gurbi mai kyau a zuchiyata. Ina fatan za'a tausaya mun" Murmushi nayi mishi nace. Baka da matsala zuchiyarka tazo hannun da akasan mutuncin so. Ka daure ka tafi dare nayi saida safe." Na jiya na shiga cikin gida da sallama. Duk suna baje a tsakar gida na shigo kiki_kici da ledoji. Batula da Hauwa suka yo kaina da oyoyo harda tafi. Duk suka amshe ledojin suka nufi ɗaki. Da sallama na shiga ɗakin nima Hajja Mama na waya na zauna a gabanta. "Kar ka damu Dr yadda kake so ai haka za'ayi likita bokan turai. Gata ma yanzu ta shigo bari in turota" Ƙit ta kashe wayarta.. "Tashi maza Dr na waje wai kinyi