← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 236 OF 237

Sashe 236

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

"Am ina ganin kuka duk ba naku bane face ku nuna godiyarku ga Allah. Ku zo ku zazzauna muyi abinda ya taramu a sallami kowa.
Cewar Anty Sumayya kenan. Hannuna Baɗɗo ta kama ta zaunar dani a ƙasa gefen ƙafar Yafendo A'i kaina a ƙasa falon ya ɗauki shiru. Alhaji Usman ne yayi gyaran murya ya soma jawabi a hankali kuma a sanyaye tun daga haɗuwarmu har zuwa yau ɗinnan. Yana gamawa falon ya ɗauki salati da tafa hannaye. Idanuna na ɗago na dubi Yaya Hamma idanunshi sun koma jawur farin cikinshi ya koma baƙin ciki jikinshi har rawa yake yi ƙirjinshi yana ta hawa da sauka, hawayene naga suna bin kumatunshi kawai, kunsan fa Yaya Hamma akwaishi da kishi. Idanuna na lumshe kawai wasu hawaye masu zafi suka zubo mun.
Alhaji Usman yace.
"Hassan Husaini wannan shine mahaifinku, waÉ—annan dangin mahaifiyarku ne. Kuje ga mahaifinku yasa muku albarka"
A sanyaye yaran suka isa ga Hamma yayi musu wata iriyar runguma kukan kishin da yake dannewa ya saki kawai. Niko tsabar hawaye ko gani bana yi ma.
Yaran sun daɗe sosai a jikin Hamma kafin alƙali yace yaran su ɗanje daga waje tukunna, a samu a yi abinda ya dace.
Alƙali yace.
"Wanan shine mijin ita wannan baiwar Allah?"
Yaya Hamma ya É—ago kanshi yace.
"E nine ranka shi daÉ—e"
"Ko zamu iya jin labari daga naku ɓangaren dangane da ɓatan ita Iyabo?"
Uwani ce tayi gyaran murya ta basu labarin komai. Falonnan ya ɗauki shiru, can alƙalin yace.
"Tsawon tafiyarka shin Iyabo ita ke ciyar da kanta, ko kuma kai kake ciyar da'ita, duba da yadda ka daÉ—e a wajen kiwo, duk da wannan daÉ—aÉ—É—iyar al'adace da akasan fulani da'ita tun zamanin baya."
"Ranka shi daɗe mahaifiyata na kula dasu, sannan ƙannena maza na kulawa dasu su suke ajjiye hatsi, ɗan kuɗin cefanene suke nema da kansu"
"To Alhamdulillah naji bayaninka Alhaji Usman, suma ɓangaren Hamma naji nasu bayanin. Da kai da Iyabo, da Hajja Mama baku da laifi ko kaɗan ita Iyabo hankalinta aka gusar mata rayuwarta ta baya ta mance. Ita Hajja Mama bata san bayan Iyabo ba, kai baka san tana da aure ba wannan abun an yishi ne a bisa rashin sani, baku da laifi har a wajen Allah.
Ina fata bayan bayyanar wannan lamarin babu wata mu'amular auratayya data shiga tsakanin ku?"
Alhaji Usman ya ja ajjiyar zuchiya ya sauke kana yace.
"Babu ranka shi daÉ—e"
"To Alhamdulillah. A zahirin gaskiya dawowar iyabo hayyacinta shi yake nufin aurenku babu shi ya ƙare ya zama tarihi, har gobe tana a matsayin matar Hamma tunda yana da ranshi gashi a gabanmu, babu makawa aurenku da kanshi ya warware kanshi ba'a buƙatar sai ka rubuta takadda. Sai dai ku ɗauki dangana kawai. Ƴaƴa da kuka haifa yarane na sunnah tunda ta hanyar aure aka samesu kuma suna da gado kamar sauran yara.
Tare dukkanmu ukun muka ɗago muna kallon alƙali illahirin jikina rawa yake yi, Alhaji Usman yace.
"Allah shi gafarta ina bayani akan za'a iya bata zaɓi ta zaɓi da wanda zata yi rayuwa? Naji kace aurena dake kanta ya mutu"
A raunace yayi maganar, alƙali ya gyara zamanshi yace.
"Ba irin wannan case ɗin bane yake ɗauke da irin wannan hukuncin ba Alhaji Usman. Ita wannan baiwar Allah hankalinta ne ya gushe ta baro bayanta, ta manta komanta, kai kuma ka aureta, sabida haka bata da zaɓi dole aurenta na farko yananan daram. Shi wancan da kake maganar zaɓi shine in shi mijinne ya tafi ya barta shekara da shekaru babu waiwaye babu aike, babu ciyarwa har an cire rai da dawowarshi to sai taje kotu alƙali ya saketa tayi wani auren, to bayan tayi wani auren in shi wannan mijin ya dawo shine alƙali zai bata zaɓin zaɓar ɗaya a cikin mazajen nata. Kaga kuwa ai naku case ɗin ba haka bane, da fatan kun gamsu?"
Idanuna na runtse ina ambaton Allah. Alhaji Usman ma inaji yana ambaton Allah a fili, ya kasa mallakar kanshi"
"Yanzu abu na ƙarshe shine Iyabo zata yi idda na wata uku, ko kuma ince jini uku dan wata mace a wata biyu take yin jini ukunta. In kuma ta wuce yin jinin al'ada sai ta ƙirga wata uku. Da zaran wannan lokaci ya cika Iyabo zata koma ɗakin Hamma a matsayin Matarshi suci gaba da zama, ba sake ɗaurin aure, ba sabon sadaki, ba akwati. Wannan shine hukuncin. Da fatan zaku bi yadda yazo a musulunci kar abi son zuchiya duk da akwai malaman da suke ba da fatawar macen na da damar zaɓan da wanda zata zauna a hakanma. Zance mafi inganci shine dole ta koma hannun mijinta na farko.wannan shine ƙarshen maganata."
A hankali sautin kukana ya dinga shiga kunnuwan jama'ar cikin falon hankalina ya tashi sosai da sosai. Bayan an barni nayi kuka ishasshe sai Usman yace.
"Ina neman alfarma ɗaya a wajen Iyabo da Hamma. Hassan da Hussaini sun riga sun zame mun jinin jikina so nake a barsu a hannuna ko baku barmin su halak malak ba a barsu su ƙarƙare digree da mastas ɗinsu dan Allah ni wannan alfarmar nake nema musu a dubeni. Nasan Hamma shima zai so a yanzu ya tattare kan iyalinshi waje guda, ku dubeni kuimun adalci dukan zai yi mun yawa zai yi mun yawa Hamma"
Anty Sumayya sai ta fashe da kuka.
"Nima damuwata yaranne wallahi Allah, mun yi shaƙuwa dasu sosai ya zamu yi Hamma ka tausaya"
Gyaran murya Hamma yayi nayi saurin É—agowa na dubeshi, ashe Usman yana ankare dani, ina sake É—agawa muka haÉ—a idanu
Ba shiri nayi ƙasa da kan nawa.
"Alhaji Usman zan soma maka da godiya. Wallahi Allah da ace ina da ikon bar maka Iyabo da na bar maka ita. Balle su Hassan, haƙiƙa ka fini son su, ka fini shaƙuwa dasu, sabida haka na barsu a hannunka su yi zamansu tare da ku. Sai dai in da hali kuma ku bamu daya a cikin yaran ita iyabon gudun kar kaɗaici yayi mata yawa. Mun gode ƙwarai Ubangiji Allah ya saka maka da mafificin alkhairi wannan hidima da kayi da iyalina har gaba da abada bazan mance ba. Malam kaima mun gode sosai da kasancewarka tare damu Allah ya saka da Alkhairi "
Wawuyar ajjiyar zuchiya na sauke da naji Alhaji Usman yace.
"Ta ɗauki Rumaisa'u autarta tunda nayi muku bayanin mun juya mahaifarta sakamakon ciwon bayan data kwaso a saudiyya sai kai mun afuwa bansan cewar haka bane abun da duk abinda ya faru bazai faru ba. Inma su matan take so harda Nana ta ɗauka wallahi bazan hanata ba, sai dai da sun kammala sakandare zasu zo su sameni a India zasu jona digree ɗinsu suma likitocin nake so su zama. Nagode sosai Iyabo da irin zaman da kika yi damu Allah yayi miki albarka. Kai kuma kaji tsoron Allah ka dubi Iyabo kai mata riƙon da zata yi alfahari da dawowarta cikin hayyacinta"
Akwai motarki a harabar gidannan in zaku tafi to ki tafi da abunki. Wannan gidan da kike ciki na mallaka miki. Sannan ga wannan babu dai yawa million biyar ce ko sana'a sai kiyi dasu. Yaran zansa a shiryasu ku tafi Anty Sumayya zata biku taga wajen."
Yana gama fadar haka ya zaro takaddun gidan yasa hannu, nima nasa, Burodami Debisi da uwani suma suka saka, sai alƙali ma ya saka. Ya rubuta mun check ya bani.
Usman ya saka kai ya fice a falon ko waige bai ba. Ji nayi kamar in bishi, dan har na so tashi kaifin idanun Hamma ne yasa dole na zauna kaina a ƙasa ina kukan zuchi.
Ƴan uwa anata murna falo ya gauraye da jin dadi da farin ciki, sai waye waye suke yi.
A wannan zama ne naji abun alkhairi da uwani ƙawa ta gari ta yi mini dukiya ta habaƙa ta girma.
Yau ni Iyabo na zama nurse gani da gidaje, gwala-gwalai, ga mota, ga Hamma ya dawo mun, ga Dadana tana da rai gani cikin dangi tsamo_tsamo amman wallahi Allah bani da nutsuwa kunji fa wata ƙaddara tausayin Usman ya hanani samun lafiya da tsantsar son shi. Bazan ɓoye muku ba inason Usman so mai yawa, shekara goma sha bakwai bafa wasa bane. Kuma a wannan shekarun rayuwarmu muka gudanar cikin aminci, wayewa, da sanin darajar juna madallah da salihi kuma nutsattse Usman.
A wannan rana bamu samu ganawa da Yaya Hamma ba, ina dai cikin ƴan uwa anata bani labarin rashe_rashe da ƙaruwar da aka sassamu.
Iyaa Debisi ta rasu shekara uku kenan ashe babu rabon zama gana. Iyaa Kokodeen kuma tana raye babu dai yadda take, su Bose da su Burodami Debisi sun manyanta sosai ga iyali sun tara masha Allah.
Yaya Hamma ya samu ganawa da yaranshi sai farin ciki yake yi. Yaran dai basa wani farin ciki duk sun shiga damuwar zan tafi in barsu su kaɗai. Ni dai haƙuri na basu na zaunar da yaran duka naita musu nasiha, su manyan nai musu bayanin da zasu iya fahimta dai. Suka shiga dangina suka sake.
Washegari muka ɗau azamar tafiya Kano kafin mu wuce Jaɓɓi lamba.
Ni a motata muka zauna Burodami Debisi ne zai tuƙa.
Da yaran dukka muka tafi Anty Sumayya zata dawo da Alhaji karami.
"To Iyabo Allah ya ƙaddara saduwarmu ku gaishe da ragowar dangi, nima zanzo in sha Allah"
Cewar Alhaji Usman. In yi magana na kasa wallahi, in yi sallama da matanshi da matan ƙannenshi ni dai na kasa haka muka kama hanya.
Gaga_gaga sai gamu a kano can gida.
Naga soyayya muraratan ƴan uwa da maƙota duk sun taru. Wata ƙudurar Allah a nan muka haɗu da Gwadabe da su Toye suma sun zo harda Bara'u a shirgegiyar motarsu Gwadabe ya haɗa ƙiba da katon ciki, girma ya saukar mishi sosai.
Yara sun girma masha Allah Allah al hakeem yau Gwadabe ne zaune a cakuÉ—e da Æ´an gidanmu a É—akin iyaa Debisi rayuwa kenan komai mai wucewa ne.
Nan ma Gwadabe suka tafi suka bar mun yara.
Suna fita ƙofar gida Gwadabe ya dubi Bara'u yace.
"Hmm Iyabo ce yau ta zama nurse harda rayuwar aure a India. Bara'u na taya iyabo murnar dawowarta hayyacinta ta wani ɓangaren na taya ta takaicin baro india da tayi. Nifa Hamman nan nata Allah cikin amincewarshi naƙi jininshi"
Bara'u ya dafa Gwadabe yace.
"Kamar yadda har abada Hadiza ba zata ƙaunaci Iyabo ba. Allah ya shiryeka shaƙiyi"
Kwananmu biyu a Kano muka yi Adamawa gabaki É—ayanmu.
Allah mai iko Dada ta tsufa ta yamushe, amman da kafarta take tafiya muryarta raÉ—au.
Kuka kawai ta dinga yi na murna.
Dangi akaita tururuwar zuwa kallona, maƙota ɗalibaina, Chubu dake aure a birni, Daso ne da duk ta lalace ta tsofe duk kowa yazo baƙi sun ƙi ƙarewa sun ƙi barinmu mu keɓe.
Kwanan Anty Sumayya da Hajja Mama biyu a jaɓɓi lamba suka tafi tare. Alhaji Ƙarami yanata kukan shi zai zauna da Nana. Haka dai sukai mana sallama suka tafi ƴan biyu kuma mun roƙi ba yanzu zasu koma ba tunda lokacin ne ma ake zuwa yi mana barka.
Ɗakina nasa Baɗɗo ta kaini na shiga komai yananan daram a ɗakin babu ko datti. Saboda a nan Hamma yake sauka in ya shigo Jaɓɓi lamba.
Tsugunnawa nayi naci kuka iyakar iyawata.
"Uwani kin tuno sanda aka kawonu ina Amarya idonmu idon azara?"
Dariya muka tuntsure dashi. Uwani tace
"Ni danna kan hama a ruwan wanke_wanke shi yafi komai tsaiwa a raina ƙawata. Baɗɗo tace.
"Hmmm ai Hama ko a haka ta ga aya. Dan har yanzu batai aure ba tana gidan yarta sai tallar nono rayuwarta abun tausayi.
Ajjiyar zuchiya na sauke.
Nasan dayawa a cikin makaranta burinsu ganin Hama ƙila ta haukace ko ace tayi haɗari tayi raga raga ko? Kamar yadda yake faruwa a ƙagaggun labarai, ko ace muna haɗa idanu ta fita a guje tana hauka ko?
Wannan ba haka bane labarine na gaskiya wata shariar sai a lahira, wani sakamakon sai an je gaban mai kowa zai cire maka hakkinka, ni ko a iya kasa auruwa da tayi raina yayi fari abadan babu yafiya a tsakaninmu, ni bamma sake sakata a idanuna ba.
Amman naji labarin wulaƙantacciyar rayuwar da take yi a gidan yarda da irin yadda aka washeta a ƙauyen ta zama tamkar mujiya.
MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
NAMA YA DAHU....
ROMO ƊAÑYE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA HUÆŠU
20
ƘARSHE
Chapter 236 · 0% Book details