Sashe 39
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da jan Æ™afa na bi wannan Æ´ar budurwar da nake kyautata zaton kanwata ce uwarmu É—aya. Wani waje ne aka É—an keÉ“eshi aka zagaye da kara, nuni taimun da hannunta halamar nanne ban É—akin. Ruwa ta zuba mun a buta ta miÆ™o mun nasa hannu na karÉ“a, tare da shiga ban É—akin. Ƙasace a ban É—akin , sai É—an gefe guda da akayi daÉ“e inaga a wajen suke wanka, sai ramin shadda a gefe. A Æ™yamace nayi bawali na fito, inda zan É—aura alwala ta nuna mun, naga gidan kamar komai da tsari suke yinshi. Nayi alwala muka fito a tare. Har zuwa wannan lokacin Ina jiyo muryar Dada tana magana. Da Æ™yar nayi sallolin da ake bina nayi jigum akan buhun da aka shimfiÉ—a mun nayi Sallah. Abinci wannan budurwa ta kawo mun a cikin Æ™warya an rufe Æ™waryar da faifai. Ya sunanki ne?" Na tambayeta ina É—an fara'a. "Sunana Cubu" Kin sanni?" Na sake jefo mata tambaya. Sai ta girgiza mun kanta halamar A'a. Sai na yi É—an murmushi nace. Ke yarinyar Dada ce?" Sai da tayi dariya sosai kana ta bani amsa ta hanyar É—aga mun kanta halamar e" Kwaryar abincin na buÉ—e tuwone da wata miya baÆ™a Æ™irin ba koriya ba, sai wani irin Æ™amshin ganye take yi marar daÉ—i, amman dake ina jin É—an karen yinwa ba shiri na nutsa hannuna a cikin tuwon. Wallahi da Æ™yar na iya haÉ—iye tuwonnan, ko da na haÉ—iye dambe mu kai ta tayi, yana shirin dawowa ni kuma ina Æ™oÆ™arin mayar dashi, dan gudun kar suce na Æ™yamacesu. Inaga Cubu ta fuskanci bazan iya cin tuwon bane, sai ta miÆ™e ta kawo mun madarar shanu. Dana kafa kaina sai da na shanye madarar tas. Ina sauke kofin nayi gyatsa, sai ga Dada ta shigo tana sharar hawaye cikin dabara, dan ita a tunaninta ma bamu ganta ba. Zargina ya tabbata akwai wani babban abu da aketa É“oyemun tsawon shekarunnan da ba'ason ni in sani. Ni kuma ina ganin lokaci yayi daya kamata in sani. Bakin gado ta zauna kanta a Æ™asa kamar yadda ta saba tace. "In kin gama cin abincin Cubu ta rakaki gidan ÆoÉ—É—o acan zaki kwana, Æ™anwatace a gidan itace uwar mijin BaÉ—É—o uwarmu É—aya ubanmu É—aya babu wata matsala. In Allah ya kaimu gobe na dawo tallan nono zan biyo gidan in same ki. Cubu Æ™anwarki ce Æ™anwar ÆoÉ—É—o, yar Yusuf. Amma. Akwai Amaduyal shine a sama da ÆoÉ—É—o sai dai shi baya zama, yanzu haka suna togo, sun fita kiwon shanu tsawon shekara biyar basu dawo ba, amman ana jin labarinsu, suna yo aike gida, matarshi Sa'ada tana cikin gidannan, da yaranta biyu" Kai na gyaÉ—a. mamakin daya kamani shine jin Dada ta ambaci tallan nono, kenan itama tallah take yi kamar yadda na ga wasu guggun mata a Jere Banyo da Æ™oren tallarsu? Iko sai Allah ai yaci ace Dada tana zaune ne tana morar haihuwa ba wai ace har yanzu aikin wahala take yi ba. MiÆ™ewa nayi tsaye Cubu ta É—aukarmun jakar kayana. To sai Allah ya kaimu goben Dada" Na yi magana a mugun sanyaye. Cubu da Yusufu ne suke gaba ina biye dasu a baya, ina kallon gari maza suna kwakkwance a tabarma, wasu kuma sunyi da'ira suna cin abinci. Yayinda samari masu jini a jika suke ta sha'aninsu kawai. Ta wani dandali muka zo wucewa nan naga kyawawan Æ´an mata farare, da kyawawan Samari. Ƴan mata na waÆ™a samari na yi musu tafi. Wasu kuma keÉ“e suke a gefe guda suna musayar kalaman Æ™auna. Rayuwar Æ™auye akwai ban Æ™awa a cikinta, bugu da Æ™ari akwai nishaÉ—i sosai. Tafiyace miÆ™aƙƙiyar gaske mu kayi kafin mu iso gidan BoÉ—É—o, duk na gama galabaita, ga gajiyar hanya da dama ban huceta ba, ga wannan tafiya me nisa da muka sake yinta. Suna kwance a tsakar gida mu kai sallama muka shiga, mazan gidan kuma kafin mu shigo sai da mukai musu sallama. Da sauri BoÉ—É—o ta taso ta tare mu." Ina tsaye bansan me Cubu tace da'ita ba. Kawai sai naga ta rungumeni ta fashe da kuka. "Adda Jabu ashe zan sake ganinki a rayuwa? Cike zukatanmu suke da maraicinki" Ta faÉ—i hakan da kwaÉ“aɓɓiyar hausa. Nima hawayene suka gangaro kan kumatuna. Nan BoÉ—É—o ta shiga dani cikin gida tana ta nunani, ni dai Adda Jabu kawai nake jin tana ambato. ÆŠakin Yafendo KaÉ“oji ta kaini Æ™anwar Dada surukarta kenan. Kanta ta dinga jijjigawa tana nanata sunana. Abunda na fahimta Æ™anenane kaÉ—ai sukai farin ciki da ganina. Hannuna BaÉ—É—o ta jawo muka shiga cikin bukkar data kasance É—akinta, Su Yusufu na biye damu. BoÉ—É—o ta kalli su Cubu tace. "Sunanta Adda Jabu. Yayar Amaduyal ce, Dada ce ta haifeta itace yarinyarta ta farko. Ina tunanin sanadintane ke sa Dada Æ™unci da zubar hawayen da tun tasowarmu muka tsinci Dada a wannan halin." Runguma suka kawo mun dukkansu ukun, babu nuna Æ™yama ba komai. Hawaye masu É—umi sukaita zurubtu a kumaruna, hankalina a madadin ya kwanta sai ya sake tashi. Ni kaina na jima ina tausayama rayuwar Dada, na daÉ—e ina zargin bata jin daÉ—in rayuwa akwai wani babban lamari data Æ™unsa a cikin ranta yake nuÆ™urÆ™usar rayuwarta. A wannan daren mun yi hira sosai da Æ™annena na yaushe gamo, dan su Cubu sunÆ™i tafiya a cewarsu sai dai du mu kwana a zaune. "Adda Jabu ki ce su tafi, Baffa zai yi faÉ—a sosai, ko ma yazo gidannan a darennan. Gobe Cubu zata kai nono cikin gari, Yusufu kuma zai fita da Shanu kiyo Kuma zata burga madara ta fitar da man shanu da asuba." Jim na kuma yi jin abinda BoÉ—É—o take faÉ—e. Cubu tunda kinsan hakane, ku yi haÆ™uri ku tafi gida. Ni ina nan na dawo rugarnan kenan, daku zanci gaba da rayuwata" Da kyar na lallaÉ“asu suka tafi, suna tafiya sai ga mijin BoÉ—É—o ya shigo ya miÆ™o balangu a baÆ™ar leda. BoÉ—É—o ta gabatar mishi dani a matsayin babbar yayarsu. Cike da jin kunya ya sake gaisheni yana sosa Æ™eyarshi shi a dole kunyata ce ta kamashi. Kai fulani a kwaisu da kunya da kawaici sosai. Fitar mijin BoÉ—É—o ke da wuya mu ka jiyo sallamar wata mata da BoÉ—É—o ta yo kiranta da suna Hama Ƙwarya ta ajjiye mun a gabana tace. "Use baÆ™uwa" Farar bafulatana doguwa gata da baÆ™in gashi. Da fara'arta muka gaisa duk da hausar kamar ta yara Æ´an koyo suke yinta. "Adda wannan matar wan su Yuguda ce, mijinta shine Babba a gidannan, yana fita aiki cikin birni. Allah sarki, sannu Hama nagode sosai da fura" Murmushi ta kuma yi mun haÆ™oranta kamar Æ™anÆ™ara dan haske, a gaskiya Hama kyakkyawar macece banga wata makusa a tattare da'ita ba face ta rashin wayewa, da Æ™azanta kuma dan Æ™afarta duk faso fasonnan ya É—ebi wata annakiya ya adana. Ga gashi iya gashi amman kitson a furje kuma cike da yayin katifa. BoÉ—É—o tace. "Hama wanna itace Babbar yarmu Adda Jabu, ba lallai bane ki san labarinta ba. Nima naci da bin diddigi yasa na san labarinta. Ta taÉ“a zuwa rugarnan da daÉ—ewa lokacin muna yara Æ™ananu." Tare da Hama mu ka ci balangunnan mu ka taÉ“a hira dai haka. Duk da gajiyace ainun a jikina, ga tunane _tunane da suka haÉ—u suka cukurkuÉ—e mun rayuwata. Duk wani bugun zuchiyata bugawa yake yi da so da Æ™aunar Gwadabe na. Haka tausayin mahaifiyata da son jin matsalarta suma su ka dabaibayeni. Ina fatan in zame mata sanyin idaniya, maganin zubar hawayenta.amman ta yaya tunda mijinta ma bai karÉ“eni a matsayin Æ´a ba, tunda gashi a darennan ya kasa haÆ™uri ko da kwana guda ne in yi. Ko ma Iyaa Debisi ta faÉ—a mun yana da faÉ—a, bauÉ—aÉ—É—en mutum ne ainun. Tunani, da zafi, da sauro su suka hanani huce gajiya ta hanyar saka haÆ™arÆ™arina a Æ™asa, katifar yayin dana kwanta akai sai sossokeni kawai take yi. Babu shiri na miÆ™e na fito tsakar gidan, duk yawan matan gidan suna kwance a tsakar gida bisa katifun yayi. A kan tabarma na kwanta iska na É—an hura ni kaÉ—an. Da haka É“arawon bacci yayi awon gaba dani izuwa asubar fari, kwaramniya da kukan shanu ne ya farkar dani. Ashe nonon shanu ake ta tatsa, su kuma sai kuka suke yi. Wasu daga cikin matan na gansu suna burga nono da wani itace mai kama da maburgin miyar yauÆ™i, wasu kuma suna ta aikin dahuwar madarar shanu, yayin da wasu suke sharar garken Shanu, wasu kuma girkin safe suke yi. Ina buÉ—e idanu Hama dake shara tace. "Jabu kukan nagge ya tashe ki ko? " Tai maganar tana murmushi. Nima Murmushi nayi mata kawai, na miÆ™e BoÉ—É—o dake zaune a cikin jerin matan da suke ta burga nono ta miÆ™o mun buta, tai mun nuni da ban É—aki. Ruwa na kama na fito na É—aura alwala na shige ciki. Na jima ina roÆ™on Allah yayi mun mafita, ya kuma sassauta mun soyayyar Gwadabe a ruhina, bazan roÆ™i ya cire mun soyayyr ba dan abadan Gwadabe bazai gaza samun gurbi a rayuwata ba. Tunano Æ´aÆ´ana yasa hawaye suka zubo mun a kumatuna, ba shiri na miÆ™e na fita. ÆŠaya bayan É—aya na dinga bin matan gidan muna gaisawa, mun shiga É—akin Æ™anwar Dada ma mun gaisa. Cikin garken shanu BoÉ—É—o ta jani wai in taya ta mu tatsi nonon Saniya ta dafa mana mu sha. A baya na bita zuwa cikin garken shanun a nan muka tarar da Hama a ciki ita da mijinta suna shafa ma wata saniya magani jikinta duk kuraje ya fito. "Wannan itace baÆ™uwar tamu BoÉ—É—o? Ai Hama yanzu take faÉ—a mun cewar mun yi bakuwa kuma ma Æ´ar uwa" Cewar mijin Hama wani dogo siririn bafulatani sosai, ga gashi a kwance a kanshi lub, na lura kamar yafi kowa tsayi a gidan, ko dan ya fi kowa sirantane oho. "E Yaya Hamma itace baÆ™uwar tamu, Ita ce sama da Amaduyal, daga ita sai shi, a birni take aure can Kano" Murmushi ya sake faÉ—aÉ—awa yace. "Sannu da zuwa, baki tawo mana da yaran ba?" ÆŠan murmusawa nayi bayan mun gaisa nace dashi. Na baro yara a gida sabida makaranta" Baice komai ba sai É—an murmushi da yayi, ya kaÉ—a shanu sama da talatin suka bi bayanshi da Æ´ar sandarshi da halama kiwo zashi. Ni