← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 231 OF 237

Sashe 231

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kwance nake a ɗaki idanuna a lumshe, bayana kamar zai dare gida biyu dan azaba. Tun cikin dare ciwon bayannan ya tashi mun dan ko runtsawa ban ba. Ban kira Usman na sanar mishi ba gudun kar ya baro aikinshi na dare ya dawo gida. Hassan ne ya shigo da gudu ya faɗo kaina. "Umma kinga Alhaji ƙarami yana mun gwalo ko?" Da ƙyar na buɗe idanuna na dubeshi. Wai baka ga Rumaisa'u na bacci bane so kake ka tasheta kai da baka da girma, yanzu Alhaji ƙaramin ka kawo ƙara, ina Halima ta barku kuna wasan banza?" Kafin ya bani amsa Nana ta shigo hannunta riƙe da kofin tea yarinyace ƴar hekara uku ƙanwar Alhaji ƙaramice, yayar Rumaisa'u kuma. "Umma abinci zanci" Hassan yi maza ka kirawo mun Halima yanzu." Na dubi Nana nace. Bari Halima tazo ta baki abincin, ku da in ba makaranta kuka tafi ba bakwa barin mutum ya huta Kafin in rufe bakina sai ga Halima ita da Usaini da Hassan" "Anty gani. Naga har yanzu baki fito ba. Kuma Abba ya kusan dawowa." Agogon dake manne a bangon ɗakin na kalla ƙarfe takwas na safe. Kiba Nana abinci, ki ɗauki Rumaisa'u da su Hassan kuje can ɗakinku ku Zauna bana jin daɗine zasui ta damuna." Ina gama faɗa mata hakan na miƙe da dabara na shiga kitchen. Dankalin turawa Halima ta fere ta tsane a kwalanda shine abincin mu na karyawa yau dake manne a taswurar girkin gidana. Mai na ɗaura a wuta na zuba dankalin. Na sake ɗaura ƙaramar tukunya na haɗa kayan chai tea na jama'ar india. Na gama zuba komai a kula kenan na jiyo sallamar Abban yara a falo, tare da hayaniyar yaran sunata mishi oyoyo. Ni dai ina tsugunne bayana ya kage nama kasa ɗagowa balle har in fito. A haka ya shigo ya sameni yana sanye da lap kot ɗinshi ta likitoci. "Subhanallaah Habibty lafiya na ganki a haka?" Ya faɗa cike da kulawa da tsantsar damuwa. Tallafoni yayi jikinshi da ƙyar muka karasa ciki. Baku tambayeni ƙiba ba hahaha ƙiba sai abinda ya ƙaru akan na da hutu da gogewar rayuwa yasa na zama kyakkyawa sosai. A bakin gadon ɗakinshi ya zaunar dani. "Meke damunku haka, ai ni na ɗauka ma zamu haɗu a asibiti har ward ɗinku na je ƙawarki Sabitri tace mun baki zo ba, kuma ta kira wayarki a kashe. Ba morning kike dashi bane?" Duk wannan maganar da yake yi mun hidima yake yi dani, ya kwantar dani, ya samun fullo ta bayana kamar yadda yake yi mini a duk sanda wannan ƙaddara ta ciwon baya ta tasanmu. Duk bincike, da kwarewa ta likitocin india, da irin kayan aikin da suke dashi wallahi sun kasa samo maganin ciwon bayannan nawa, hoto babu irin wanda ba'ayiba ba'a ganin komai, magani ko nasha sai dai ya lafar da ciwon. In kuwa cikine dani bana iya moruwa wannan dalilinne yasa Usman yasa aka juya mun mahaifar tunda muna da yara biyar ai sun ishemu. "Sannu kinji, amman me yasa baki kirani ba, kuma kika wani shiga kitchen kina haɗa kayan kari. Ai da kin barshi ko tea inna dawo sai in dafa mana ba, ko girkin kike so ba inayi muku ba?." Miƙewa yayi ya ɗakko man zafin da in ciwon ya tashi ake mun masach dashi ya shiga yi mun masach ɗinnan. A kife fuskata take kafin ya gama mun na jiƙe fulo sharab da hawaye. Azabar tana da yawa ainun. Wayata ce tayi ruri a gefen gado. "Ga Hajja Mama na kiranki, bari in ɗauka nasan ba lallai ki iya magana ba" Kai kawai na ɗaga mishi. "Hello Hajja Mama barka da safiya" Daga cikin wayar tace. "Likita bokan turai. Ya gida, ya jikokin nawa?" Murmushi yayi yace. "Suna can ɓarayinsu ai da suna jin na ambaci sunanki zasu soma ihu dake uwar ba lafiya wallahi nima yanzu dawowata daga aiki kenan, ita ko aikin ma ba zata samu zuwa ba" "Assha wannan ciwon baya sai adda'a kawai. Anyi na asibitin, anyi na hausan abu yaƙi ci yaƙi cinyewa. Sai dai muce Allah ya dubeta ya bata lafiya kawai. Kai wannan yarinya tana ibadar Allah. Dama tsintsiyar ƙamshine (turaren wuta ɗan tsinke) masu shaguna suka soma sanarwa yayi ƙasa shine nace bari in kira in sanar mata, to ashe ita babu lafiya ma." Usman yace. "Babu damuwa ai ko Halima sai ta je ta saro tunda tare suke zuwa. Kin turo sunayen waɗanda kuke sonne?" "Na turo likita bokan turai. Muna godiya sosai da irin gudunmawar da kake bama Iyabo, dama mu kanmu mungode ƙwarai Allah ya barku tare har ƙarshen rsyuwarku. Jiya take sanar dani zaku sake zuwa Umara nace baka gajiya ne?" Dariya kawai yayi yace. "Sabida ciwon bayannan nata ne shi yasa nake yawan kaita ka'aba tana roƙon Allah ya yaye mata, in kuma bana warkewa bane Allah yasa shine silar shiganta aljanna. Irin na mata mai farfadiya da ma'aikin Allah ya shaida mata wannan ciwon shine silar shiganta aljanna" Sun ɗan jima suna tattaunawa. Kafin su kai sallama ya ajjiye wayar. Idanuna a lumshe suke amman ba bacci nake yi ba. Ji nayi ya fita, bai jima ba ya dawo da abinci da tea. "Taso kici abinci sai ki sha magani ki kwanta. Zan kira asibitin da kaina in sanar musu baki da lafiya." Sai da ya taimaka mun na samu na iya zama na jingina bayana a kan gadon. A hankali nake cin abincin mu na ɗan taɓa hira, duk da rabi da kwatan hirar ƙorafine akan ban kirashi a waya na sanar mishi ba. Matarshi data kirashi a waya ne ta ceceni ya fita amsa wayar. Sabida karamcinshi baya iya amsa wayar matarshi a gaban ɗayar matar tashi. Asma'u uwar kishi da raina ɗan adam kenan. Na rasa dalilin da yasa matan Usman suke kishina haka. Akan zamana tare dashi a nan da komawata makaranta an sha artabu dasu sosai da sosai, Alhaji Baba ne yake taka musu birki. Dan a baya babu irin magiya da rarrashin da bai yi musu ba akan su bishi su dukka su dawo can da zama sabida suntirin yayi yawa. Ko wacce ta nuna ita tafi son aikinta ba zata iya tafiya ta bar aikinta ba. Ko zuwan da suke yi in anzo da ɗaya azo da ɗaya da ƴar suka yarda shima a cikin ɓacin rai suke yi. Ni sai daga baya ne yake bani labarin komai da zama yayi zama, ya kuma bani labarinshi tun daga ƙuruciya har girmanshi, da rasuwar mahaifiyarsu. Alhaji Baba ma yace duk su tawo Indian tare da yaran nasu. Sai suka nuna su sai dai ni in dawo duk mu hadu mu zauna shine abinda suke so. Irin muguntarnan ta mata na ɗabi'ar kowa ya rasa. Shi kuma Usman ya nuna baisan wannan ba. Shikenan al'amuran gidanshi suka rincaɓe. Duk haihuwa biyu da nayi a can Gombe nake yin wankan jego a gidana. Haihuwar Alhaji ƙarami dukkansu basu zo sun ga yaro ba, sai dai a waya da sukai mun barka. Inata saka idanu inga ranar suna zasu zo ayi hidimar komai dasu, nanma shiru. Hajja Mama ta tambayeni ko sunzo barka na faɗa mata basu zo ba. Nima kuma da yace mun inje bayan suna a lokacin muna shirin komowa nace mai bazan je ba. Ya tambayeni dalili na faɗa mishi. Dan yasan bana musu dashi, bani da fitina akan kishi. A gaskiya ya ɓatar musu sosai ya ci musu. Haka muka dawo India ban sake shiga Najeriya ba. To a Umara na soma ganin hajiya Suhailat taje daga najeriya nima munje daga india, naga kishi irinna mata dan so tayi ita ta kwace mijin acan. Nima anan sai na botsare nace bansan wannan zance ba, dole haka aka shiga rabon kwana a hotel kunji wani kudurar Allah fa. Naga kishi, naga makirci iri da kala, kunsan larabawa akwaisu da wata baƙar zuchiya akan kishin abinda suke so. Ga Iyabo kuma da son soyayya nima. Gaga gaga muka gama ibada tayo Najeriya muma muka koma India To haihuwata ta biyu dai dasu akai taron suna sunzo. Haihuwata ta uku kuma ni banje ba zamana nayi kawai anan. Wannan tsawon lokacin sau biyu rak na taɓa saka matanshi a idanuna. Bayan ya gama wayarshi ya shigo da nashi abincin yana ci muna hira shine yake sanar dani Hajiya Asma'u zata je umara itama zamu haɗu acan. Murmushi nayi nace Allah dai ya nuna mana, babu damuwa " A baya ya bani labarin mahaifiyarshi margayiya. Ya bani labarin gabaki ɗaya kab rayuwarshi. A wannan lokacin ni kaina naso ace ina da ɗan labarin da zan tsokata mishi amman ina, ƙwaƙwalwata a juye take bata iya gane komai bana fahimtar komai. Kwanana biyu a gida a rana ta uku na koma bakin aikiba a asibiti ni nurse ce ba likita ba. Bayan wata ɗaya muka wuce Umara yaran muka kaisu gidan Mus'ab da aikinshi yake Tamil. A Umara Hajiya Asma'u ta so kwata mun irin na Hajiya Suhailat ni kuma nace ba za'ayi haka ba ni naci girman ita ta riƙe mijin Hakan kuwa akayi kwananmu goma sha biyu jirginmu ya ɗaga, dole ƙanwar naƙi itama ta wuce Najeriya. Muna dawowa muka ci gaba da aikinmu dake asibiti ɗaya muke aiki a nan Geetanjali hospital Rajasthan, ɗayane daga cikin manya manyan asibiticin da ake ji dasu a fadin duniya ma. Wannan abun ma yana sake takaitar kishiyoyina Ku dai rayuwa tai ta garawa tana murtsuwakawa. Wata rana kwatsam sai ga kira daga Najeriya Allah ya amshi ran Alhaji Baba Allahu Akbar. Iya tashin hankali Usman ya shiga dan wata iriyar shakuwace ta musamman a tsakaninsu, kasancewar shima yana son su sosai, kuma soyayyar da yake ma mahaifiyarsu itac kacokan ta dawo kansu. Nice na dinga tausarshi da bashi kalma. Ai kuwa nan muka shirya tafiya, sai ranar uku muka iso a nan gidan Alhaji Baba muka sauka dan ko buɗe gidana ni banyi ba. Muka shiga karɓar gaisuwa, baƙi sukaita shigowa daga gari _gari dan familynsu Family ne mai girman gaske. Ina zaune a cikin mata Hassan ya shigo a lokacin shekararshi goma sha bakwai sun riga da sun gansame yana aji na biyu a jami'a kasancewar karatunsu nacan ya bambamta dana gida Najeriya." "Umma Abba
Chapter 231 · 0% Book details