← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 237

Sashe 40

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dai ina raɓe a bayan Hama tsoron shanun nake yi, ina dai kallo Boɗɗo na tatso nonon wata farar ƙatuwar saniya mai baƙin ido, ita kuma Hama tana dai ta shafama wannan saniya magani a duk jikinta, kuɗa sai damun saniyar suke yi tana ta kaɗa kanta. Fitowarmu daga cikin garken kenan sai ga su Cubu sun shigo gidan, amman ta wata ƙofa da ban ba ta ƙofar da muka shigo jiya ba. Idanu na ƙura musu, su basu da fari can ɗinnan . Yanda duk suke kallona a kunyace su nai mun kallon so da ƙauna shi yafi komai burgeni sosai. A barandar dake ƙofar bukkar Boɗɗo muka zauna. "Adda Jabu wadannan duk ƙannenki ne iyakarmu mu huɗu ne, shi Amaduyal shi baya nan. Iyakar yaran Dada kenan, nasan baki san iyakarmu ba, kamar yadda suma duka babu wanda ya sanki sai ni, nima saninna gani ɗaya ne." Daɗi ya lulluɓeni ganina a cikin ƴan uwana cikin Dadana, kuma sai kirana suke da Adda Jabu fuskokinsu da zuchiyoyinsu a cike da fara'a. Nawa bazai ma musaltuba. Tuwon farar masara aka kawo mana ɗumame da baƙar miya kamar kwalta, ko miyar meye wannan oho, sai madarar shanu mai zafi, tuwon sai ƙamshin man shanu yake yi. Loma ɗaya da nai karambanin sakawa a bakina da ƙyar da maƙyarƙyata na iya haɗiyewa tare da danneshi da Madara mai ɗumi. Muna zaune a wajen ina ɗan musu tambayoyi suna bani amsa, wata hausar ma da ƙyar suke fahimtar me nake nufi sabida tayi musu girma. A bakinsu naji ai kullum Dada tana zuwa cikin bini kai nono, fura, da man shanu. Tsawon tasowarsu da hakan suka san iyayen nasu, su kuma yara maza kiwon shanu suke fita yi, in suka girma har gari_gari suna iya fita kiwon shanun. Boɗɗo tace. "Ko ni ma kullum ina fita tallar nono, mu da kuɗin wannan nonon muka dogara, bamu da wani abunyi sai kiwo. In mace ta siyar da nono, a ciki zasu ci su sha, su yi sutura, har su tara kuɗin magani in wata saniya ba lafiya a nema mata magani dashi. Ƴan mata kuma da ba aure a kansu, da kuɗin tallar nononsu ake yi musu kayan ɗaki da komai da komai, wata ma har ta tara kuɗi itama ta sai ɗan maraƙi da haka har su zama garken da yaranta zasu ci gado suma. Matan ma a wasu gidajen suna fita kiwo. Ko su Cubu suna zagayawa amman da awaki ba shanu ba." Jigum nayi ina ta kallonsu jikina a mugun mace. Dama duk uba uban tsarabar da Dada take yi mun in zata zo ganina da kuɗin tallar nono take yowa?" Sai naji zubar hawaye masu zafi, tare da saka ɗamarar sauya ma Dada wannan rayuwar tallan da izinin Allah. Ana cikin haka sai muka jiyo sallamar Dada ita da wasu mata su su biyu, sai namiji guda ɗaya sun shigo kai tsaye kasancewar gidan duk dangin junane. Ɗakin Yafendo Kaɓoji suka nufa, mu kuma muka mara musu baya zuwa cikin bukkar. "Zo Jabu ki zauna a kusa da Yafendonki." Wata mai kama da Dada ta faɗa. Kusa daf da ƙafafunta na zauna kaina aƙasa na gaishesu cike da ladabi. Suma cikin karramawa da haba_haba suka amsa. "Wannan ƙannenane duka. Ga Yafendo A'i, ga yafendonki mai sunanki kin zauna a kusa da'ita. Zai Baffanku Musa gashi, sai Yafendonki Kaɓoji gata nan itace surukar Baɗɗo,. Ta nuna mun mahaifiyar mijin Boɗɗo. Kafin ta ɗaura da nuna mun su Cubu tace. " Wadannan kuma duk ƙannenki ne kece babbarsu, Amaduyal baya nan shi kuma na faɗa miki tun jiya." Murmushi kawai nayi dan na lura a damuwa Dada take sosai. Yafendo Jabu ce tace. "Zan ɗaukeki in tafi dake gidana, can ma akwai Daso shekarunku zasu yi ɗaya mijinta rasuwa yayi ya barta da yara tara. Zan zagaya dake dangi su ganki, zaki ɗan jima kafin ki koma ko?" A sanyaye nace. Na dawo nan da zama baki ɗaya ne, auren nawa ya ƙare. Kuma dan Allah a hannun Dada nake son zan zauna" Gabaki ɗaya suka kalleni, banda Dada domin ita bata wani gane Hausa har sai da ƴan uwanta su kai mata tafintar abinda na faɗi. Da sauri ta ɗago ta kafe ni da ido cikin yaren yarbanci tace. "Yanzu sai da wannan auren ya mutu, dangin mahaifinki sun ƙi barinki kiyi zaman auren ko? Dama tun farko da dan tani akabi da Debisin dai zaki aura domin shi yafi cancanta da sanin daraja da kimarki. Ita Iyaan taki ce ta amince miki ki dawo hannuna da zama alhalin tasan komai, zamana tare dake Jabu bazai yiwu ba. Tun jiya da kika shigo garinnan ban runtsaba har zuwa wayewar garin yau. Abinda nake so dake shine ki bi Yafendonki ki zauna a hannunta akwai Daso zaku dinga zuwa tallar nono tare, komai ma zaku ringa yi a tare. Amman ina mai baki shawarar ku koma birni inda kika fi wayo ki ci gaba da zama rayuwar Ruga cike take da ƙalubale, kumama ba iyawa zakiyi ba. Nima in kuɗaɗena suka haɗu zan je in dubo yaran naki. A hannun dangin ubansu kika baro su?" Wasu zafafan hawayene suka gangaro kan kumatuna, tabbas akwai matsala shin mijn Dada baya ƙaunar ganina kenan, baya son ya samu ladan riƙon marainiyar Allah, ko da wani abunne wanda ni ake ta ɓoye mun ne? Duka waɗannan amsoshin na adanasu inaso duk lokacin dana samu lokaci mai kyau da Dada zata amsamun, ta bani tarihin mahaifina cikakke. Dan bansan wasu abubbuwa a game dashi ba sosai. Na dai san sunanshi, sai hotonshi babba dake kafe a falon Iyaa, sai hirarshi da watarana ke shigowa cikinn zance haka in su Iyaa na yi a tsakar gida. Baffa Musa yace. "Allah shi kyauta. Ni ina ganin tabi Jabu ta zaunaa a hannunta ko babu komai zasu dinga ɗebe ma juna kewa ita da Daso. Kuma komai zasu iyayi. Dan in hanuna nace ta komo bani da wata budurwar ƴa a gabana ma. Tunda tace tana son zama a zuba mata ido, in taji wuyar da bata sababa da ƙafafunta zata koma Birni aradu" Yafendo kaɓoji tace. "A barta a hannuna tana ganin Boɗɗo sai hankalinta ya kwanta, kuma anan akwai Hama naga tun jiya da tazo suke hirarsu tare, kuma akwai matan ƙannenta a cikin gidan ƙila tafi jin daɗi. Kema Adda Daso zuwa ganinta zai fi miki sauƙi. Zasu dinga zuwa tallar nono da Hama dan kar damuwa ta dameta." Baffa Musa yace. "A'a ki barta dai Jabu ta tafi da'ita can wajen nata. Ita kanta Daso tana buƙatar wacce zasu dinga shawartawa dan gudun damuwa. Ke Jabu ki je ki ɗebo kayanki sai ku tafi, Allah bashi in ita Daso mahaifiyarki ta samu daidaito da Mijinta kya dawo hannun nata, duk da nasan mutumme bauɗaɗɗe ga taurin kai da dagiya. A kan ki meye ba'ayiba a shekarun baya da suka shuɗe. Ita yar mahaifinkiToyosi ai tasan komai yaƙi an yishi" Bani da zaɓi dole haka na kinkimi jakata na bi Yafendona zuwa gidanta, tafiya mu ka yi mai ɗa karen nisa, kamar ma ba ƙauye ɗaya suke da Dada ba, kuma fa a ƙafa su kamar ma basa son hawa Acaɓa. Gidanta kam ita kaɗaice a yadda na lura daga ita sai mijinta da yaranta. "Jabu ga ɗakin Daso ki shiga ki ajjiye jakarki, zan tafi tallar nono yanzu, ki shirya sai in kai ki wajen Daso ku zauna kina tayata miƙa Nono. Mu nan ba'a zama daga masu kiwo sai masu fita tallar Nono " Ɗan murmushi na ƙaƙaro kawai. Bukkar data nuna mun ciki na shiga na ajjiye kayana a gefen gadon ƙasa, a kusa da inda naga jakar kayan da nake zaton na mai ɗakin ce Daso. Taya Yafendo ɗaukar ƙwaryar nono ɗaya da buhun bakonta nayi. Muna tafe muna cin karo da mata da yara kowa da ƙwaryarshi ta nono a ka za'a tafi talla. Maza da samari kuma sai wuce mu da garke_garken shanu suke yi suna shiga jeji kiwo. Rayuwar ƙauyen ta matuƙar bani sha'awa, gasu da tsabta ainun kamar ba ƴan ƙauye ba ma, ƴan ƙazaman basu da yawa. Wannan akori kurar muka kuma shiga cike da mata masu tallar Nono, sai yarata yaren Fulani suke ta faman yi, ni dai ina cikinsu ƙwalam har muka iso babban titin mota inda matafiya ke wucewa, anan naga mata da yara jejjere a titi sai ƙulla Nono a leda suke yi, wasu kuma suna damawa. "Mu je kinga ga can Daso bari in kai ki wajenta, ni cikin gari can nake zuwa tallan nono ni da Daso uwarki" Zungui_zungui na bita har gaban wata siririyar fara sol ɗin mace kamanninta kamar an tsaga kara ita da Dadarmu, har kaminnin ya ɓaci. A cikin yaranta ma babu wadda yayi kamannin da ita irin haka. Dariya Yafendo tayi ganin irin yadda na ƙure Daso da ido. "Daso kenan mai kama da Adda Daso sak. Sanadiyyar kamanninsu ne yasa taci sunanta. Daso ga ƴar uwarki tazo daga birni . Zata taya ki siyar da Nono, in yaso zuwa gobe itama sai ta fito da nata ƙwaryar." Hannuna Daso ta jawo ta matso dani kusa daf da'ita. Sai farin cikin ganina take yi kamar dama can ta sanni. Da Yafendona ta yarata mata wacece ni da yare ai sai ta rungumeni tana mai cike da farin ciki. Nima sai naji zuchiyata ta ɗan yi wasai. Anan Yafendo ta sake hawa abun hawa ita da tawagar wasu mata. Mu kuma duk motar da tazo wucewa sai mu tawo da gudu ana turereniya a tsakani, yayinda kowa ke son asai nashi. Haka suke yin tallarsu. A gefen titin cikin ciyawa mu kai sallar azahar, Daso ta dama mun fura da nono da siga cikin ƙoƙo. Tas na shanye furarnan ga nonon ba tsami sai garɗi. Wajajen bayan la'asar lis muka ɗau hanyar komawa gida, nono da furar da Daso ta ɗauko ya ƙare duka. Ko da muka doso ƙofar gidan sai mu ka ci karo da Yaya Hamma mijin Hama a tsaye a ƙofar gidan hannunshi riƙe da ƴar baƙar ledarshi. Yana ganinmu yayi murmushi. "Yaya Hamma kaine a tafe da yamma sakaliya haka?" Cewar Daso kenan. "Nine Daso, kin ganni na jima ina sallama ashe
Chapter 40 · 0% Book details