← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 237

Sashe 68

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokaci É—aya taji kishin Iyabo ya soki murfin zuchiyarta fiye da kishin wacce za a haÉ—asu zaman kishin na gasken_gasken.
Bata sami zarafin furta mishi kalma ba Auwala da Anty Badi'a suka shigo a tare.
"Hadiza in kin shirya muje Yayanku ya rage mana hanya ko?."
" to"
Ta furta tana kallon Gwadabe, wani irin kallo daya kasa fahimtar fassararshi.
A kunyace ya gaishe da Anty Badi'a, ta amsa cike da kulawa.
"Gwadabe maza muje Mammada na jiranmu kasan fa yau muna da aiki." Cewar Auwala kenan. Kafin ma ya miƙe Malam Magaji ya iso dokin kofar yana faɗin.
"Yarannan har yanzu basu wuce aikin ba, Auwala me kuke yi a ƙunshe a ƙurya haka?" Da sauri suka fito, sumi_sumi sukai ma iyayen sallama suka fice a gidan. Cikin sa'a Gwadabe ya gwada sake kiran layin Shafa ya samu a buɗe. Sai dai harta gama kuka ta tsinke ba a ɗaga ba. Yana sauke wayar a kunnenshi sai ga kiran Tamu ya shigo.
"Abokina yau kaine da kira sassafe haka, ya kwanan iyalin kuma?' Cewar Gwadabe daya tari numfashin abokin nashi ta hanyar rigashi magana. Ajjiyar zuchiya ya sauke yace.
"Tun jiya Ayashe ta sanar dani Shafa nata faman kuka ta kulle kanta a ɗaki. Ko da aka wayi safiyar yau taƙi cin abinci, taƙi zuwa wajen aiki. Shine nasa ita Ayashe tai kiranta dan inji menene. To ta dai ƙi yin magana ma, bansan ko kana da masaniya akan kukan ba, kasan yarannan fa da zafafawa akan soyayya, dan naga ta ɗauki lamarinka da girma. Kasan mata da surutu ina jin labaranka sosai ta bakin Ayashe" Jim Gwadabe yayi kawai yana mamakin halin da Shafa da Hadiza suka shiga a kanshi, ya ɗan shafo ɗan siririn hancinshi tare da shiga zancan zuchi.
"Ohh ni Gwadabe ni ba kyau mai suna kyau ba, ni ba tsayi ba, ga tumbi, ga ƙaton kai. Amman akaina waɗannan matan suke shiga damuwa haka? Dama_dama Iyabo na cancanci ta soni, duba da yanda tasha naci a wajena, da irin yanda na jajirce kan soyayyarta. Amman waɗannan haɗani dasu dukka akayi, bawai ni nace ina sonsu ba."
"Kana jina kayi banza dani Gwadabe ko network ne, ko ko dai wani rashin kunya Shafa tayi maka?" Tamu ya tsinke mishi zaren zantuttukam zuchin shi. Da sauri yace.
"Kai kasan komai Tamu akan Hadiza da Baba Magaji ya bani bayan na baro najeriyane. To ita Hadiza bata san da zaman Shafa ba, kamar yadda Shafa bata san da zaman Hadiza ba." Nan dai ya kwashe labarin duk yadda ta kasance musu a jiyan. Tsaki Tamu yayi kawai tare da cewar.
"Shirmen banza harma ka tunzurani ƙila saina zaneta ma. Yanzu akan wannan maganar ne duk ta takure kanta?"
"Kul wallahi kar ka soma dukan mun mata ni dai na faÉ—a maka dan ubanka" Dariya suka yi Tamu yace.
"Wannan siriki kwai fitsararren maras kunya" Dariya suka sake sawa, kafin Tamu yace.
"Yaushe zaka shigo mana najeriyar ne Gwadabe, ka gujemu. Ko dai har yanzu damuwar rashin Iyabo ne ya hanaka zuwa? Mu kuma cike muke da kewarka, ko babu komai ya kamata kazo kaga yara" Gwadabe yaji wata kewa ta kamashi, take yaji yana sha'awa da son ganin abokan nashi da ma yaranshi.
"Tamu zan zo zuwa ƙarshen wannan watan da muke ciki, kaga yau wata yayi goma biyar, yana kaiwa ƙarshe zan zo in duba ku. Ya yaran?"
"Yara kowa lafiya lau sunata karatunsu hankali kwance. Toye ma dana shiga ƙauye naga yayi noman masara shi da yaron Bara'u baka ga yanda masarar tai kyau ba. Na lura yaron yana da mai da kai akan abinda yake gabanshi, shi kanshi Bara'u ya yaba" Sun jima suna hirarsu ta abokai kafin daga bisani su kai sallama. Ko da yaje wajen aiki daya fito cikin ramin haƙar zinariyar dan hutu sai ya kira lambar Shafa, bata shiga ma baki ɗaya. Da ƙyar ya samu dai ta shiga, kuma yaci sa'a aka ɗauka. Daga nan zancan fishi ya ƙare, bayan ƴan bayanai daya yi mata, da kuma kalamin kwantar da rai, sai suka balle da hirar soyayya, wanda rabi da kwatan hirar Shafa ke yinta, shi dai yana dai ƙarfafa mata guiwa ne. Bayan sun yi sallama ya kira Hadiza ma yaji yaya jikin nata tare da ɗan taɓa hirar da rabinta da kwatanta labarin zafin da taji a zuchiyarta ne, shi dai aka barshi da aikin rarrashi.
Jigum ya zauna yayi tagumi bayan gama wayarshi da Hadiza. Kanshi ya ɗauki caji ainun. Harga Allah shi dai bazai iya gane yana son su Hadiza ne, ko kuma yana kallon darajar waɗanda sukai mishi tayinsu ne ba. Domin mace ɗaya tilo Iyabo itace a zuchiyarshi abadan. Yasan abune mai wuya dawowar Iyabo cikin rayuwarshi. Yana fatan inya shiga Najeriya Allah ya haɗa fuskokinsu ko da a hanya ne. Yana kuma da burin son ƴaƴanshi su yi rayuwa a gefenshi damin ya ɗauke musu raɗaɗin maraicin uwa a rayuwarsu. Mammada ne ya dafa kafaɗarshi, yana zaune a gefenshi shi bai ko ji tawowar tashi bama. Abinci ya miƙa mishi, garau_garau irinta leburori irinsu, yasa hannu ya amsa.
"Menene Gwadabe, kaddai batun Hadiza ne duk yabi ya dameka?"
"A'a wallahi Mammada tunanin rayuwa kawai nake yi da rashin daÉ—in aikinnan, tare da tunanin yarana da basa kusa dani anan" ÆŠan murmusawa yayi, sai da ya ciko garsu_garau a cokali ya danna a bakinshi dam kafin yace.
"Wannan ai mai sauƙine Gwadabe, kai da kake jarumi me auren mata biyu, ai zasu riƙe maka yaranka wannan bama wata matsala bace" Abincinshi yaci gaba da dannawa a baki bashi da damuwar komai. Sai Gwadabe yaji dama ace shine Mammada da yaji daɗi. Wunin wannan rana da tunanin Iyabo da yaransu Gwadabe ya wuni. Yayi ƙoƙarin samun layin Bara'u ma dan ya sanar mishi da batun zuwanshi, amman dai basu sami damar jin juna ba. Kamar dai yadda aka saba bayan isha Gwadabe ya aiki yara su kai mishi kiran Hadiza. Yana zaune a saman dakali tazo ta sameshi, bayan sun gaisa yayi mata ya jiki, sai shiru ya biyo baya. Dukkansu a cikin tarawa da ɗabewa suke. Sai dai tunaninsu ya sha banban dana juna.
"Menene ya dameka wanda harya kasa ɓoyuwa akan fuskar taka, ko baka samu damar jin muryar Shafa bane?" Ɗagowa yayi suka haɗa idanu. Ɗan gajeren murmushi yayi mata tare da cewa.
"Babu mamaki dan naji sunan Shafa raɗau a bakin ki, tunda Malam yasan sunan. Yaya jikin naki da sauƙi, kuma kinsha magungunan da suka baki? Ya jero mata tambayoyin da yake tunanin zasu jaye hankalinta daga barin batun Shafa. Amman sai ta jefo mishi wata tambayar da cewa.
"Ni ko zan so ganin tsohuwar matarka ko da a hotone domin inga da abinda tafi sauran mata" Ta ƙarashe maganar da taɓe bakinta. Anan ne taga ya gintse fuskarshi dukkan annurunshi ya dakata.
"Kar ki kuma kawo maganar Iyabo anan wajen. Ki tsaya dai iyakar matsayinki da kike dashi a zuchiyata. Batun ita kanta Shafa ki shafe shi a kan ki, ni dake mu tattauna akan iyakar abinda yake gabanmu. Kuma ko ita Shafa in tayi mun magana a kan ki, ko Iyabo, dakatar mata zanyi domin babu abinda zaku ji daga gareni. Dukkanninku kuna da matsayi na musamman a zuchiyata" Ajjiyar zuchiya ta sauke. Ranta yayi matuƙar ɓaci ainun, idanunta kuma sun rufe da kishi. Amman a zuchiyarta tasan ita ke da laifi da bata cakalo zancan ba da ba'ayi ba ma balle har ya tsayar mata.
"Karshen watannan inaso zan leƙa Najeriya in dubo su Babala da yaran wajena in Allah ya nuna mana da rai da Lafiya." Cikin dakiya tace.
"Allah ya nuna mana lokacin" Ya amsa mata da "Ameen" Shiru ya sake wanzuwa a tsakaninsu na kusan minti biyar cur, Gwadabe ne ya daure yace.
"Kishi yau ya hanaki yin magana ko Hadiza? Bansan me yasa kike damun zuchiyarki har haka ba wallahi. Mata ku dinga sassautama rayukanku akan kishi ko a zauna lafiya " Kallonshi tayi ido a cikin ido tace.
"Ashe kishin abinda kake so yana iya zama illa ni ban sani ba? Ai na É—auka wanda yake da girman daraja ake kishi ba wanda bai isa ba" Kai ya dafe tare da lumshe idanunshi.
"Yi haƙuri Hadiza kinji. Bance laifi bane dan kin nuna kishinki a gareni ba. Amman tunda lamarinnan ya faru baki bar zuchiyata ta zauna lafiya ba. Kinga na dawo a mugun gajiye yau. Hira dake yana warware dukkan gajiyar dana kwaso. Amman yau ke da kan ki kike shirin labto mun wata gajiyar ta daban ma" Yayi maganar da irin sigar daɗin bakin maza mai zurma matan da basu gane kan rijalu ba ( Ummu nabeeha ana magana) Jin ya faɗi haka ne yasa ta ɗan sassauto har suka taɓa hirar dai ba wani armashi.
Haka kwanaki sukaita tafiya dare ya shigo, haske ya maye gurbinshi. Gwadabe sai ɗan siyan tsaraba yake yi yana adanawa kafin zuwan lokacin tafiyarshi. Baba Fhatsima itama sai shirin tafiya take ta tayi. Matan gidan kuwa sai tashin hankali ya ƙaru a garesu. Cikin kwana goma suka shirya tsab da yamma Tasi'u ya ɗaukesu izuwa Airport. Al'amarin daya mugun tada tarzoma mai girma a gidan bayan tafiyarsu Malam. Dan Baba Asshi tana kuka a tsakar gida ta dinga kiran iyayen Baba Fhatsima tana kunduma musu ashariya. Hakanne ya tunzura Hadiza da su Auwala da shigowarsu kenan. Al'amarin dai baiyi daɗi ba sam, Yaya Tasi'u ne ya dakatar da faɗan ta hanyar yin hargagi ga ƙannen nashi akan kowa ya kama gabanshi. Dan samarin ɗakin Baba Asshi ma sun shiga rikicin.
"Ku yi haƙuri Baba. A dai dinga kai zuchiya nesa. Ya kamata ace yanzu maƙota sun dena jiyo sautin faɗa da ashariya daga gidan Malam. Wannan al'amarin tun muna yara aketa faman yinshi har yanzu tsugunne bata ƙareba. Ya kamata ace mun haɗe kawunanmu tun kafin wankin hula ya kaimu ga dare"
Cewar Yaya Tasi'u kenan cikin takaici da baƙin cikin irin rarrabuwar kawunan dake cikin gidansu. Inama zasu yadda a haɗe a zama abu guda. Amman kash an bar kari tun ran tubani. Malam shi ke da sa sannu a faruwar komai, kuma yafi kowa da kowa son ganin ya haɗe kan ahalinshi sun dawo abun sha'awa a yanzu da yake ganin kamar wankin hula na shirin kaishi dare fa"
Chapter 68 · 0% Book details