Sashe 113
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana fitowa daga É—akin Hadiza ya sauke ajjiyar zuchiya sassanya. Tsaki yaji an doka daga gabanshi, É—agowar da zaiyi yaga ashe Baba Asshi ce a tsaye da yaranta da matansu a tsakar gidan suna Æ™us_Æ™us. "Ina wuni Baba Asshi?" In kun tanka Baba Asshi ta tanka. Saida ya wuce ta sake jan wani dogon tsakin, kanshi kawai ya gyaÉ—a yana fata da burin kar a samu irin wannan rarrabuwar kan a nashi gidan. Da sallama ya shiga É—akin Amarya Shafa. Tana zaune akan kujera tasha adon atamfarta baÆ™ar macce Æ´ar leda. Bakinnan nata yasha janbaki raÉ—au sai sheÆ™i yakeyi. Komai zaune yake daram a muhallinshi. Da sauri Shafa ta miÆ™e ta tawo da sassarfa izuwa wajen mijinta. Isowarta ke da wuya ya haÉ—e jikinshi da nata ya riÆ™eta gam. Ajjiyar zuchiya ya sauke mai Æ™arfi a zuchiyarshi yace.."Lallai aure ni'imace akwai hikima a auren mata biyu, shi yasa ubangijinmu ya umarcemu da somawa da biyu madamar zamuyi adalci. Ko wacce mace da irin Æ™amshinta, taushin fatarta, kalaminta, Sannan da irin baiwar da Allah subuhanahu wata ala yai mata. A wannan daren Amarci Gwadabe ya gwangwaji Amarcinshi lami lafiya kuma Alhamdulillah Shafa ta kawo cikakken budurci marar kokonto a cikinshi. Tana kwance a Æ™irjin mijinta tana baccin daÉ—i da wahala zuchiyoyinsu fes. Ta É“angaren Hadiza kuwa tana kwance tana lissafe lissafe gami da hasaso abinda bazai taÉ“a bata kwanciyar hankali da nutsuwa ba. Dan a wannan daren sai da ta dinga tambayar kanta to waima me yasa ta amince da Auren Gwadabe ne ma?" Nasihu da surruka, da dabarun zama da kishiya, da zama tauraruwa a idanun miji da Baba Fhatsima ta karanto mata, shi ya sake faÉ—i mata. Wasu zafafan hawaye suka gangaro suka wanke mata kumatunta. Zurub ta miÆ™e ta faÉ—a banÉ—aki ta É—auro alwala ta koma É—akinta. Ta maye gurbin tunane_tunanen da basu da amfani da yin sallolin nafila tana miÆ™a kukanta ga Ubangiji kan ya sassauta mata kishin dake zuchiyarta. Yaa kuma kareta da cutar da abokiyar zamanta koda da furucine. Ya É—aga daraja da kimarta a idanun mijinta. Haka ta dinga sallah tana adda'a, ai kuwa saida taga bacci yana shirin kayar da'ita sannan ta kwanta. Ta kuwa samu bacci mai nutsuwa kuma nannauya. Asubar fari ta miÆ™e ta nufi kitchen. Dai_dai Shafa itama ta buÉ—e Æ™ofar É—akinta ta fito kitchen. Idanu suka haÉ—a duk da dai akwai duhu amman sunsan juna suke kallo. "Yaya barka da asuba" Shafa ta faÉ—a tana Æ™oÆ™arin buÉ—e kitchen É—inta. "Yauwa barka dai Amarya mai maganar suger. Ya kwanan angon naki?" Shafa tayi murmushi ta É—an sauke kanta Æ™asa bata ce komai ba dai. Kitchen Hadiza ta faÉ—a tana murmushi, amman a baÉ—ini zuchiyarta ma bugawa yake yi, hatta hannayenta sai taji suna rawa kakakar_kakakar. Cikin zuchiyarta tace. "Kishi bala'ine. Gaskiya mana a gidanmu aka kasa samun dedeto. Ashe haka kishi yake da tasiri mai girma?" Hawayen dake shirin zubowa a idanunta ta mayar da hanzari. A gurguje ta kunna risho ta faÉ—a banÉ—aki bayan ta É—ora ruwan wanka. Jikinta a mugun mace ta fito daga banÉ—akin, daidai Gwadabe ya fito daga É—akin Shafa zaije wankan tsarki. Shafar tana biye dashi da dukkan halamu tare zasu je suyi wankan. Lallai soyayya ta kai soyayya. Murmushi ta sakarma Gwadabe, murmushin daya kasance tamkar garwashi wajen Æ™una. Shigewa tayi É—aki tana haki. A daddafe tayi ra'atanil fajir, ta É—aura da sallar asuba. Ta jima sosai akan sallaya tana roÆ™on Allah ya sa mata salama a zuchiyarta game da wannan kishi mai kai mata mahallaka ya baro. Saida ta karanta Qur'ani suratul naba'i ta shafa adda'a sai taji zuchiyarta tayi wasai. Cikin sauÆ™in zuchiya ta shalla wanka, ta shiga gyaran É—akinta cikin Æ™anÆ™anin lokaci ta kammala, a madadin kunna turaren wuta tunda bata da gawayi kuma yayi wuri ta aika gida a É—ebo mata saita kunna É—an tsinke ta bishi da Room freshener na MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI mai Æ™amshin oud Cikin Æ™anÆ™anin lokaci gidan ya É—auki saiti. Zama tayi a barandar data haÉ—a Æ™ofofin uku, tana iya hango masu gilmawa, suma suna iya hangota. Doya ta gutsura ta fereye kaÉ—an, ta É—aura abun suyanta ta zuba mai ta soma suyan doya. Matar Sabitu ce ta fito tsakar gidan taci uban Æ™ananun kaya kanta babu ko É—ankwali kasancewarta mai gashi daidaiya, sai karairaye takeyi da ledar shara a hannunta ta gangara Æ™asan gidan dan jefar da ledar shara a babban durom É—in shara dake gefen bayan gidan tsakar gidan. Kai Hadiza ta jirjiza kawai. Doyarta ta soyu ta kwashe ta juye man a samira ta adanashi. Sai ta mayar da kaskon kan wuta ta fasa Æ™wai biyu ta yanka albassa ta É—an barbaÉ—a dunÆ™ule ta soye Æ™wanta gidan ya kaure da Æ™amshi. Da É—aya da É—aya amaren gidan suketa fitowa domin É—ora abinda za'a durama Æ´an hanji, dama dai kunsan Amare a gigice suke tashi da yinwa. Ruwan tea Hadiza ta haÉ—a dama tana da ruwan zafi a flaks É—inta. Ta gama haÉ—a kayan karyawanta tsab ta kai ciki. Ta yafa mayafinta da Æ™aton kaskonta me murfi ta fito tsakar gidan. Ta haÉ—u da matar Abdullahi da matar Jazuli, babu wanda ya kalleta itace dai ta gaishesu a wani wulaÆ™ance suka amsata har suna shewa, ko ta mecece ohon musu dai. Æarayin su Yaya Tasi'u ta nufa. Da matar Yaya Jamilu ta soma cin karo Innar Khadija. Tana soya dankalin turawa a Æ™ofar kitchen É—inta a gawayi. Tayi kaca_kaca da wajen, É“awon dankalinma da É“aron Æ™wai duk ta zubar a Æ™asa yara sun tattaka. "Me zan gani Amarya sassafe haka. Af na mance ashe zawara kwana uku akeyi mata ango ya koma É—akin Amarya ko?" ÆŠan murmusawa Hadiza tayi, inda sabo ta riga da tasan dama irin zaman da akeyi. Magana ta arziki bata haÉ—a kowa da kowa, face habaici da son gumama juna. "Hakane ango yana É—akin Amarya. Nima gaushi nazo ku bani" Sai ta tuntsure da dariya tace. "Ga gaushi zo ki É—iba kafin ku soma hura naku. Tunda me gidan maganin Æ™arfin maza yake siyarwa" Ajjiye kaskon tayi, domin furucin Innar Khadija yayi mata zafi. Sun daÉ—e suna kushe sana'ar Gwadabe a cikin gida. Dan Amaryar Malam har yara take turawa da nera É—ari tace wai a bata maganin basir malam zata ba. "Bari in gaisa da Anty Badi'a tukunna sai inzo in É—iba." Nan ta wuceta ta barta da zunÉ—enta ta baya. Tun daga kofar da zata sadaka da É“arayin Anti Badi'a kake jiyo Æ™amshi na tashi. Falonta tsab yasha gyara, ta shiga ta samu Sailuba na fesa Room freshener a labulayen É—akin. Anty Badi'a data ci kwalliya da riga da sikert É—an kanti wani mai tattara na zamanin tana gaban durowar da tv yake kai tana juna abun Æ™ona turaren wuta mai amfani da wuta ( electric burner wanda a lokacin batai yawa ba, sai gidan Æ´an gayu ake iya ganinta) "Anty Hadiza, Mama ga Anty Hadiza " Cewar Sailuba kenan. Maman ta É—ago da dariya tace. "Uwargida sarautar mata ke ko me kike yi a nan sassafe kamar wacce tayi É“atan kai?" Hadiza dake ta kallon falon kamar ta wanke makanta tace. "Ke dai Anty Bari. Kinga rushi nazo É—iba inaso kafin in karya in kunna turaren wuta" Sai Anty Badi'a tayi Dariya tace. "Ina zuwa. Sailuba ki zuba mata farfesun kan ragonnan a Æ™aramar kula maza" Ta shige É—aki sai gata da sabuwar ( electric burner) a kwalinta ta miÆ™a mata dama guda biyu ta siyo tafiyarsu Umara ita da mijinta. "Ga wannan aita Æ™ona turare lafiya." Hadiza ta amsa da murnarta taima Anty Badi'a godiya mai yawa. "Na ganki da leshi kina wayayya. Ai leshi kwalliyar dare ce, ko rana. Da safe ai Æ™ananan kaya ya kamata ki mayar su zama ababen sawarki. Karfa ki ba damu yarinya Æ™arama ta ciri kambu" Hadiza ta zaro idanunta waje tace. "Nifa Anty Æ™ananan kaya guda É—aya jol gareni. Wata rigace doguwa mai hannu É—aya. Itama Æ™awatace ta kawo mun. Ina dai da rigunan bacci" MiÆ™ewa Anty Badi'a tayi tace. "Jira" Bata jima ba sai gata da leda ta miÆ™o ma Hadiza. "Kije maza ki sake kayan jikinki ki sa wannan. Zuwa anjima Sailuba zata zo ta kira mun ke. Akwai Hajiyar da nake siyayyar Æ™ananun kaya a hannunta kayanta suna da kyau Dubai take siyosu. To anjima dama zata kawo mun kaya, da Æ´an sabulan gyaran fata." Cikin murna Hadiza ta fito tana shima Anty Badi'a da albarka. Koda ta fito bata ga Innar Khadija ba, ta É—ebi gaushinta ta wuce. Tana kunna turaren wuta ta shige É—aki ta buÉ—e ledar da Anty Badi'a ta bata. Riga da sikert ne irin na jikinta sak kalace ta bambanta. Na jikin Anty Badi'a siket É—in mai ruwan gorrone, sai rigar mai ruwan madara da kwala a wuyan rigar. Ita kuma Hadiza nata siket É—in kalan jinin karene maron sai rigar mai ruwan madara. Ta saka kayannan yayi É—as a jikinta rigar ta É—an matseta dan tafi Anty Badi'a cikar Æ™irji. Tana gyara gashi ta jiyo sallamar Shafa a falo. Shi kuma gogan naka masu abu da abunsu sai ya kutso kai ya shigo cikin uwar É—akin. Ƙur yayi mata da idanunshi yana mata wani mahaukacin kallo mai É—auke da guguwar sha'awa da burgewa a ciki. Manna Æ™irjinshi yayi a nata Æ™irjin, yayi lub a jikinta yana shaÆ™ar Æ™amshin dake saurin tayar mishi da jarabarshi. Ajjiyar zuchiya Hadiza ta sauke. Gwadabe ya É—ago idanunshi da suka sauya kala yace. "Wallahi kinyi kyau sosai. Kayannan ya amshi jikinki da fatarki Æ´ar duma_dumata" Murmusawa tayi wani farin ciki ya baibaye zuchiyarta. "Nagode ango mijin Amarya. Naga sai sheÆ™in angwanci kake yi." Murmushi yayi mata dan yaji sautin kishi a muryar tata. "Shafa tana falo kizo muci abinci." Da sauri ta kalleshi tace. "Abinci kuma, a ina za'aci abincin ba'a É—akin Shafa kake ba?" Dariya yayi mata. "Abincinne nace ta É—akko muzo muci a nan É—in. Hakan nake so mu dinga yi, sabida zai samar mana nutsuwa da fahimtar juna. Wacce bata da kwana ma zata samu damar zantawa da mijinta. Muje ko?" "Amman Yaya Gwadabe" "Shishshsh... Bana son kice komai, kizo muje" Ba dan ran Hadiza yaso ba dai. Tayo jigum har Gwadabe ya fice tana tsaya tana tunanin ta ina wannan lamarin zai soma. Yama za'ace wannan tsarine me kyau.