← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 237

Sashe 24

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

8 A kwana a tashi A haka rayuwarmu tai ta garawa, yau fari gobe tsumma, babu laifi Alhamdulillah yanzu kam munfi ƙarfin abinda zamu saka a bakin salati. Koda yaushe Gwadabe a cikin tafiye_tafiye yake, duk garin da ya je yakan siyo mana tsarabar garin, su bushasshen kifi, manja, doya, wake, gawayi duk yana siyowa ya kawo. Babala ta jima sosai a gidan sai data warke tsab, ana gobe zanyi arba'in ita kuma ta tattara ta koma ƙauye. Irin ƙoƙarin da taga Gwadabe nayi a kanmu sai ya sake dagula komai. A tsakar gida Babala bata da aikin daya wuce faɗin an ma ɗanta asiri sai wahala nake bashi, ya shiga tarkon yarbawa jikokin oduduwa. In hakan baiyi mata ba sai ta sameni har ɗaki ta ƙaremun tanadi tsab, ni dai zaman gidan gabaki ɗaya ya gundureni, haka naita haƙuri har Allah yasa ta koma Takai. Gwadabe ma haka yasha haƙuri da Babala, damuwa duk ta haɗu tayi mishi yawa, ga matsala da yake samu a wajen ƴan lodi akwai wani bawan Allah da yasa Gwadabe sosai a gaba, domin yawan tashi da motar Gwadabe take yi wajen sufurin kaya, ada yafi kowa ƙwazo a matukan tirelolin har ana mishi kirari da giya dubu, akwaishi da sharara gudu a hanya dandanan sai ya isa ikko, yana isa zai sauke lodi ya sake nauso hanya. To samuwar mota a hannu Gwadabe sai ya doke giya dubu wajen ƙwazo da kazar_kazar bil haƙƙi Gwadabe yake komai. Wata rana ana ma Gwadabe lodi giya dubu shi kuma shigowarshi ƴan lodin kenan, da ya kalli Gwadabe sai yace. "Wata rana ma ba zaka samu ƙafafun da zaka taka mota ba, balle hannayen murza sitoyari in dai muna tasharnan gasa da ni ba daɗi." To daga ni har Gwadabe sai muka shiga damuwa daya dawo yake sanar dani, mu kaita adda'ar neman tsari harda sadaka, ga wannan damuwar ga damuwar Babala abubbuwa suka cakuɗe goma da ashirin. Washe garin ranar da Babala ta tafi muka cika kwanaki arba'in. Ƴan biyu sun yi kuɓul kuɓul dasu gwanin sha'awa. Tun sassafe naketa kaye_kaye dan yau kam a gidanmu zanje in wuni yawon arba'in. Kafin sha biyu na gama duk abinda ya dace, Toye na dawowa daga makaranta, na kwaɓe mishi inifom na watsa mishi ruwa, na shiryashi tsab, naima matan gida sallama. Atampa mai haske nasaka da sabon takalmi da mayafi, ina fita tun kafin in sauka daga kan tudun gidan na soma jiyo hayaniyar muryoyinsu suna gulmar da suka saba. Muna zuwa titi na tari Bus sai ƙofar Nasarawa inda anan gidanmu yake. Cikin layinmu na shiga tun daga titi nake gaggaisawa da mutane, wasu dole ma in tsaya su ga ƴan biyu a haka harna isa ƙofar gidanmu. Gidane mai ɗauke da karamar ƙofa gefe da gefen ƙofar shagunane biyu. Ɗaya na Iyaa Debisi daya na Iyaa Kokodeen. Iyaa Debisi soson danga dasu lagwani, ashana, sitati, gyalu, bula, kayan robibi. Su take siyarwa tana da injin niƙa har biyu dana wuta dana ruwa. A shagonnan mu kai rayuwarmu, akwai ƙofa a cikin shagunan wanda zaka ɓulla babban tsakar gidan namu. Iyaa Kokodeen kuma albo, garin Amala, daddawar kalwa, da bushasshen rogo, garin rogo su take siyarwa harda ma kamun jar dawa. Wannan sana'ar tasu da ita muma mu ka yi wayo muka gansu akai, gashi har yanzu ana takusawa. A bencin dake ƙofar shagon Iyaa Debisi na zauna dan na gaji sosai. Toye kuma yayi cikin gida da gudu. Iyaa Debisi tana zaune a cikin shago taci leshi ɗinkin buba ɗaurin ɗankwalinnan a cukurkuɗe sai gyangyaɗi take ta yi abunta, dama kullum aikinta kenan wannan gyangyaɗi ba'a rabata dashi, kuma a zaune ake yinshi. Iyaa Iyaa!! Na kirayi sunanta tare da ɗan buga benci kaɗan sai ta buɗe idanunta muka haɗa idanu. "Ahhh Iyabo kece da tsakar ranar nan da yara, ku yaran zamani baku da hankali ai mace mai goyo ko ciki bata fitowa sa'ilin da rana ta take. Maza shiga ciki gani nan zuwa. Mahaifiyarki ma yanzu isowarta ko awa ɗaya ba'ayi ba tana ciki" Miƙewa nayi ina fara'a dan na jima banga Mamana ba. Shagon Iyaa Kokodeen na shiga na durƙusa a gabanta na gaisheta , itama tace maza in shiga ciki rana ta take. Ko da na shiga samarin gidan basa nan kowa na wajen aiki, babu ƴan mata a gidan tuni sun jima da aure, Bose ce da aka bari itama gashi tana gidan mijinta. Sai matan ƙannen su Iyaa su su uku Iyaa Beji, da Iyaa Lekan, sai Iyaa Amope. A ɗakinmu na ya da zango mahaifiyata tana tsaye tana sallah goduwa farar bafulata siririya, gata da alkunya da sanyin hali bata iya sakewa tayi hira dani, iyakarta dani gaisuwa da tambayar ya nake ni da mai gidan nawa. Iyakar hirata da'ita kenan saita tsuke bakinta tayi shiru kanta a sunkuye." Tana idarwa ta juyo tace. "Jabu kune a tafe? ( Jabu sunan da dangin mahaifiyata suke kirana dashi kenan, dangin mahaifina kuma iyabo)" Data juyo sai naga ta rame sosai idanunta sun zurma da yawa" Dada kinzo lafiya ina wuni?" Bata amsaba sai miƙo mun hannu da tayi na tashi na sunto yaran na saka mata a cinyarta. Tayi ƙuri tana kallonsu tana musu adda'a. Take Naji hawaye na kwarara a idanuna, Allah ya ɗaura mun tausayinta sosai a zuchiyata. Inna dubeta sai inga kamar tana cikin ƙunci da matsi a gidan aurenta. Dada baki da lafiya ne naga kin rame?" Cikin gurɓatacciyar hausarta ta fulanin daji tace " E jinya nayi kusan wata shida sai dai a kwantar sai dai a tayar, shine dalilin da yasa ban ɓulloku ba." Sai kuma taci gaba da magana dani da yarbanci, dan Hausa mugun wahala take bata, dama da yarbancin muke magana." "Ashe kin samu ƙaruwa Allah ya raya. Ina ɗayan jikan nawa?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Yana ɗakin Iyaa Beji can na baro shi, ya wajen Baɗɗo da mai gidanta? ( Boɗɗo ƙanwatace a gidan da Dada take aure yanzu, sau ɗaya na taɓa ganinta tal a rayuwata) "Ɓoɗɗo ta haihu tana goyon Daso an yi mun takwara" Sai naji ina kewar ƙannena da dangin mahaifiyata ma, sai naji inason kasancewa dasu. Dada inaso in zaki koma zan tambayi izinin mai gidana zan biki in gano rugarku, inaso lokaci zuwa lokaci in dinga zuwa ziyartarki ke da danginki nima ya kamata yarana su san dangina na wajen uwa su saba" Da sauri ta ɗago ta dubeni tace. "Kar ki soma, kiyi zamanki na yafe miki. Ni zan dinga zuwa ina dubaki kamar yadda na shafe sama da shekaru ashirin ina zuwa ganinki." Ƙur nayi mata da idanu ina karantar yanayinta, duk sai naga ta ruɗe, tashi tayi ta bani su Taiwo ta haye ƙaramin gadon Iyaa ta kwanta ta juya mun baya. Na rasa me ake ɓoye mun ne da Dada bata ƙaunar in ziyarceta, bata son danginta su sanni, to meke faruwa ne tabbas tana ƙasa tana dabo. Iyaa ce ta shigo tana faɗa sosai kamar zata ari baki, tana yi tana dukan cinyarta tanata faman yare. Ashe da Debisi take yi shigowarshi cikin gidan kenan. Da yare yace da'ita. "Kiyi haƙuri Iyaa nifa ba cewa nayi yemisi ta ajjiye aikinta ba, gani nayi ta fifita aikinta fiye da zaman auren da muke yine. Kuma tama ga damar zuwa ta haɗa mun jarfa ne" Ya ƙarashe a sanyaye. Iyaa Kokodeen ce ta shigo ɗakinnan tace. "Haba Iyaa Debisi wannan yaron fa yana da gaskiya kuma ma ai yayi ƙoƙari sosai Ya kamata itama yemisi ta dena zuwa tana yawon kawo ƙararshi wajenki ko wajen mahaifiyarta. Ai ga irinta nan abunda ake hango muku daban abinda kuke hango ma kawunanku daban, ku kun ɗauke mu ba wayayyuba. Dama duk namijin da zai auri soja ai dole sai dai ayi zaman haƙuri." Wannan maganar tamkar ingiza iyaa Debisi Iyaa Kokodeen tayi dama har gobe da mikin ƙin aurena da Burodami Debisi yayi a zuchiyarta. Dan da ƙyar ma aka shawo kanta bayan aurena ta zubar da makaman yaƙinta, macace mai kafiya da binbinni, gata da mita. "Basshi ai duk abinda na guje mishi kenan, shi yasa naso ya auri ƴar uwarshi Iyabo. Musamman dana fahimci ita iyabon tana sonshi. A gida ma ita ke kula da komanshi ina ga ya aurata. Yaronnan ya buɗa mana ƙasa a idanu, dana matsa ya je ya haɗoni da dangin ubanshi akazo aka danneni. To yanzu me yake so ayi mishi? Ai haka zaka je kaita kwashe takaici da baƙin cikin zama da Soja, kuma ban yarda ka sake takurama Yemisi akan batun aikinta ba." Daga ni har Burodami Debisi muka yi tsamo_ tsamo tamkar kazar data faɗa ruwa, ya ɗago mu haɗa idanu ya kasa sabida kunya tare da nadamar abinda ya aikata. Lokacin na shiga tunanowa a zuchiyata, a lokacin da Burodami Debisi ya murtsuke idanunshi yace shi Allah ya kashe shi bazai aureni ba. Ji nayi tamkar alƙiyamatace ta tsaya. Abun bai zo mun da daɗi ba, domin jaririyar zuchiyata da so da tsantsan kaunarshi ta ginu, ban taɓa tunanin zuchiyata zata iya son wani mahaluki bayan Burodami Debisi ba. Ni ban iya sa abu a zuchiyaba, ban iya son abuba. Da wasa da wasa Gwadabe ya maye gurbin dana adana Burodami Debisi a ciki, harya samu matsayin da shi kanshi Burodami Debisi bashi da irinshi. Yanzu kuwa da Gwadabe ya riga ya lasamun giyar sonshi na shiga mayen ƙaunarshi jinshi nake tamkar numfashina, ko kuma bugun zuchiyata, ina ma mijina irin son da har abada bazai iya samun macen da zata so shi kwatan son da nake yi mishi ba. Muryar mahaifiyata ne ya katsemun tunani, cikin ƙwarewa a yaren yarbanci ta soma magana kamar ba bafulatana ba. "Ai aikin gama tuni ya gama. Abinda zai faru ya faru. Jabu tayi aure harda albakar aure. Shima Debisi yayi aure harda ƙaruwar haihuwa. Ni ina ganin Toyosi ki yi haquri ki kawar da wannan batun. Kai kuma Debisi aure ai cike yake da ƙaɗdarori iri daban _daban. Ita kanta Jabu kana ji da ganin irin matsalolin da take fuskanta da dangin mijinta, auren ba daɗinshi take ji ba ana dai zaune zaman yara ko ba haka ba Alima?" Ta kai dubanta kan Iyaa Kokodeen wacce ainihin sunanta Halima, to a
Chapter 24 · 0% Book details