← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 226 OF 237

Sashe 226

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dan Allah kar ki sake biye mata dan in Hajiya Sa'a ce zata kuma" Kai Uwani ta gyaɗa a zuchiyarta tace. "Ai ni nafi son ta kuma in koya mata hankali tukunna in yaso daga baya a sasanta. A fili kuma ta ja ajjiyar zuchiya tace "Babu komai Hajiya Mansa komai ya wuce na gode da shawara" Sallama Hajiya Mansa tayi ma Uwani ta fita. Ita dai Uwani har washegari bata fito tsakar gidan ba da daddare Alhaji Sama'ila ya shigo ɓarayinta yayi mata faɗa sosai a ranar taga ɓacin ranshi. Amman da safe da ya shigo su gaisa sai ya sake kamar ma ba shi ba. Cikin soyayya suka yi sallama. Da rana Laure ta shigo da sallamarta ta tsugunna a gaban uwani. "Hajiya kice fa zaki yi girkin rana. Hajiya Sa'a bata dawo ba tun fitarta. Hajiya Mansa kuma ta fita girki shine tace in sanar miki kar yaran makaranta su dawo ba'a gama abinci ba" Murmusawa Uwani tayi tace. "To Shikenan Laure ki soma fere mun doya bara in ƙarashe goge _goge zan gangaro, ki jiƙa mun bushasshen kifi da ruwan zafi da gishiri" Laure ta amsa mata da. "To Hajiya " Ta wuce. Uwani ta ƙalƙale ɗakinta ta bunka mix V.I.P turaren wutanta na Mrs Bukhari ko ina ya ɗauki ƙamshi kafin ta sakko ta samu Laure a kitchen suka yi faten doya da wake da bushasshen kifi. Ta sallami kowa aka ba direba na Alhaji Sama'ila ya kai mishi kasuwa. Da yamma Alhaji Sama'ila ya kirata yace me zata girka ne? "Abincin larabawa na musamman" Dariya yayi yace. "To Shikenan yau zan cika tumbina da kyau ashe" Su ka taɓa hirarsu dai kafin daga bisani suka yi sallama. A ranar Uwani ta zage ta dafa mackuba rice ta larabawa kaji ƴan shila guda uku ta zuba, ko wacce kaza gida biyu kawai aka rabata. Sai kazar Alhaji Sama'ila guda ta ɗaura mishi a saman shinkafar. Ta yi jus na bushasshen inabi da dabino mai ɗan karen daɗi. Zuwa takwas da rabi Alhaji Sama'ila ya shiga ɓarayin Uwani wani sanyin ƙamshi falon yake yi cakuɗe da ƙamshin wannan shinkafa. Idanu ya lumshe ganin uwani yasa gajiyarshi ta soma raguwa. A gurguje ya watso ruwa yazo daining ya tadda uwani ta zuba mishi abinci. Yana ci yana santin wannan shinkafa. Suka jiyo ƙwanƙwasa ƙofa. Uwani ce ta taje ta buɗe ƙofar. Hajiya Sa'a ta gani a tsaye tare da wani dattijo. "Ki mana magana da Alhaji" Ta faɗa rai a haɗe. Murmushi Uwani tayi mata ta dubi wannan dattijo da batasan ko waye ɗinta ba ta gaisheshi kana ta rufe ƙofarta. Ƙarasawa tayi ta zauna bata ce mishi komai ba har sai da ya gama cin abincinshi kafin ta bashi saƙon. "Yanzu kaje ka dawo ina jiranka zanyi ma tausa, gashi nayi maka babban tanadi" Murmushi yayi mata yace. "Bazan jima ba zaki ganni, ke dai ki zauna da shirinki" Fuskarta ya shafa tare da zura malum_malum ɗinshi ya fice. Bayanshi tabi da wata muguwar dariya tace. "Yau Hajiya Sa'a Uwani ta balbalin zata nuna miki ta fiki masifa da bala'i wallahi. Ni da ke shege ka fasa dan uban Mutum. To a wannan dare dai an sha gagarumin rikici a tsakanin Hajiya Sa'a da Tabalbalin Alhaji Sama'ila kuwa yana tsakiya. Duk bala'in Hajiya Sa'a sai taga Uwani ta damata ta shanye. Hajiya Mansa itace ta raba wannan taƙaddamar. "Alhaji tunda dai Hajiya Uwani itace tayi girkin rana dana dare, kuma ka riga da har ka shiga ɗakinta kafin ita Hajiya Sa'a ta dawo. Ni ina ganin ka kwana a ɗakin Hajiya Uwani Allah bashi gobe sai ka koma can din faƙat." Harara Hajiya Sa'a ta sakarma Hajiya Mansa itakuwa a zuchiyarta tana farin ciki sosai da zuwan Uwani wannan gida ko babu komai dole kowa ya kame kanshi danta lura uwani a tsaye take ya maman maza" Gaga gaga haka rayuwar gidan Alhaji Sama'ila ta ci gaba da wakana, Uwani dai sai da ta koya ma Hajiya Sa'a hankali aka hau sama aka rikito aka juya gidan sama a ƙasa , har zaneta sai da Uwani tayi kafin komai ya sassauto suka soma shiri da juna sosai. Ita kuma mai girma uwargida dama tana gefe bata shiga sabgar kowa, ƴar kasuwace kullum tana hanyar Dubai, Uwani kuma na hanyar Saudiya sari. Dukiya sai sake haɓɓaka yake ta yi, wayon da Uwani tayi shine a cikin ribar kuɗin Iyabo da ake juya mata ita da Burodami Debisi sai suke sai mata ƴan ƙananun gidaje haka ana zuba haya ana sake dulmiya kuɗin a kasuwanci. Uwani tayi ƙoƙari dan har aike take yima su Toye a madadin Iyabo, kuma bata rabu da zuwa duba Dada a jaɓɓi lamba ba. Takan baro ƙauyen cikin damuwa da kewar aminiyar arzikinta. Gashi har zuwa lokacin babu labari su Hamma, wanda zai kawo labarin nasu ma babu shi. Wannan kenan" Gaga_gaga haka dai rayuwa taci gaba da wakana. Hafizu yana kawo ma uwani su Ummu Kulsum duk ƙarshen wata su wuni da daddare ya je ya ɗakkosu Alhaji Sama'ila ya ɗauki kuɗi ya bashi yana yaƙe baki yana dariya zai karɓi kudinnan. Uwani kullum a zuchiyarta tana faɗin Allah wadaran naka ya lalace. Rannan kuwa Hafizu ya kawo yara yayi katari Uwani zuchiyarta a sama take. Da Hafizu da yaran duk tace kar su zauna mata a falo. "Wai meye ne nifa Hafizu ka zame mun ƙarfen ƙafa kai da yaranka duka. Na gaji da zuwanku, ina baƙin cikin zuwan da kake yi mun. Dan haka ga hanya ka fice mun, suma su bika. Ke Ummu Kulsum zaki iya gane gidannan ko?" Yarinyar tayi saurin ɗaga kanta haramar e. "To ki dinga riƙo hannun ƙannenki kuna zuwa ku bazan hanaku ba. Amman wallahi hsfizu duk randa na kuma ganinka a gidannan zan sakar maka kare su yo mub farautarka Dariya Hafizu yayi yace. "Haba Uwani me yayi zafi naga duk mun zama ɗaya ni dama in talauci ya doke nine sai in riƙo yaran muzo. Ki daure kar ki yi mun..... Wani kallo da tayi mishi ne yasa yaja bakinshi yayi shiru, ta ja yaran suka nufi hanyar fita. Juyowa yayi yace. "Uwani ko abinci bamu ci ba tun jiya, yarannan an korosu a makaranta, bamu da kudin motar zuwa gida ma. Ki taimaka ko ɗari biyu ce ki bamu" Nera ɗari biyar ta danƙama ƴar tace. "Maza ku je." Haka suka fice. Dole Hafizu ya dena zuwa gidan uwani sai dai yaran. Ashe ya zage ya samu mijin Uwani a kasuwa ya mishi bayanin halin da suke ciki ya bashi buhun shinkafa ya kuma ɗauke nauyin karatun yaran uwani har jami'a. Ai ranar da su Ummu Kulsum suka zo suns ba uwani labari. Har tashar su Hafizu taje tayi mishi biji_biji ta koma gida. Kunji wata jar jaraba fa a wajen Hafizu. Shi bashi da zuchiya dai. Nima nace Allah wadaran naka ya lalace.
Chapter 226 · 0% Book details