Sashe 194
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
IYABO:. Da guduna na nufi Cubu na ɗagata tsaye ba sai jini ya yanke mata ba. Kishiyoyinta dukka suka ruɗe. Baku da imani amman yarinyarnan kasheta ku ka yi niyyar yi, ku ko ganin girmanku bakwa yi ne? Sannu Cubu muje daga inuwa" Najata na kaita baranda jini dai bai tsaya ba a haka mijin nata ya shigo ya samemu numfashinta ma lokacin ya bar gangar jikinta, kishiyoyin duk sun tsure. Shikenan ta mutu kun kasheta kun huta kishi ya ƙare bar maku gadin duniyar" Carab mijin Cubu yace. "Wani abun suka yi mata ne ni ban sani ba?" Shigowa nayi na samesu sun zauneta suna son su kasheta ita da abinda ke cikinta dan rashin imani" Ni da mijin Cubu muka kinkimeta muka yi waje da,ita a haka a sume aka hau mashin da ita har zuwa Girai ba shiri aka bata gado duk mun ruɗe muna cikin tashin hankali ni kam hawaye kawai nake yi. "Waye mijin yarinyarnan da aka shiga da'ita ɗakin haihuwane?" Yayi zuruf ya miƙe. "Ganinan?" Likitan ya ƙare mishi kallo dattijone fa babba, ita kuma Cubu irin fulaninnanne sirara kamar Yaya Hamma ga karancin shekaru." "Shin ka taɓa barinta taje awon ciki kuwa?" Da tsoro sosai a fuskarshi yace. "A gidana ba'a zuwa asibiti kwata_kwata itama dan kishiyoyi sun so halakata ne shi yasa na amince muka tawo" Ajjiyar zuchiya ya sauke likitan in da sabo ai ya saba da ganin fulani da ɗabi'unsu iri iri. "Hannu zaka saka mana yanzu anan. Baiwar Allah kamar ke zaki fi fahimtata tiyata za'ayi mata domin a samu a ceto ran ɗaya kar a rasasu duka" Mijin Cubu dai yaƙi saka hannu sai ni nasa hannu aka shiga da'ita ɗakin tiyata. Sauƙin da aka samu ya biya kuɗin duk abinda ake buƙata. "Ni zanje in sanar a gida, sannan a turo wacce zata taimaka miki wajen kula da'ita. Sannan zansa yara su kawo kayan jaririn" Da kwaɓaɓɓiyar hausarshi yayi magana kafin ya tafi ni kuma na samu waje na zauna sai tubka da warwara nake yi. Wannan rayuwa ni ta isheni wallahi komai ya fice mun a kaina, ni rayuwarma banƙi ace ta tsaya ba aima kowa hisabi ya kama gabanshi. Wai me mata suke son zama ne a rayuwarnan akan kishine?" Idanuna na lumshe wasu hawaye suka zubo a kumatuna. A haka babban yaron mijin Cubu ya kawo kayan jarirai cikin ghana most go, ya bani kuɗi nera dubu uku yace in riƙe ko za'a buƙaci wani abun. Yana tafiya na miƙama ma'aikatan jinyar kayan suka shiga dashi, ni ko dubawa banba. Cikin awa uku akaima Cubu tiyata likitan ya fito. "Alhamdulillah mun samu nasarar ciro abinda ke cikin nata yana cikin ƙoshin lafiya Namiji ne. Ita uwar itama tana cikin ƙoshin lafiya, sai dai muna da buƙatar jini leda biyu da za'a ƙara mata" Hamdala nayi na godema Allah, na sake godema Allah. "Likita a ɗebi jinina in zaiyi a saka mata" Jim yayi yana nazari kamar bazai yarda ba dai sai kuma ya amince. Muka je aka ɗebi jinina akayi gwaje_gwajen daya dace da aka tabbatar da lafiyarshi sai suka ɗibi leda biyu. Amman nafi awa ɗaya a kwance ina hutawa kafin na tashi na goya biyu na fito. "Yafendo na gani, da matar Babansu Baɗɗo a zaune a benci" "Yafendo kun iso kenan?" Yafendo ta miƙe tace. "Nuna mana ɗakin da Cubun take, munfi minti talatin da zuwa ai munata zaune" Kafin in basu amsa sai ga ma'aikata jaye da Cubu a gadon marasa lafiya zuwa ɗakin hutawa. Dasu muka ɗunguma muka shiga, jarirai wasu na kuka, wasu na bacci, wasu suna kwance shiru. Jaririn Cubu ma yana kwance sai bacci yake yi kanshi duk suma. Likitane akan Cubu yana ɗaura mata ledar jini. Matar Babansu sai wani hararata take yi tana wani fiffiƙa, komai itace akan gaba sai zaƙewa. Daga can gidan Babannasu aka kawo mana tuwo. Dada ma ta aiko mana da shinkafa da miyar da nayi mata. Nan matar Baban ta kasa haƙuri saida ta riƙe bakinta. Haka dai muka wuni cur sai zuwa dubiyar Cubu akeyi. Da magriba sai ga Baɗɗo, Yusufu, da Daso sun shigo. Daso harda filas ɗinta na ruwan zafi cike da shayi mai madarar luna. Naso in kwana a asibitin Yafendo ce taƙi yarda haka nabi su Baɗɗo muka koma gida. Nan sintiri ya auremu kullum muna tafe dai har aka sallamota . Kishiyoyinta kuwa babu wacce tazo dan tsoron abinda suka aikata. Mu sai daga baya ma muke jin labarin ya korasu gida bisa laifin da suka aikata. Allah cikin ikonshi sai mijin yace a wuce da'ita gidan Dada. Munyi farin ciki sosai amman wallahi ko kwana guda batai ba mai nagge yazo da kanshi ba aike ba ya tusata a gaba . Muna ji muna gani gidan suka je suna ni kam banje ba an dai kawo mun abinci da naman suna dai. Banma sake sa Cubu a idanuna ba har saida sukai arba'in suka zo mana yawon arba'in ɗin. Yaronta yayi ɓukeke dashi sosai gata ƴar firit da'ita sabida fargaban tsotso duk saita sake suɗewa" "Kin rame sosai ko bakya samun abinci kina ci ne Cubu" "A'a Adda inaci, kawai zaman gidanne ya isheni so nake in koma. Mugunta suke yi mun, kuma ko Baban yaronnan ya kawo mun abun daɗi dasu da yaran gidan suke cinyewa. Kuma Baffa ko batun komawata bayayi. Shima Baban yaron inna tambayeshi yaushe zan koma, baya iya bani amsa sai inga ranshi ma ya ɓaci Adda" Kai na gyaɗa nace To ko dai wani abunne, ko kuma wata kitimirmurar kishiyoyinki suka ƙulla miki. Amman kina yin addu'o,in da nasa kika haddace?" "Inayi sosai Adda, kuma ina yawan ambaton la'ilaha, illah, anta, subuhaka kuntu minal zalumin, sai in ƙara da hasbiyallahu, la'ila,illah anta, alaihi,tawakkaltu,wahuwa rabbularshirazeem." Yauwa da kyau ki riƙe kiy ta nanatawa Allah zai kareki daga sharrin masu sharri. Zanci gaba da yin makaranta amman a gidan Dada zan dinga yi da daddare, kafin ki tafi saiki dinga zuwa. In kin koma ma in mijinki zai barki ki dinga zuwa sai ki dinga leƙowa ai" Haka muka wuni muna hirarmu, da yamma sai ga Khari ta leƙo, kafin ma ta zauna sai Baɗɗo itama ta shigo. Nan muka buɗe sabuwar hirarmu ta zumunci. Harga Allah ina jin farin ciki sosai inna ganni a cikin dangin Dada, ina matuƙar son Dadane. Gaga_gaga muka komar da karatunmu zuwa gidan Dada. Inna gama dasu Baɗɗo da Amaduyal sai in koma wajen Dada itama in mata ƙari a Qur'ani. Nayi iyakar yina dan ganin na koya ma Dada baƙi amman dai ta kasa koya, sai muka haƙura nake yi mata Qur'ani da hadisi. Su Baɗɗo kuma Qur'ani, hadisi, da koyoon baƙi nake yi musu. Cikin sati guda ba sai makaranta ta girma ba, maƙotansu Dada duk suka shiga makarantata ina koyar dasu inajin nishaɗi, in sati yayi su bani kuɗin laraba nera ashirin_ashirin. A cikin sati uku na tara ɗalibai talatin cib duk sati ina samun kuɗin laraba nera ɗari biyar banda su Baɗɗo. A cikin sati na huɗune nake sanar dasu zanje birni amman bazan jima ba in sha Allah. Gaga_gaga na shirya tafiyata ranar talata na shiga Kano da tsaraba rigi_rigi kai tsaye gidan uwani na yada zango. A tsakar gida na tarar da kishiyarta tana wanke kayan jarirai, Ummi ƙanwar uwani kuma tana wankin kayan jini. "A'a Anty Iyabo har kinzo? Ko dai tun tana nakudar ta kiraki a wayane?" Cewar ummi da tazo ta tarbeni. Ta sauka kenan? Ni da ƙauyenmu ba sabis ya za'ayi ta kirani ranaku kawai na kintata na tawo. Yaushe ta haihu?" Kishiyar Uwani ce ta katse mana hanzari ta ganyar gaisheni a turɓune. Fuskata a sake na amsa mata ni da ummi muka rankaya ciki. Hajiyansu Uwani na ciki ita da Hafizun. "Iyabo kece da magribarnan maraba" Wallahi kuwa Hajiya. Saina taki sa'a ashe ta sauka?" "E ta sauka, zauna ga ƴar taki ki ɗauka, bata fi minti talatin da haihuwar ba, ita ko wanka batai ba" Zama nayi na amshi yarinyar tubarkalla da'ita ga hanci. Gaisawa muka yi da Hafizu sai naga ba yadda muka sababa. Hajiyace ta katsemun tunanina ta hanyar cewa da Hafizu. "To ya rage a tsakaninka da Uwani Hafizu. Ta riga data haihu idda dai ta ƙare. Sai kaje ku sasanta inta amince maka sai a sake sabon ɗaurin aure. Ni kam tunda Iyabo ta iso zan tafi" Hajiya ta tashi ta fice. Ni wallahi mamaki ma ya hanani yin sallama da Hajiya. Uwani kawai nake kallo, ita kuwa sai shan shayi take yi a ƙaton jug. "Iyabo tunda Allah ya kawoki komai zai zo da sauƙi nasa. Kuskurene ya shiga tsakaninmu da Uwani har takai da na furta mata kalmar saki. To Allah cikin ikonshi ɗazu ina tasha ana mun lodi sai kawai sanarmun da haihuwarta akayi. Kinga idda ta sauka a kanta. Ki tayani bata haƙuri ni ko nawa take so na sadaki zan nemo in bata. Inma so take yi in yi mata akwati wallahi zanyi" "Iyabonce zata sa in koma sabida uwatace? Ai wallahi kama ji na rantse na gama aurenka kenan. Kuma yara zasu koma hannunka babu yaron da zan riƙe. Daɗine ma yayi maka yawa in ciyar da kaina da yarana, in biya musu kuɗin makaranta akan mitsiyaciyar matarka mai kama da bulugari Ni Hafizu ka jefa da kalmar saki. Ai aure da kai har duniya ta naɗe. Gashi can za'a shiga sallah kayi da jiki" Kasaƙe ni dai na kasa magana. Tashi Hafizu yayi yana sharce zufa har ya kai bakin ƙofa yace. "Iyabo ki taimakeni. Wallahi inason Uwani. Jarabarta ce duk taja mana. Jeka Hafizu zamu tattauna in sha Allah za,a samu haske" Godiya yayi mun ya fice. Uwani kar kiyi haka. Ki tuna Hafizu na sonki sosai. Sannan ki duba yara" "Iyabo in kina so ƙawancenmu ya cika. To ki kaso aurenki kizo ki maye ma Hafizu gurbina mana. Ni ba tsuntsun soyayya bace da soyayya za tai ta jan rayuwata kamar ke da kika zama bagidajiya ba Jibakki yadda kika dawo fa ruwan kwara_kwara. Ni bana ma son namiji mai nacin soyayya kin ganni inason a dinga barina in samu sarari, ba ko da yaushe nake son takura ba.' Leƙowar ummi ce ta katse Uwani. "Anty