← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 192 OF 237

Sashe 192

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ya tafi. Kafin ya tafin saida ya ba ko wacce wadataccen kuɗin tsaraba, ya shiga ya duba Malam yai mishi sallama ya kama hanya. Nan su Shafa suka shiga shirin tafiya. Tsakanin Shafa da Hadiza gaisuwace kawai itama gaisuwar bata girmamawa kamar yadda Shafa ta saba Yaya sama Yaya ƙasa ba, ana dai gaisuwar a hakanma Gwadabe ne yai ta tausarta. Ita kanta Hadiza tasha jinin jikinta dan hatta su Yaya Tasi'u basa amsa gaisuwarta kuma suka sanarma Malam abinda Hadiza ta aikata. Ya dirar mata da faɗa Baba Asshi da Baba Suwaiba, da Amaryar Malam duk sukai mata faɗa akan kuskurenta. Malam yasa akai mai kiran Shafa ya bata baki ya bata baki sosai. "Babu komai Malam wallahi ya riga daya wuce" "To Allah yayi miki albarka Shafa'atu, ina su Abba?" Ɗan murmushi tayi tace. "Suna ƙofar gida makaranta" Sallama tayi mishi ta komawarta gida, ta shiga aikin girki, Hadiza ma aikin girkin take yi na tarbar Oga, matan gidan ko wacce na aikinta anata zuba hira abun gwanin ban ƙawa. Daf magriba sai ga Gwadabe ya shigo da niƙi_niƙin kayan tsaraba. Daga ƙofa ya zunguri Shafa da ledar lemo da ayaba. "Riƙe nan inna dawo sallah ki sameni a ɗakin Hadiza mu tattauna" Ta amsa tayi godiya, ta ajjiye ledar ta shige banɗaki, shima alwalar yayi ya tafi masallaci a gurguje dan har an tada Sallah. Sai da Shafa ta sake gyara kwalliyarta dan yanzu a fice take ta ɗauki shawarar wata ƙawarta abokiyar aikinta data ziyarceta washegarin ranar da Hadiza ta bita har ɗaki. Ba iyaka Gwadabe Shafa ta ɗaga ma hankali da kwalliyarta ba harda Hadiza dan kusan tafi Gwadabe firgita. Ga gashinta sai sheƙi yake yi, gashi dai shi ba yawa ba amman ta gyare abunta tsab gwanin sha'awa. Zama tayi a gefen Gwadabe jikinsu na gugar juna, Hadiza na daga ɗaya ɓangaren. "Barka da dawowa ya hanya, da fatan abinda akaje nema an samo? Barka da gida umman Ummi" Saroro Hadiza tayi tana kallonta tama gagara amsa sannun da take yi mata ta bita da idanu kawai. "Sannu Shafa Irin wannan kyau haka. Ina Iyabo kika barota ?" "Iyabo tayi bacci shine na shinfiɗeta a kusa da Abba" Da yanga take magana. "A_a _a_a je ki ɗakkota inta farka tana neman nono fa? Maza jeki ɗakkota bana son abinda zai taɓa Iyabo" Har Shafa ta fice ta dawo tsakanin Hadiza da Gwadabe babu wanda yace komai. Shinfiɗe Iyabo Shafa tayi a kujera. "Hadiza zuba mana abincin yau dai muci tare sai in rarraba muku tsarabarku data yaran ko?" Fuska a turɓune Hadiza ta zuba musu lafiyayyen tuwo da miyar bushasshen karkashi wanda yaji naman ragon suna da kayan ciki. Tsakankanin Shafa da Gwadabe ne kawai suke ta hirarsu har aka kammala cin abincin dai. Atampipi da leshi ya zaro a ledarshi ya ajjiye a tsakar ɗakin. "Wannan naku ne da zaku dinga kuyi fitar sunan Sakina. Gashinan kala uku_ukune ke Hadiza tunda kece babba ki soma ɗauka" "Itama babbace ta ɗauka ta bar mun nawa" Shafa tasa hannu ta zaɓi ta darje tace. "Mungode Allah ya ƙara arziki" Leda ya miƙoma Shafa yace. "Wannan nasu Abbane gashinan kinmun ƙorafin Abba bashi da wanduna kwanaki, to ga wannan a ƙara mishi dashi. Hadiza kema ga na su Ummi, wannan kuma na sabuwar jinine. Hadiza ta karɓa tana bin manyan laidojin da Gwadabe ya bama Shafa. Ta kalli ta hannunta ta gyaɗa kai kawai. Tace angode wallahi ta kasa dan wani ƙududune ya tokareta a wuya. Shafa kuwa sai adda'a take yi mishi. Ya haɗa musu da dubu shida_shida. "Wannan kwa yi dinki. Ragowar kayannan Hadiza ki ajjiyesu a wajenki na Sakinane sai ku ƙara da taku gudummawar. Ke Shafa ɗauki Iyabo bari in ɗebar miki kayan in rakaki" Hakan kuwa akayi, suna fita Hadiza ta wuce ciki fu tayi kwanciyarta. Ko da Gwadabe ya dawo yayi mata magana tayi watsin ruwan tsarki dashi, shi kuma yayi tunanin ma bacci take yi. Gaga_gaga har ranar tafiya Takai yayi sukai ma jama'ar gida sallama suka tafi. Da daddare suka shiga Takai Bara'u na ƙofar gida ya gansu. "Gwadabe kune a tafe? Maraba lale da zuwa. Hadiza, Shafa bismillah ku shiga ciki' Bayan an gaggaisa sai suka wuce ciki Gwadabe kuma yayi zamanshi wajen amininshi tunda yana jiyo muryoyin mata a gidan. "Ya bayan rabuwa Bara'u. Ya labarin Iyabo da rayuwar gidan aurenta?" Dariya Bara'u yayi yace. "Kai Gwadabe maimakon ka soma da tambayar yara da noma kamar yadda ka saba sai ka somamun da batun Iyabo? Nasan ana binka sallah ga buta yi alwala kayi Sallah. "Haram munyi sallolinmu dukka a hanya. Kai dai bani labari" Ajjiyar zuchiya Bara'u yayi fuskarshi ta sauya. Yace. "Labarin tsuntsun soyayya babu daɗi. Ga wani babban al'amari daya faru a gidanku wanda duk garinnan na Takai anata tsogumi akan abun Gwadabe. Nasan baka sani ba Gwadabe. Yanzu haka Babala tana asibiti rai a hannun Allah. Tashin hankalin da take ciki ya kai. Mrs Bukhari ce Ayi haƙuri da wannan idanun nawa bai warke ba. Sannan dan Allah ba kullum zan dinga posting ba sau uku a sati zaku dings samu sakamon idanuna daya matsa mun da ciwo nasan zaku yi mun uzuri in ku kai la'akari da ni bana wasa da typing sam. Nagode. Ku taya ni jaje Allah yayi ma magena rasuwa mai suna Sameer jiya.
Chapter 192 · 0% Book details