← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 237

Sashe 20

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saye nake da doguwar rigar leshi, ɗaya daga cikin kayan da aka bani a gidan aiki. Toye na kwance a kan bargo a ƙasa yana bacci. Ƴan biyu kuma suna kan gado suna baccinsu sun sha overoll farare tas. Yaran ya zuba ma idanu da kyau sai murmushi yake faman yi. Zama yayi a bakin gadon ya ɗauki Taiwo dan tafi kusa dashi. Zama nayi ina fuskantarsu yayi kyau da yarinyar a hannunshi. Rabon yarannan ne yasa iyayenmu suka amince da aurenmu bisa dole, dan wannan rabon ka iya ajalin duk wanda ya kafe ba zamu auri juna ba. Gwadabe ina alfahari da aurenka, ina alfahari da soyayyarka gareni. Hakanne yake sa in mance da kyara, tsangwama, ko ƙyamata daga danginka. Domin kai kam ka zame mun komai, ka cike duk guraben dake da giɓi a rayuwata madallah da samun miji nagari irinka" " Ifemi ( masoyiyata) Na gode da soyayyarki, ina jinjina juriya gami da haƙurinki, samun mace irinki abune da sai an tona shi a wannan zamanin, musamman a ƙabilarku da matan yarbawa suke da zafin rai da saurin faɗa. Mala'ikun Allah ku shaida ni Gwadabe na ɗaga ƙafafuna Iyabo ta shiga aljanna, ku sake shaidawa ita da kishiya sai ta gidan aljanna, a can ma itace shugabar su " Dariya mu ka yi dukkanmu kafin ya ja fasali yace. "Ina da tarin tulin tambayoyi kin shirya?" Ahaf ni dama nasan ba zaka barni ma zuwa gobe ba. Tambayeni in baka amsa, amman kafinnan bari in kawo maka abinci, kana ci kana kora koka kola zai fi. Miƙewa nayi abincin na gefen sib a tiran silver ɗauke da duk abun buƙata. Tuwon shinkafane miyar bushasshen karkashi wacce ta ji kayan cikin rago, iyakar kayan Cikin miyar shine iyakar rabon da muka samu a raguna biyu tiƙa_tiƙa. Zuba mishi nayi na matsar gabanshi, Ajjiye Taiwo yayi tare da sakkowa ƙasa, ya tanƙwashe ƙafarshi yanata kallo ina hidima dashi. Lomar tuwon farko a bakina ya sauke mun, tare da yankan saifa. "Bani labarin tv da kafet tukunna, dan dasu na soma cin karo" Sai da na saisaita nutsuwata, na sake tausasa muryata kafin nace. Burodami Debisi ne ya sake ma Yemisi kayan ɗakinta, shine ya bibbimu da tsofaffin" Kafeshi da idanu nayi ina karantar yanayinshi, dan Gwadabe bashi da daɗi sam ta wajen kishi. Ya zafafa kishinshi sosai akan Burodami Debisi. Alhalin shi babu ni a zuchiyarshi sam, bana mance lokacin da Iyaa tace zata haɗa aurenmu ayi tuwona maina. Har hawaye Burodami Debisi yayi ma iyaa dan ta tausaya mishi ta janye maganar auren. Ba dan ƙiyayya ba sai dai kawai bana daga cikin jerin kalar matan da yake burin rayuwar aure dasu. Ni ina da ƙiba sosai, gani da cikar kumatu dan har idanuna da hancina sun shige ciki, ga mazaunai masha Allah. Shi kuma baya ra'ayin mace mai irin zubina. A cewarshi siriraya doguwar mace yake so, wacce zai iya bi da gudu ta zura ya rufa mata baya. Akan wannan dalilin ya kafe dole cikin fishi da hasala Iyaa ta janye batun aurenmu dole ta ɗauki idanu ta zuba mishi, har kwsnciya jinya ssida yayi. Bayan aurena da shekara biyu ya auri Yemisi ƴar ƙawar Iyaa. "Me yasa daya kawo baki bari na zo kin nuna mun ba?" Kai na sauke ƙasa ganin yanda fuskar Gwadabe ta sauya launi. Ka yi haƙuri in karɓar da nayi ya ɓata maka rai. Amman ba roƙa nayi ba, har gida ya kawo mun. Gwadabe ka rage ƙiyayyar da kake yi ma Burodami Debisi, dan shi ya ɗauki ɗawainiyar rayuwata tun daga yarintata har tasowata. A matsayin wa nake ganinshi, shima bani da wani matsayi a wajenshi daya wuce na ƙanwa" "Ki tsahirta mun haka nan Iyabo. Ai nasan wanki ne, sai dai ai wa ne irin wanda akwai aure a tsakani. Danni na kasa gane menene manufar Debisi sonki yake yi ko tausayinki" Zim naji jikina yayi, ba wannan bane karo na farko da Gwadabe yake ƙumaji sabida debisi ba, kuma ba fa zargina yake yi ba ni na ɗauka a matsayin yana tsare mutuncina da nashi ne baki ɗaya. Gwadabe..." Hannu ya ɗaga ya dakatar dani. Ya soma cin abincinshi zuchiyarshi cunkushe da kishin Debisi har ya gama tsakanin ni dashi babu wanda yayi ko tari, sai ja da sauke numfashi da muke yi. "Batun kuɗin asibiti kuma shima Debisinne ya biya ko, so kike ya samu hujjar ganin kamar bana ƙoƙari a kan ki ko? Bayan kinsan komai da irin tsanar da ake nuna mana. Kina fa gani ƴan uwana ma bana neman taimakonsu" Nasan idanun Gwadabe ya rufe da kishine, shi yasa nayi murmushi nace. Ashe na fika dauriya da haƙuri tunda har na iya haɗa ɗaki da matar da akeson a aura maka. Matar data baro gidan mijjinta sabida kai. Haba Gwadabe in hankali ya gushe hankali ake turawa ya nemo shi. Ko da Burodami ne ya biya kuɗin asibitina bai kamata ace an yi fishi dashi ba, ballema Burodami kokodeen ne ya biya komai da komai." Shiru yayi mun, yasha jinin jikinshi, dan maganata tamkar na ɗaureshi da jijiyoyin jikinshi ne. "Kiyi haƙuri da fishin dana nuna, kishinki ne yai mun yawa. Amman nasan har ga Allah kin fini dauriya da mayar da komai ba komai ba. Mala'ikun Allah ku shaida na sa ma rayuwar Iyabo albarka." Ajjiyar zuchiya na sauke tare da yin dariya. Shima dariyar yayi. "To leshi da kika ɗinka mana shi kuma ta ina kuɗin ya ɓullo?" Labarin yanda akayi na tara kuɗin na bashi tare da kayan kwancen da aka bani a gidan aiki. Miƙewa tsaye nayi na ɗebo mishi duk kayayyakin da na samu na suna, da duk kuɗaɗen da aka babbani. Ka gansu duk albarkar haihuwa ne, kasan ƴan biyu akwaisu da farin jini" Dani dashi mu kaita wauware kayayyakin muna kallo, muna hirarmu ta yaushe gamo, ina bashi labaran abubbuwan da suka faru shima yana bani labarin yanda suka kwashe da Babala kan batun sunan yara da ya saka. Da ankon leshi da muka yi, ashe Babala har kuka saida tayi, wai Gwadabe ya zama beyeraben dole. "Kaya sun yi kyau an gwangwajeki da kaya gaskiya, babu abinda zance sai Allah ya amfana. Sunan yazo mun da sauƙi wallahi ko da yake ance ko wanne yaro da arzikinshi yake tafe" Gaskiya ne kam. Allah ya ƙara rufa mana asirinmu fid duniya wal akira" Gwadabe yace. "Ameen dai Maman ƴan biyu. Toh yanzu me kike ganin ya dace kiyi da kuɗinnan tunda kinga suna da kauri, in yaso sai ki haƙura da zuwa gidan mutane aiki, dama ba asan raina kike zuwa ba, tunda na samu aiki ƙwaƙƙwara a hannuna kema ki miƙe ƙafarki ki huta kamar yadda ko wacce mace take hutawa ko?" Miƙewa nayi na tattare kwanukan daya gama cin abinci na fito falo dasu. Abun mamaki Laila na gani a laɓe tana sauraren hirarmu da Gwadabe. Tana ganin fitowata tayi kamar maiyar da aka kamata ƙiri_ƙiri tana lashe kurwar surukarta, har wayarta tana faɗuwa a ƙasa tsabaragen kaɗuwa. Tsaki nayi mai ƙarfi na harareta. A cikin bahun na zuba kayan wanke_wanken na rufe da bahun na yi komawata ciki. Gwadabe ya sake dawo da maganar sana'a tsabaragen ɓacin rai yasa ban iya ce mishi komai ba, na tuɓe kayan jikina na zura doguwar rigar baccina, nayi hayewata gado na juya bayana ina hawaye." Cikin ɓarin jiki Gwadabe ya hayo gadon yasa hannunshi a kafaɗata, yayi amfani da ƙarfi wajen juyo dani, hawayen da yaga yana tsiyaya ta gefen idanuna ne yasa ya kasa magana. Cikin rishin kuka nace. Yaushene Laila zata bar ɗakinnan Gwadabe ka sanar dani a darennan, wacce hanya ka sama mana ta yanda Laila zata bar gidannan? Ni da ɗakina Laila bata Isa ta hanani zaman lafiya ba, nagaji Gwadabe ni gidanmu zan tafi" Na ƙarashe zancen da rushewa da kuka mai gunji, ji nake yi zuchiyata na yi mun tuƙuƙi. Rungumeni Gwadabe yayi tsam a ƙirjinshi yana rarrashina, amman fur naƙi rarrasuwa. Ana cikin hakane muka jiyo wani ihu daga falo mai razanarwa, wanda yai sanadiyyar farkarmun da yara daga bacci suka saki kuka a tare. Kafin in ɗaukesu muka sake jiyo ihun a karo na biyu. Da sauri Gwadabe ya fita na mara mishi baya da ƴan biyu a hannuna. Me zamu gani hmm Laila muka gani a kwance tana burgima tsaraicinta na fitowa, sai ihu take kwarmayawa. Har ɗan diras ɗinta muna hangowa fari sol dashi, da sauri Gwadabe ya kawar da kanshi gefe. Kafin kace me matan gidan sun cika ɗakin, Laila na ganin haka saita soma kwaɓe suturarta tana fatali da'ita. Ba shiri Gwadabe ya fice a ɗakin. Sai adda'a aketa faman tofeta dashi ita kuma tana ta surutai. Mamanta na ƙurama idanu farare sol dasu luwai_luwai ko wacce mace nayi imani zata so dama itama mamanta haka yake. Kuma Gwadabe fa ya ga maman nata, dan sai da ta yar da rigar maman kafin ya fita har yana tuntuɓe hawayena na share dan nayi imani babu wata iskar dake damun Laila tsagwaron iskanci da makircin data riƙa a matsayin makamin da zai fitar dani daga ɗakina ita ta maye gurbina kenan. Ina tsaye a gefe na kasa daidai da motsawa jiri ne ke shirin zubar dani, da zanyi gigin ɗaga ƙafata tabbas da jiri ne zai kwasheni ya zubar a ƙasa tim. "Sannu Laila Allah ya baku haƙuri. Haula kawo ruwa a bata tasha, ƙilama wani agumun aka mata danta bar gidan a haukace, tunda mu a iyakar saninmu Laila bata da iska." Cewar Yaya Halima wacce take riƙe da kafaɗun Laila. Gude ta ɗauki zani a kujera ta suturta mata ƙirjinta dashi. Ni dai ina tsaye ina kallon bariki. Ruwa aka bata tasha, Babala tace ta kwanta ta rufe idanunta. Ta ko kwanta ta rufe idanta ruf. "Toh Allah shi kyauta, Allah yasa ba mayu bane ma suka kama mata kurwa ba, kunsan jiya an yi taron na ayya" Cewar Babala wacce take hanyar ficewa daga ɗakin. Ina tsaye duk suka watse suka barni, sai muryoyinsu nake jiyowa a ƙofar ɗakina. Rigar maman Laila na bi da idanu kawai na yi ƙuta tare da shigewa ɗaki na kwantar da ƴan biyu da suka koma baccinsu nima na kwanta ina share hawaye mai zafi. A
Chapter 20 · 0% Book details