← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 237

Sashe 155

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da ba lafiya ishasshiya gareni ba bada kai nayi bori yahau. Muka raya wannan dare cike da aminci. Washe gari zuchiyoyinmu wasai kamar ma ba mu ba. Bayan Yaya Hamma ya karya yana shirye tsab yace. "Bari inje wajen Baɗejo in karɓo kuɗinn da nace zan biyaki na kayanki da kuɗaɗenki da aka sace. Sai dai baki faɗa mun nawa ne kuɗin ba. Shagwaɓe mishi na kuma yi tunda na fahimci shagwaɓe na daga cikin abinda ke kunna shi. Fuskata ya shafa yace. "Anya yau zan iya fita aikin ma kuwa ba zama zanyi inyi jinyar matata ba?" Da naji ya faɗi haka saina sake matseshi a jikin kujera na soma mishi wasannin da baisan dasu ba sai haɗuwata dashi. Nan muka sake lulawa duniyar ma'aurata. A wannan ranar dai Yaya Hamma saida na roƙeshi ya yarda ya fita. Bayan ya caskemun kuɗin kayana da kuɗin da aka haɗa aka sace mun. Ya ƙaramun da Nera dubu ɗari da hamsin. Ya ƙwaɓeni sosai akan ka da in sake kowa yasan labarin kuɗin daya bani, dan Saniya ƙatuwa ya siyar ya bani kuɗin dukka. Naita mishi godiya na rakashi har ƙofar gida. A tsakar gida naci karo da Uwani. "Uhm Tattabara Uwar soyayya har an shirya da halama komai ya dawo kan seti kenan?" Hannunta naja muka koma ɗakina na danƙa mata wannan kuɗi a leda na labarta mata yadda muka yi ya bani kuɗin. "Kin kyauta ko babu komai kaɗan zaki cika ki ɗakko dila kasuwancinki yaci gaba. Wannan karon me zaki saro to?" To ina ganin kayan yara ma sun wadatar na maza da mata. Tunda ya farfaɗo mun da jarin kinga Shikenan. Uwani tace. "Akwai dubu talatin ɗinki a hannuna kuɗin hayar gidanki du ɗakuna ukun an zuba haya. Kinga bama saina ara miki ko sisi ba. Dana koma Kano zan kira Faty muyi magana, zanje hajj kam in tura mata kuɗin. In kayan sun iso zaki ganni ni da kaina zanzo in kawo miki. Amman Iyabo me zai hana ki shiga ɗakin Hama ki dubo turamen zannuwanki ki kwashe. Mitsiyaciyar dai nasan da kuɗin zata tafi rugarsu" A_a Uwani tunda dai Yaya Hamma ya biyani kuɗin komai harda ƙari bana son in kunno wata fitinar" "Bari kiji Iyabo gobe zata iya miki satar da ta fi wannan muni, sai kiyi yaya kenan in tun yanzu baki ma tubka hanci ba?" Nisawa nayi nace. Idan ta kuma zata gane kurenta kinsan Allah inna zauneta saita amayar da ƴan hanjinta." Nan muka taɓa hirarmu ta yaushe gamo, saida Yafendon tazo tayi mun ya jiki sannan na tuno da ciwo ashe nake. Da safe dai nasha magani, Yaya Hamma ya ɗigamun na idanun yana ta faman yi mun sannu ni kuma inata langwaɓewa. Da yamma na sa mayafina muka je gidan Dada ni da Uwani. Hmm kunsan ƙauye da gulma ashe Dada ta riga da tasan duk abinda akayi sarai, bata shiga zancan bane sabida tasan Yafendo ba zata bari a cutar dani ba, haka shi kanshi Hamman bazai cutar dani yana cikin hayyacinshi ba. Nasiha da ban haƙuri ta dinga yi mun, tare da jajanta mun bisa asarar data hauni. Da yamma sakaliya muka koma gida muka tarar ƙanwar mahaifiyar Hama tazo an turota jin ba'asi. Su Baɗɗo suna tsakar gida suna aikace_aikacensu muka wuce, matan gida kuwa in banda Safiya babu wacce taimun ƙaƙa jiki, mazajensu dai sunzo sun dubani, amman dake su a bayan Hama suke shi yasa haushina ma sukeyi. Washe gari sassafe Uwani ta kama hanyar Kano. Wannan karonma ta sari man shanu a hannun Baɗɗo mai yawan gaske. Gaga_gaga soyayyarmu ni da Yaya Hamma ta ƙara burunƙasa matsawar da Hama tayi saita bamu damar sake shaƙuwa da junanmu, mukaita ragargazar amarci. Yaranta kuwa a cikin kwana biyar da tafiyar uwarsu harsun sauya. Na tsefe musu kansu na wanke musu tas, na musu kitso, kullum saina musu wanki tare da Babansu da Yafendo. Gari ya ɗauka amaryar da Hamma ya auro a birni ta mallakeshi ta rabashi da Matarshi. Shima har tareshi akeyi a hanya ana mishi magana akan ya daure ya dawo da Hama. Abu ɗaya yake faɗa musu Yafendo ce ta koreta ba shiba, bashi da damar tsallake maganar mahaifiyarshi. Ni dai a cikin sati biyu da tafiyar Hama har wani haske da ƙiba nayi, kullum Yaya Hamma sai ya riƙo mun kayan daɗi yake shigowa, ga wani irin tattalina da yake yi. Roƙonshi nayi akan inaso in soma koya ma Baɗɗo da Safiya karatun Qur'ani a tsakankanin magriba zuwa isha. Babu musu ya amince mun nake koyar dasu a tsakar gida. Abu kamar wasa ba sai har matan maƙota suka soma shigowa ɗaukar karatu ba. Ya zamana ina koyar da mata ashirin karatun Alkur'ani da kuma abinda ya danganci tsarki, da alwala. Abun mamaki da yawansu basu iya wankan tsarki ba, ƙalilan daga cikinsune suka iya sai gyara da akayi musu. Ina jin daɗin ɗalibaina suma suna jin daɗina. Wannan makarantar daren saita sake debe mun kewa, ya zamana kuma an sanni sosai a ƙauyan. Wata ranar juma'a da rana babu kowa a gidan ina kwance ina karanta littafin Hausa mai suna Allurar cikin ruwa na Bilkisu funtua . Bayan na gama bitar fassaran hadisin da zamu yi da ɗalibaina. sai kawai naga an wangale mun labude. Ɗagowar da zanyi sai naga Hama ce riƙe da labulen. Duk ta rame idanunta ya zurma. "Kinci nasara a kaina gaki ga gidan Hamma. Ni zan bar miki gidan baki ɗaya kayana nazo kwasa. Amman ki sani babu ke babu kwanciyar hankali sai kin fita tsirara a haukace daga ruggarnan" Ta saki labulen tana wata dariya. Jikina sai naji ya mutu murus na rasa kataɓus. In yinƙura in tashi na kasa, inaji Hama nata kwaramniya a tsakar gida. Ashe kayanta ta kwashe tsab saida Yafendo ta dawo muka gani, ko tsinke Hama bata bari ba. Da Hamma ya dawo da daddare ya sameni a ɗakin Yafendo ta labarta mishi hama ta kwashe kayanta. Duk saiya shiga damuwa ainun ina lure dashi. Ko da muka koma ɗaki kasa cin abinci ma yayi, ƴar hirar da muka saba ma yau babu. Yaya me zai hana kaje kayo bikon matarka ta dawo tunda kana son matarka ga yara a tsakaninku" Anan naji abinda ke cikinshi. Cemun yayi. "To ya zanyi Dada taƙi fur. Kullum inna shiga saina roƙeta akan tayi haƙuri ta yafe ma Hama ta dawo ɗakinta ko dan sabida yara, maganar gaskiya nima inason ta dawo. Sai tace a'a" Shiru nayi ina kallonshi da mamaki bil haƙƙi a cikin damuwa yake. Saina sanya salama a zuchiyata nasan lafiya lau yake zaune da matarshi kafin zuwana, har tatsar nono tare suke yi, tare suke duba dabbobi marasa lafiya. Bazanyi tsammanin ya soni fiye da Hama ba. Miƙewa nayi zuruf. Yayi saurin kamo hannuna muka ƙurama juna idanu, kishin sai neman ingizani yake yi, nifa sai naji nama tsaneshi ni kam, kamar in dira a wuyanshi haka nake ji. Ina zuwa yanzu zan dawo" Na furta a raunace. Idanu ya lumshe ya miƙe tsaye ya shige jikina ya ƙanƙame ƙuguna ƙam. Runtse idanu nayi kawai kishi nata ɗawainiya dani, sha'anin maza akwai munafurci a ciki. Babu mamaki acan ɗakin Haman haka yake mata irin wannan soyayyar koma fin hakan. Ai da wannan tunanin ya bijiro mun saina sa hannu bibbiyu na ɓamɓareshi a jikina na fice, inaji yanata kiran sunana ko tankashi bamba. Ɗakin Yafendo na shiga har tayi shirin bacci. "Jabu lafiya kuwa" Tsugunnawa nayi nafi minti talatin ina bata baki akan ta yi haƙuri Hamma ya dawo da matarshi. Ta dinga kwatantamun in bari kawai tunda Hama da kanta ta yanke hukuncin haƙura da shi. Na kafe akan ta dai yi haƙuri. "Shikenan Jabu jeki Allah yayi miki albarka" Ameen Yafendo nagode, sai da safe" Sallama nayi mata na fita. Ina zuwa daidai bakin ƙofar ɗakina sai naji kamar wani abu ya shiga jikina haka. Nayi saurin runtse idanuna ina karanto duk adda'ar da tazo bakina, har saida na samu nutsuwa. A sanyaye na shiga ɗakin inaji tsigar jikina na tashi. A kan gado ɗare_ɗare na samu Yaya Hamma idanunshi biyu amman ya shiga zurfin tunani juyo kai yayi muka haɗa idanu. Hannuwanshi biyu ya miƙo mun halamar inzo in shiga jikinshi. Basarwa nayi na samu jefen gado na zauna. Hannayena duka biyu Yaya Hamma ya riƙo yana murzasu yana daga kwance, suna ratsani sosai. Da wata murya sassanya yace. "Ina kikaje kika barni ni kaɗai cikin kewa" Idanuna na lumshe a zuchiyata nace. Lallai kishi aikine ja, banga laifin Hama ba da taita hauka lokacin da za'a auroni. Bansan sanda nace. Kewar uwar ƴaƴanka data bar gidanka ko?" Da sauri ya miƙe zaune banyi aune ba ya soma aiko mun da saƙon kai tsaye, tun ina gane yaren har na dena gane komai ya fahimci raina ya ɓacine da damuwar daya nuna akan matarshi a gabana, sai ya zage ya dinga mun abubuwan da yasan inaso sosai. Sai da komai ya lafa kishin yaci gaba da nuƙurƙusata. Shi fa gogan yama yi baccinshi niko idanuna biyu ina kallon hawa da saukan numfashinshi. Ina aiyanawa a raina, ko wanne irin kalami yake ma Hama oho, gashi ya iya soyayya mai sanyi da tsaiwa a rai. Nina ɗauka irin wannan soyayya sai mutanen birni, ashe abun baiwane daga Allah. Sannan ya danganta da yadda namiji yake son mace. Su fulani Allah yayi su da iya soyayya da son mace sosai. Sai Allah ya basu basirar iya tattalin macen gashi dai rayuwarsu a ƙauye, mazan kuma rabin rayuwar a jeji ma suke yi. Wannan dalilin yasa matan fulani sunansu yai shura wajen kishi da yima kishiya mugun asiri. Ajjiyar zuchiya nayi na shafi fuskar ɗan fulanina ina murmushi. A haka bacci ya kwasheni. Amma me zai faru ina cikin bacci sai naji kamar ana tsaye a kaina. A razane na tashi zaune dafe da ƙirjina, hakan yasa Yaya Hamma ya tashi shima, yana riƙe dani ni kuma na runtse idanuna Wannan inuwar tana saitina. A zahiri ina ganin inuwa, a cikin jikina kuma ina jin halamar mutum a tsaye a kaina. Yaya Hamma yana tambayata menene, ni dai adda'a nake yi babu ƙakƙautawa da ƙyar na buɗe idanuna sai naga wayam babu wannan inuwar. Ajjiyar zuchiya na
Chapter 155 · 0% Book details