Sashe 148
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zuchiyata sai naji tana wani irin fusga. Labarin da Baɗɗo take bani ya jijjigani tsoro ya sake shigata sosai, ni dai har muka isa inda zamu hau acaɓa ya fitar damu jere bonyo bance komai ba. A lokacin kawai na riga da nayi saranda na yarda Hama ta ruguzamun rayuwata. Muna isowa jere muka soma cin karo da matan ƙauyanmu masu nono. Nan ƴan gulmammakinmu na mata ya soma tashi, har a bayan akori kura wata ƙawar Hama saida ta kasa haƙuri ta tambayi Baɗɗo. "Baɗɗo hatsari yayarki tayi ne naga fuskarta a kumbure idonta ya tara jini baƙi ga bakinta a fashe?" Ɗagowa nayi na dubeta, na dawo da kallon nawa zuwa ga Baɗɗo. "Zamewa tayi a bayan gida shine taji mummunan rauni asibiti ma zamu je" "Asibiti a cikin ƙauyannan ana zuwa asibiti dama?" Ni dai takaina nake yi, dan ni a lokacin wallahi ji nake kamar kaina zai faɗo, ga wasu jijiyoyi da suka ɗaɗɗaure a kaina sai nake jina wani iri haka. banma dawo hayyacina ba har saida naji motarmu ta kawo kan iyaka mun iso Girei. Da ƙyar na sakko jiki duk ciwo, ko ina yayi tsami ga ciwon baya ya far mun. Mun jima a titi kafin muka samu bus ɗin da zata shiga gari. Wayata na zaro a jakata na kunna a lokacin rawar ɗari ma nake yi. Muna shigowa Adamawa kafin ma mu sauka na danna kiran wayar Uwani. Nako taki sa'a ringi biyu ta ɗauka. "Kaga Amarya ƴar gaban goshi, shalelen Hamma, yau an fito birni kenan?" Idanuna na lumshe hawaye suka zubo mun da ƙyar na ɗan saisaita nutsuwata nace. Uwani ki roƙi Hafizu dan Allah ya barki kizo. Wallahi ina cikin matsala, abubbuwa da yawa sun faru yanzu haka mun shigo garine Baɗɗo zata kaini asibiti, zaiyi wuya su sakeni in koma gida ma yau." Sai na fashe mata da kuka duk na tashi hankalin Uwani. "Shikenan Iyabo. Yanzu zan shiryo in tawo, zamu dinga waya har in iso. Kiyi haƙuri koma menene zanzo zamu samu mafita in sha Allah " Wayar na datse ina share hawayena wasu na zubowa. Ni hama zata sama wari a jiki, ta rabani da Hammana, to dama shi kishin haka yake, ko kuma a ƙauyen haka suke nasu kishin na azaba? Ya Allah ka ɗauke mun wannan lalurar warin da aka ɗauramun Allah ka bi mun kadina" Idanu na runtse zafin idon daya tara jini har tsaƙiyar kwanyata babu shiri na buɗe. Motarmu ta sauke mu a bakin tasha, acaɓa muka tare zuwa bakin asibiti. Muna bakin asibitin Uwani ta kirani motarsu ta baro kano. Mu kuma muka shiga ciki, Baɗɗo ta zauna mun a layi ni kuma na buɗe fayil na yanki kati. Akwai layi bana wasaba haka mukaita bi. Saida wata mace tazo wucewa ta ganmu a layi ta dubi idona tace. "Likitan idanu kuke son gani, dan naga idanunki suna ciwo sai ruwa kuma suke zubarwa?" Nace da'ita. E likitan ido nazo gani" "To ku biyoni, nan ba ɓangaren masu lalurar idanu bane. Kuzo muje" Haka duk uban layinnan da muka bi ya tashi a tutar babu. A baya mukaita binta har ɓangaren masu lalurar idanun. To mun kuma yi latti, da ƙyar wannan matar dai ta samu a layi dan taga idanun ya matsa mun. Mune har bayan azahar bamu shiga ɗakin ganin likita ba, sai wajajen uku saura aka kirayi sunana. Baddo na barma jakata da wayata na shiga ofishin likitan idon. Izinin zama ya bani, ya ɗago ya dubi idon da kyau kana yace. "Me ya sameki, dukanki akayine, ko me ga idon yanata zubar da ruwa?" Faɗuwa nayi a banɗaki shine na faɗi idona da bakina suka daki gini" Girgiza kai yayi yace. "Ashsha, Allah ya kiyaye gaba. Ga gado zo ki kwanta inason duba lafiyar idanun" Bayan na hau gadon sai yaga jikina na wani irin ɓari, ni kaina ɓarin da jikin nawa yake yi saiya tsoratani. Ba shiri ya taɓa jikina yayi wani irin mugun zafi, ni dai nasan inajin gadon dana kwanta yana juyi dani. Daga haka ban sake sanin abinda ke faruwa ba. Ban sake samun kaina ba sai farkawa nayi naga ledar ƙarin ruwa a hannuna. Baɗɗo na zaune a ƙasa, Uwani na zaune a kan gadon da nake sun ƙura mun idanu. "Ta farka Baɗɗo. maza jeki ki kirawo likita. Iyabo sannu yaya jikin?' Uwani har kin iso ashe?" Da faɗar haka saita soma share hawaye, murmushi nayi nace. Ki dena kuka, tawa jarabawar ta wannan auren kishiyace Uwani. Wai yau nice a gadon asibiti, namijin da nafi sonshi fiye da kowa shi ya dokeni, banda wari da matarshi ta saka mun. Jarabawar da girma Uwani. Amman akwai Allah " Shiru Uwani tayi ta kasa cemun uffan. Niko wani tawakkaline naji ya shigeni ainun, lammurana suna ga Allah. "Tun jiya muke asibitinnan Hamma baizo ba, matar tashi ma bata zo ba ko leƙe. Surukarki dai ta zo jiya sai wajajen magriba ma tabar asibitin. Dada kuma basu san halin da kike ciki ba,haka Baffa Musa, saidai Amaduyal ya sani. Kinga shi ya kawo mana abinci jiya, da safennanma shi ya kawo mana. Iyabo na tausaya miki. Amman wallahi kinsan Allah saina rama dukan da Hamma yayi miki a jikin figaggiyar matsiyaciyar matarshi?. Ƴar iska ke da zaki zage ki ci ubanshi ko da asiri da kin matseshi gobe bazai tunkaroki da duka ba. Jibi yadda ya nakasaki fa Iyabo . Taya zan tsaya wani ɗan ƙauye jahili yaimun irin wannan dukan, wallahi ko ya fi karfina da cizo, da yakushi saina kwaci kaina, in haɗa da hauka." Idanu na lumshe kafin in buɗe likita ya iso shi da Baɗɗo. "Sannu Jabu. Yaya yanayin jikin naki kike jinshi?" Ko ina ciwo yake yi mun. Kaina kuma yana matsanancin ciwo, ga wata jijiya da tai tsaye ta saman idon ciwo take yi mini" "Ki nane idonki mai lafiyar marar lafiyar ki barshi a buɗe" Umarninshi nabi, amman me koda na toshe idona mai lafiyar na bar marar lafiyar a buɗe dishi_dishi kawai nake gani" "Kina iya tantance kalar kayan jikina?" A'a gaskiya baƙi nake gani babu kala" Sai naji kuka na shirin kamani. "To to Shikenan sake hannunki, ki biyoni zamu je ɗakin gwaji, domin musan a wanne mataki ciwon yake. Karin ruwan dake hannuna ya cire mun" Uwanice ta taimakamun na sakko akan gado. "Baddo ki zauna ki jiramu, zan rakata" Cewar Uwani kenan. Tare da'ita muka shiga cikin ɗakin gwajin. Abubuwa mataki_mataki akaita bi. Har Abcd aka nuna mun a allo akace in karanta, in ban iya karatunba in ina ganinsu da kyau in sanar. Aka sakamun tabarau a idona, asa wannan a cire wannan, harda tocila saida aka haskamun idona likita sai tambayoyi kawai yake yi mun ina bashi amsa. "To Shikenan zaku iya komawa. Ƙila zamu sallameta zuwa anjima ko kuma gobe da safe" Jijjunanmu a mace murus muka dawo ɗakin jinyar. Muka tarar da Yafendo ta zo." "Jabu sannu da jiki" Yauwa Yafendo sannu da zuwa, ai da kin yi zamanki" Na zauna akan gadon kaina a ƙasa. "Ban isa in zauna ba, wallahi jiya ko baccin kirki ya kasa zuwarmun." Uwani tace. "Haura ki kwanta Iyabo sabida yanayin jiki" Sai data taimaka mun na kwanta, suka gaisa da Yafendo, ta tambayesu yanayin jikin. "To kusan dai zamu ce ido kam ya samu matsala, dan inuwa take gani dashi. Yanzu haka daga ɗakin gwaji muke. Sai dai muce Allah ya bata lafiya ya bata haƙuri dan matsalar idanu tana daga cikin manyan matsaloli kusan zamu iya kiranta mutuwar tsaye. Sannan fa Yafendo har yau Hamma ko matarshi babu wanda ya leƙo asibitinnan. Ni cewa nayi sun san Iyabo bata da lafiya kuwa?" Salati Yafendo ta saki tana tafa hannaye. "Uwani kina nufin Hamma baizo ya duba jikin Jabu ba?" Uwani tayi ƴar dariya tace. "Baizo ba wallahi, kinga dai tun jiya nake asibitinnan" Shiru Yafendo tayi ta kasa cewa komai harna tsawon muntuna masu dama. Har wata ma'aikaciyar jinya tazo ta mayar mun da ƙarin ruwa, aka diga mun magani a idona. Har zuwa lokacin Yafendo bata ce komai ba." "Jabu, cuta ce an riga an cutar dake tunda kome za'ayi a matsayin ɗaukar fansa ba zai goge wannan lulurar data sameki ba. Amman ki sani wannan yaron bashi da laifi yi mishi akayi. Ita kuma Hama zan ɗauki mummunan mataki a kanta matakin da hatta iyayenta bazai musu daɗi ba. Dan Allah kiyi haƙuri kuma a rufe wannan sirrin bana so Daso, da Baffa Musa, da su A'i suji. Mu haƙa daku mu burne. Shi kanshi Hamman a hakan zaiga fishina da ɓacin raina. Ina zuwa zanje wajen aikinsu in sameshi" Nayi juyin duniya Yafendo ta bari karta je wajen aikin su Yaya Hamma, ko saurarena batai ba ta fice a cikin fishi tea Uwani ta haɗamun. "Tashi ki sa wani abun a cikinki. Ai gara ki bari taje ɗin. Duk da ana zargin farraƙu akayi musu, baya nufin za'a zuba ido. Narantse da Allah idona idon Hama saina sabautata na nakasa wani shashe na jikinta in da daɗi sai taji" Baɗɗo tace. "Koni ɗazu dana koma gida da safe saida mukai rikici sosai da'ita. Yuguda ne ya jayeni zuwa ɗaki naso in daketa ne, amman ban samu dama ba. Na barota a gidan ita da Daso tsohuwar munafuka, ita take kaita wajen bokaye tun kina Makka lokacin" Ni dai ina zaune ina shan shayi, duk wacce tayi magana in kalleta. Sun ɗauka da zafi. Ni inata gwada musu abi komai a hankali abinda haƙuri bai bayar ba, tashin hankali bai isa ya bayar ba. Ina gama shan tean Uwani ta zubo mun jallof ɗin shinkafa mai bushasshen kifi. Loma biyu kawai na iya turawa na danne da ruwa. Ruwan hannuna na ƙarewa aka ciremun saina fita nayi alwala ina daga zaune a dadduma na soma rama sallolin da ake bina. Ban idar da sallar ba saiga Yaya Hamma Yafendo ta tasoshi gaba sunzo. Suka gaisa da Uwani ba yadda suka sababa, dan a daƙile yake magana, kuma ya cusa hancinshi a cikin rawanin daya naɗe kanshi dashi. Uwani kuwa sai harara take zabga mishi tana mai kallon wulaƙanci. Ina sallamewa na ɗago na dubeshi, sai naga ya sake mun kyau. Shima idonshi yana kaina bai