Sashe 78
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
8 "Iyabo. Abunda nake so dake shine ki kwantar da hankalinki sosai kiyi aikin ki yadda ya kamata. Kije ki soma wanke bayan gidun falon ƙasa dana nuna miki. Kiyi amfani da duk man wanke bayan gida dana nuna miki. In kin gama sai in koya miki yadda zaki yi shara da injin." Jikina a mace na gangaro ƙasa. Da wani gansamemen Balarabe naci karo a falo. Yana ganina sai yace dani. "Shayi" Yana mun halama da hannu da sha" Take na gyaɗa mishi kai na jiya kitchen ɗin. Tea spices Takarofi ta nuna mini na dafa na kai mishi yana zaune akan kujera. Nan na shiga aikina. Sai da na wanke bayan gidu takwas, tun daga bango har ƙasa. Ina fitowa na soma shara da injin ɗin shara, kafin in gama bayana ya ƙage dan azaba. Wani ruwan fesawa Takarofi ta bani da tsumma, haka na dinga bin bangon gidan ina fesawa ina gogewa yana ƙyalli. Na goge TV, TV stand, daining table da gilasan dake saman shi. Ina cikin haka na duba agogon falon naga lokacin sallah har ya gota. Gashi banyi wanke_wanke ba, ban ɗaura girki ba. Da sauri na koma ɗaki, Takarofi ta tare ni da cewa. "Lafiya na ganki afujajan?" Sallah zanyi" Agogo ta kalla, ta dawo da kallonta gareni tace. "Kin ɗaura girkin rana ne Iyaba?" A'a" Na bata amsa. "Iyabo muje kitchen ki samu ki ɗaura girki tukunna, ko a kitchen ɗin sai ki yi sallah. Ni kuma zan taimaka miki da wanke_wanken. Ƙarfe biyar yaran gidan suke dawowa daga makaranta baki gyara musu ɗakunansu ba,. Akan yarannan za'a iya korarki." Ni dai binta nayi zuwa kitchen ɗin. Sai da na tsayar da sanwar shinkafa kaza tsab sannan nayi alwala na shinfiɗa ɗankwalina na gabatar da sallah. Illahirin jikina babu inda baya yi mini ciwo. Amman haka na tashi ni ina gyaran kitchen Takarofi na wanke_wanke. Har dai girkin ya nuna aka juye a wata babbar kula ta silver, na jera komai a teburi. Kana na wuce ɗakin yara, a hargitse kaca_kaca ina hawaye ina aikinnan. Sai da na gyara ɗakin yara uku, ko wanne da bayan gida. Ina gamawa na faɗa ɗakin matar gidan na gyara, ɗakin mijinma ni na gyara. Bayan sallar magriba kuma muka fita ta bayan gidan da tulin wankin ja'amar gidan, Takarofi na koya mun yanda zanyi amfani da injin wankin. Hannuna tsabaragen gajiya rawa suke yi. A wajen wankin na samu nayi sallar magriba, a wajen naci abinci. Bamu muka gama wanki ba sai dab isha. Ga girkin dare zan ɗaura, ga wanke_wanken abincin rana, falonma yaran gidan da samarin gidan duk sun lalata. Haka na kuma gyarawa na ɗaura girki kitchen ɗin nayi isha na jejjera kayan abinci a daining yaran gidan da matar gidan suna falon suna kallon wani shiri a talavijin. Ina shiga nayi sallar isha ai sai zazzaɓi ya rabkeni, ko ina rawa yake yi a jikina abinci ma kasa ci nayi, Idanuna sai hawaye suke fitarwa "Iyabo ƙarfe tara tayi kije ki sama yaran gidan kayan bacci, samarin gidan kuma ki fito musu da kayayyakin baccin, ki kunna ma ko wanne ɗaki turaren wuta. Ga guga fa baki yi ba, ya kamata ki gama a darennan gobe ki tashi da aikin jerawa" Ai sai na rushe da kuka.. Haba kasheni za'ayi da aiki. Wannan aiki sai kace jaka" Kafin in rufe baki naji wata murya daga ƙofar ɗakinmu ana ambaton Sheika( ma'ana tsohuwa) A zabure Takarofi ta miƙe. "Taso Iyabo kinji daure" Da ƙyar na bi bayanta naje nayi duk abinda ya dace na dawo. Ina zaune sai guga nake yi. Zuchiyata kuma ta lula tunanin Yaya Hamma, da irin yadda muka rabu muna masu begen junanmu. Idanu na lumshe ina fata da burin in zama mata a gareshi. Sai da na gama gugar nan tsab nayi wanka na kwanta. Abinci ma na kasa ci sam. Ina kwanciya wannan yarinya da Takarofi tace itama ƴar aiki ce sai gata ta shigo. Bata jin Hausa bata jin turanci sai yaren Senegal. Ƴar senegal ce, sai gaisuwar kurame mu kai ma juna. Cikin bacci naji ana dukan kafaɗata, zabura nayi na zauna. Ƙirjina sai bugawa yake yi dana ga namiji a tsaye a kaina. Murmushi yayi mun yace mun. "Uridu an ashbu shayi ( zan sha shayi) Da Wata muryarshi mai zaƙin gaske. Na fahimci me yake cewa ta dalilin shayi daya ambata. A gajiye tulus na haura kitchen ɗin sama na je na dafo mishi shayin na kawo mishi yana zaune a falo. Ina harhaɗe hanya tsabar bacci da gajiya haka na isa ɗaki na faɗa gado ban sake sanin inda nake ba, sai da muka jiyo kiran Sallah. "Iyabo maza yarannan kije ki musu wanka su saka kayan makaranta. In kika ɗaura abincin karyawa sai kiyi Sallah " Bani da zaɓi haka dole na gabatar da abinda Takarofi ta faɗa mini. A kitchen ma nayi sallah abina. Zuwa shida da rabi na gama jera komai a daining. Har matar gidan, da me gidan sun fito. Cikin harshen turanci na gaishesu, suka amsa mun da "Sabahul Noor" Na juya na barsu nan. Da duku_duku na soma bi ɗakuna ina jera musu kayansu a durowa. Ƙarfe Takwas batai musu a gidanba, masu zuwa aiki sun tafi, ƴan makaranta ma haka. Tunda na shiga aiki banfa zauna ba sai ƙarfe biyun rana na kammala komai da komai, sai guga data rage mun kawai. Itama ina idar da Sallah na shiga aiki. Yau babu abincin rana, sai na dare, na dai dafa ma yara ƴan makaranta Taliya me kifi. Na cire musu kayan makaranta, nayi musu wanka, sai suka kwanta bacci. Ragowar abincin safe naci, farfesun kaza ne da dankalin turawa, sai dafaffiyar madara. "Dake da ƙwarinki kinga har kin gama aikin ki ƙarfe huɗun yamma. Aikin yayi sauri sosai. Ina mayar da numfashi nace. Amma Mama azabar tayi yawa. Wannan aikin ai dole ya illata jikin mutum, bautar tayi yawa. Ace in ka tsaya a tsaye tun duku_dukun asuba ba kai zaka zauna ba sai huɗun yamma. Shima biyar nayi zaka tashi ka shiga hada_hadar girkin dare. Ba kai zaka samu kanka ba sai kusan sha ɗayan dare." Takarofi tace. "Wannan aikin shi ya fiye miki alkhairi. Duk yarinyar da bata zaune a gidan aiki, to yawon ta zubas take yi a gari. Kinga kuwa ai zaman gidan aikin ya fiye mata ko?. Sannan inaso in ja kunnenki in gargaɗeki. Kinga gidannan akwai Samari har su shida majiya ƙarfi. Kibi a hankali dasu, a kullum in zaki shiga ɗakunansu ki yi adda'ar neman tsari Allah ya kareki daga sharrinsu. Dan suna shigo da matan banza cikin gidannan. Naga kuma ke yarinya ce, ki tsare darajarki tunda ba abinda ya kawoki ba kenan." Shiru nayi ina nazarin kalamanta hankalina ya tashi ainun, lallai ina cikik tsaka mai wuyar fita. Wannan ai shi ake kira gidan tara. Girman gidan na soma hasasowa, da yanda nake marar ƴanci a cikin gidan. Taya zan ƙwaci kaina daga wannan sharri. Ni kaɗai a gida sai samari garada, shin in ihu nayi wazai kawo mun ɗauki ma?" Na shiga tsaka mai wuyar fita. Tunanina sai ya koma gida Najeriya. Bani da wani buri daya wuce in koma ƙasata in ci gaba da rayuwa a cikin ƴanci" Wannan tsoro da fargaba sai suka samu muhallin zama daram a tattare dani. A ranar dana cikata kwana bakwai a ranar Takarofi na tayata ta haɗe kayanta tsab. Matar gidan tai mata goma sha tara na arziki. Ni dai ina kuka muka rabu da Takarofi. Damuwa da fargaba sai suka aureni. Na wuni ina bauta, da daddare kuma tsoro ya hanani bacci. Ɗayan shashen na zuchiyata bashi da aiki sai begen Yaya Hamma. A duk dare da rana tunaninshi ne ke ɗan bani wani nutsuwa da samar min da guntun farin ciki. A baya na faɗa muku ni zuchiyata bata iya son abuba sam. Soyayyar Yaya Hamma muhalli sosai ta samu a zuchiyata. Dana tuno siririyar fuskarshi mai ɗauke da fararen idanu take Sai inji baƙin ciki ya yaye mun. Amman fa son Yaya Hamma bai taɓa matsayi da darajar Gwadabe a zuchiyata da rayuwata ba. Kawai dai ina ƙoƙarin binne sonshi ne in fuskanci alƙiblar da take daidai. Ko da zamu dawo aure misali da Gwadabe, dole sai na auri wani namijin kafin hakan ta faru. Balle bana fatan Abinda zai sa in sake kai kaina inda basu san matsayina da kimata ba." Haka dai lokaci yai ta tafiya, tunani a ko da yaushe shine abokin hirana. Dan ni da Malika bama iya hira sai dai maganar kurame kawai, kuma in ta tafi ɓangaren da take aiki bata shigowa ɗakin baccinmu sai goman dare. A mugun gajiye take shigowa, to a haka ne muke ɗan taɓa hirar da bata wuce ta minti biyar ba. Wasa_wasa watana uku a gidan aiki. Duk wata wahalar aiki, da hawa da sauka ta zame mun jiki. Kullum a cikin ciwon baya dana ƙirji nake. Abinci wannan bani da lokacin da zan cishi a cikin nutsuwa, in aiki ya caɓe mun ma sai in wuni banci komai ba. Gashi a cikin kwana biyunnan kullum sai Khalifa ya shigo ɗakinmu da daddare. Sai ya taɓa jikina a kullum in zai tasheni daga bacci. Dana soma bacci sai inji mutum a kaina. Shayi dai shayi dai. Da yana zama a falo ne in dafa in kawo mishi. Amman yanzu sai yayi komawarshi ɗakinshi dole inna dafa in shiga in kai mishi. Kullum da mace a gadonshi, babu ranar dana taɓa shiga banga mace a ɗakinshi ba. Wataran tun daga ƙofa zanci karo da rigar mama da ɗan diras a ƙasa. Haka zan ajjiye in juya. Irin kallon da yake bina dashi shi yafi komai birkita lissafina. Dalilin da ya soma sani rama kenan. Yau tun safe na tashi da faɗuwar gaba da ƙunci. Ko dana shiga kitchen ɗora abinci sai na yi zaman dirshan na saki kuka. A mugun takure rayuwata take, zuchiyata babu daɗi kaɗaici na neman haukatani. Baka da wanda zaka yi magana kaji daɗi. Baka da lambar ƴan uwanka balle kaji muryarshi ko zaka ji sanyi. Akwai number Burodami Debisi, amman Uwani ta haɗa a kayanta ta tafi dashi. Daga kaina naji ance. "Maaza?" ( Menene) Ina ɗagowa