Sashe 119
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
IYABO:.
Satinmu uku a asibiti. Sai godiyar Allah domin jikin Dada ana samun haske sosai, har hira muna yi da'ita.
Da safe da Yaya Hamma ya shigo ya miƙo mun Madara mai zafi a cikin gora. Sai Dada ta dubemu tace.
"Hamma ko bayan babu raina Jabu itace matarka. Nayi imanin a hannunka zata samu nutsuwar data rasa a baya. Ina mata fatan samun miji tamkar mahaifinta Adetoye. Mutumne mai yakana wanda yasan darajar mace." Yaya Hamma yace.
"Dada ai Jabu ƙanwatace ko bani na aureta ba sai inda ƙarfina ya ƙare a kanta. Wannan aure duk dangi suna farin ciki dashi, Jabu zata dawo cikin danginta."
Dan a wannan lokacin labarin soyayyarmu ya bazu, Hama kuma kamar mahaukaciya haka ta zama. Dan soyayyar da muke ma juna ni da Yaya Hamma soyayyace wacce baki bazai iya faɗeba, alƙalami bazai iya rubutashi ba. Idaninmu a rufe suke ruf. Duk wani bugun zuchiyata ankai an kawo da soyayyar Hamma yake bugawa. Shima nunamun kulawa yake yi irin kulawar da banyi zatonta a wajen bafulacan daji ba.
Ina ba Dada Madara a baki tana sha kamar a mafarki saina hango Uwani tafe da Saleem Yana biye da'ita har zuwa gadon da muke. Gabanane ya yanke ya faɗi muka ƙurama juna idanu ni da Saleem babu um babu um_um. Kallon kewa da tsantsar so Saleem yake yi mun. Ni kuma ina mishi kallon tausayi da dana sanin saninshi, domin son maso wani babban ciwone, na ɗanɗani ɗacinshi akan Debisi. Saye Saleem yake cikin baƙar jallabiya wacce ta sake bayyana sirrin kyanshi, gemu, ƙasumba, yalwataccen gashin ido haɗe dana gira, da sumar kanshi su suka zame mishi wani irin adon da suka bashi wani kyau me sanyi, rawanine yane a kanshi mai fari da baƙi, sai baƙin agogo a ɗaure a tsintsiyar hannunshi, ƙafarshi saye da baƙin takalmi me kyau, ga ƙamshinshi duk ya cika wajen . Ana cikin wannan kallon_kallo Yaya Hamma ya shigo shi da Baffa Musa. Uwani ta gaishe da Dada tayi mata yaya jiki. Saleem sai sallama kawai yayi mata, shi ba hausaba, Dada ba turanci ba
"Jabu baƙi kikayine?" Cewar Baffa. Shi ko Yaya Hamma gaisawa su ka yi da Uwani tunda dama ya santa. Saleem ya miƙo mishi hannu suka gaisa. Cikin harshen larabci Uwani take mishi bayanin Dada ce mahaifiyata, Yaya Hamma kuma wanane, sai Baffa Musa wan Dada.
Tsugunnawa yayi har ƙasa ya gaishesu da turanci. Baffa Musa yace.
"Jabu wannan ai sai nake ganin ba bafulatani bane kamar Balarabe ne ko, amman ba larabci yake yi ba?" Yaya Hamma na É—ago na duba. Shima ni yake kallo sai naga idanunshi sun sauya launi kamar yasan abinda ke wanzuwa, dan kallon tuhuma yake yi mun. Duk saina ruÉ—e na dibibice ainun na kasa amsa maganar Baffa sai Uwani ce tace.
"E Baffa Balarabe ne daga ƙasar Saudiyya yazo wajen Jabu. To munje can gidan shine akai mana kwatancen asibitinnan muka tawo" Siraran hawayene suka zubo a idanuna dana kalli Yaya Hamma yana tsaye akan ƙafa ɗaya, ƙirjinshi sai hawa da sauka yake yi. Da sauri na share hawayen nawa dan kawar da zargi, ina cikin tsaka mai wuyar fita, bana fatan in aikata abinda zai sosa ran Yaya Hamma. Yana da mugun kishi akan abinda yake so, a bayama da bai kai ga furta mun so ba yayi kishin Debisi, balle yanzu da maganar Aurenmu tayi nisan da ba da ban ciwon Dada ba da tuni ina ɗakina. Baffa Musa ma yace ana sallaamar Dada daga asibiti washe gari za'a ɗaura auren in yaso daga baya in Yaya Hamma ya gyara inda zan zauna na tare.
"Yazo wajen Jabu?" Baffa ya tambaya yana jimamin lamarin. Hamma ya kalla shima, shi dai baice komai ba sai idanu.
"E Baffa akwai kayanmu ne a hannunshi na sare_saren dana faÉ—a muku nayo. Uwani kayanne suka iso?" Na tambaya da sauri ina kashe mata idanu. Uwani ta riga tasan me nake nufi sai tace.
"Kaya Alhamdulillah sun iso suna Kano a gidana" Shi kuwa Saleem ni kawai yake kallo. Yaya Hamma kuma ya sauke kanshi ƙasa yana kallon ƙafarshi, sai wasa da ƙafarshi dake kan wadda ya tsaya akai yake yi.
"Dada Allah ya ƙara sauƙi. Jabu bari mu ganki mana zamu jiraki a waje" Uwani na faɗin haka ta dubi Saleem tace.
"Yalla Saleem" Saleem ya dubi su Baffa yace.
"Assalamu alaikum"
Yasa hannu a ajjihu ya zaro kuɗinsu na Saudiyya masu tsoka ya ajjiye a gefen ƙafar Dada. Yabi bayan Uwani suka fita. Illahirin jikina ni kuma rawa yake yi. Yaya Hamma na duba, ni yake kallo a lokacin idanunshi kamar garwashi ƙirjinshi ya tsananta hawa da sauka, ya riga yasan akwai wata a ƙasa, dan ance marar gaskiya ko a ruwa zufa yake yi.
"Jabu kije ki samesu mana kar ki barsu suita faman jiranki" Inji Dada da bata san dawar garin ba. Kofin madarar na ajjiye da jan ƙafa wallahi na fita. Soyayya gaskiya ce, a wannan lokacin na ji haushin Uwani ainun nasan da gayya tayi maganar domin ita tafi sona da Saleem fiye da Hamma. Ina fita na hangosu a zaune a wani benci, nan na nufesu na isa da sallama siririya a bakina illahirin jikina a mace mus. Murmushi Saleem ya sakarmun na farin ciki. A zahirin gaskiya nasan Saleem yana sona, na yarda da girman son da yake yi mini. To amman Yaya Hamma yayi tasiri a rayuwata baki ɗaya, salon soyayyarshi ya wuce salon da zan tsaya kwatantawa, jin sonshi nake yi tamkar mahaɗin rayuwata.
"Alhamdulillah nagode Allah buwayi gagara misali daya sake ƙaddara saduwarmu dake IYABO. Haƙiƙa wannan ranar tana da daraja a wajena." Cewar Saleem kenan dake magana da turanci hannunshi a sama halamar roƙo, haka kanshi yana kallon sama. Ni kuma nama rasa ta cewa. Gabana sai faɗuwa yake yi, tunanina da hankalina yana wajen nemo kalaman da zan wanke kaina dasu a wajen Yaya Hamma.
"Iyabo gani na biyoki da batun aurenmu. Inaso a gama komai insan inane matsayata kafin in koma ƙasata, dan in tafi ma da iyayena sahihiyar magana" Ya sake dabaibayeni da wannan kalami a karo na biyu. Shirun nawa yayi yawa, Uwani ce ta zungureni na dawo cikin hankalina, na dubi Uwani ta gallamun uwar harara, na dawo da kallona ga Saleem shi kuma wani irin kallon soyayyar gani kasheni yake yi mun. Ƙofar ɗakin majinyata na duba, Yaya Hamma na hango a tsaye ya kakkafeni da idanu. Da yaga mun haɗa idanu sai kawai ya gyaɗa kanshi ya nufi hanyar ficewa a asibitin da wani irin mugun sauri. Ai saina miƙe ina shirin binshi da sauri. Uwanice ta finciko hannuna ta dangwarar dani a bencinnan na dawo na zauna daɓas.
"Wallahi Iyabo ki shiga taitayinki akan wannan Hamman naki abu sai kace taliyar Hausa ke ko kunya ma ba kya ji. Soyayya sai kace asiri, irin auren wahala da ci bayan da kike son yi kenan, a irin ƙauyen da ke kikeson kiyi zaman aure kenan a bukka zaku gudanar da soyayyar? Baki da hankali Iyabo wallahi. Hamma asiri ƙila yayi miki in ba asiriba banga dalilin da zaisa ki maƙale mishi irin haka ba. Arziki na kiranki ke kinfi son ki zauna a talauce. Ki tuno da irin bautar da kikayi a tafiyar aurenki na baya. Jibeshi ƙazamin banza sai tsawo kamar taliyar murji amman a haka kike so. Ji wani irin hawa da sauka na iskanci da ƙirjinshi yake yi wai shi mai zuchiya. Ke kuma da kin ɗibi ƙafa zaki bishi mu ki barmu a gantale a zaune ko?."
Murya ta sassauto.
"Iyabo kiyi haƙuri ki amshi Saleem a matsayin miji, wallahi zaki ji daɗi. Kiyi tunani ni ƙawarki ce. Ko Dada da kikeson ki taimaka ta dalilin auren Saleem zaki fi samun damar taimakonta. Nasan kina da ƙudirin zama tare da ƴan uwanki ko dan gyaruwar addininsu kamar yadda muka tattauna. Amman Iyabo ai zaki iya saka su a makaranta ba dole sai kece zaki koyar dasu yadda zasu bauta ma Allah daidai ba. Ya fa kamata ki duba"
( ku zaɓa mun miji masoya wannan labari. Ku kanku nasan kun shiga cikin tsaka mai wuyar fita ko? Ina kuma gani Iyabo. Sannan kar kuyi fishi dani akan faɗawa son Hamma da nayi. Hamma ya wuce duk tunaninku. Saƙonninku sun iso gareni ina godiya da soyayya. Akwai wata baiwar Allah data bani dariya da take cewa inna auri Hamma ba zasu yi mun adda'a ba sai dai suce Allah shi ƙara. Wallahi nayi dariya sosai. Ku dai ku biyo labarin kuji )
Anan ƙarshen littafi na biyu ya tsaya.
Zamu je hutun kwana goma kafin mu É—aura daga inda muka tsaya a labarin wasafa farin girki. Yanzu wasan ma zai soma
ðŸ™ðŸ»ðŸ™ðŸ»
Duk mai son turare yayi magana dan Allah da wuri
*ASSALAMU ALAIKUM*
_GODIYA MARAR ADADI A GAREKU MASOYA WANNAN LABARIN_
_NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFIN SUKUTUM ƊINSHI ZUWA GA AMINIYATA, SAHIBATA, MASOYIYATA, SURUKATA, KHADIJA MAIDOKI, MATA A WAJEN PRINCE, ƳAR GABAN GOSHIN YARIMAN MIJINTA._ ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MIKI A DUK INDA KIKE
NAMA YA DAHU....
ROMO ÆŠANYE
LITTAFI NA UKU
GAWURTATTU UKU
NA
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
SHAFIN FARKO (1)