← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 199 OF 237

Sashe 199

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dai babu wanda na sani bansan inda zan nufa ba. Titi kawai naje na tsaya inata kallon motoci suna wucewa. Lagos gidan cunkoso kenan. Motoci iri iri sukaita wucewa, ga jama'a a ƙafa sai yawo suke yi. Da dai naga wankin hula yana shirin kaini dare saina koma cikin tashar na shiga rumfar wata bahaushiya mai saida masa da tuwo na zauna. Wata matar shagon ta iso inda nake tace. "Tuwo ko masa kike buƙata?" Masa zaki zuba mun. Amman kafinnan dan girman Allah ku taimaka mun da masauki ni baƙuwace bansan kowa ba a garinnan" Kallona tayi da kyau ta dubi yaran hannuna tace. "Amman baiwar Allah da yarannan kika shigo bariki maimakon ki barsu a gidan ubansu. Nasan bazai wuce takaicin rijalu bane ya sa kika fito yawon duniya ba. Zan kawo miki tuwo in mun tashi zan haɗaki da Hajiya mai shagonnan ƙila ta taimaka miki da masauki amman bafa kyauta ba. Nan Lagos kika shigo kowa kika gani a nan kuɗi ya fito biɗa. Masar nawa zan sa miki?" Nera ɗari uku na bata ta wuce bata jima ba ta kawo mun masar. Hassan na sunto na soma ba, daya ƙoshi na ba Usaini ma kafin na ci nima muka sha ruwa na takure a gefe. Jama'a sukaita shigowa wannan shago. Dare yanata tsalawa. Wannan dai mata itace ta zo inda nake tace. "Baiwar Allah kizo muje office Hajiya ta ganki." Miƙewa nayi da saurina nabi bayanta. Ma'aikata sai miƙa ma mutane abinci suke yi. Ga ƴan mata tsula_tsula cikin kwalliya suna tafe da yanga. Matanma kamar zaɓarsu akeyi ko wacce babu muni a tattare da'ita. Cikin ofishinnan muka shiga. Wata shirgegiyar Hajiya kamar ni tana zaune ga kuɗi cikin robar fenti babba a gabanta sai haɗasu take yi. Ga wasu bandir_bandir a gefenta ta haɗa. Taci uwar bilicin, ga kwalliya ta alfarma sai cin cingam take yi" "Hauwa wannan ce matar da kike faɗamun, yo baiwar Allah zaki fito bariki da yara har biyu keko taya zaki samu aiki? A_a wallahi ni bazan iyaba. Kuma kinyi ƙiba da yawa ma'aikatana kinga ƴan madaidaitane masu jawo hankalin maza dai." Ni dai nayi shiru ina saurarenta. Wacce ta kira Hauwa tace. "Hajja Mama a duba na fahimci kamar gudowa tayi, dan ko jaka bata riƙo ba na kaya. A duba dai" Da harara matar ta bini. "Menene sunanki, kuma daga wanne garin kike?" Sunana Iyabo Hajiya. Bansan daga wanne garin nima nake ba, amman dai garinmu da nisa gaskiya " "To dake dai naji kince sunanki Iyabo. Ke beyerabiya ce, ku yarbawa an sanku da juriyar aiki. Zan taimaka miki zan tafi dake gidana zaki zauna a hannuna. Amman duk sati zaki biya nera dubu biyu kuɗin ɗaki, kullum ɗari biyu ake biya. Ina bayar da abinci wannan ba matsala bane tunda kune masu aikin abincin. Zan duba inga a wanne gurbi zan saki. Sai dai inada sharaɗi in kinsan yaranki masu kukane to wallahi kona ɗaukeki zan sallamekine ehe. Bazai yiwu na rufe shago biyun dare ba inaso inje in huta ace kuma yara sun hanani bacci ba" Jikina na rawa na dinga jero mata godiya harda tsugunnawa. A ofishin na rama sallolin da duk ake bina. Na zauna a gefe Hajiyannan sai kuɗi take ƙirgawa, Hauwa na sake juyo mata kuɗin daga ƙaramar robar fenti. Yadda tsarin ofishin yake, wata ƴar ƙoface kamar taga amman ta gilashi. Anan masu siyen abinci suke biyan kuɗin abincin, sai suje su zauna a tura yara su kai musu abincin. Hajiya kuma tana Hakimce tana tattare kan kuɗaɗenta. Wayarta ce tai ƙara ta duba tana ƙirga kuɗi. "To yau kuma an tuno dani kenan Dr manya" Wayar ta ɗauka tace. "Likita bokan turai kaddai ka shigo Lagos ne yasa ka kirani? Dan na fahimci abincin Hajja kaɗai kake son ci, da zaran ka bar Lagos kiran waya ya ƙare" Na cikin wayar bana jin abinda yake cewa. Jim tayi dai tana saurarenshi kafin ta ɗaura da cewa" "Ai in akwatin aure kake so ka samu balle akwatin me jego. Kai dai turo kuɗi kawai Alhaji za'a haɗama akwatin kayan fitar suna. Ina da tela duka ɗauka wannan wanda ya taɓa ma Amaryarka ɗinkin kayan lefe? To shi in harda dinkin ma za'ayi maka duka" Sai ta kuma tin jim. "To to Shikenan Alh sai na ji Alart sai kuma ka faɗamun wacce kala uwargidan tafi so. Sabida asai mata kayan da zai ƙayatar da'ita. Sai na jika likita bokan turai" Ta ajjiye wayar tana dariya tana ƙirga kuɗi abunta. Muna wannan shago har biyun dare masa dai ta ƙare tas tuwonne ma akwai ragowa. Nan aka shiga hada_hadar tattare kayayyakin daya dace. Akayi wanke_wanke da gyaran wajen tas. To a gaskiya zagewa nayi na tayasu aiki. Saina fahimci kazarniyata ta burge Hajja dama ni fatana kenan. Muka kama hanyar gida da wata akwalar motar hajja. Kusan mu rai goma a mota ɗaya gashi ni ba kaɗan ba ga yara a bayana. Sai sakkosu nayi aka riƙe mun su na saka ƴan mata biyu a cinyata suka zauna. Munyi tafiya mai nisa kafin muka shigo wata unguwa. Abun mamaki sai nake ganin mutane a layin kamar ma ba tsakiyar dare ba. Ga masu siyar da abinci nono_nono a jejjere. Ga kuma mutane a titi suna baccinsu, wasu a ƙofar masallaci, wasu akan teburan masu kayan miya. A wani gida da akayi mishi katangar kwano muka tsaya duk muka sassauko. Ni dai biye dasu nake har cikin gidan. Hmmmm fasalta ƙazantar dake cikin wannan gida ɓata lokacine, masu saurin amai da tashin zuchiya sai suyi. Haka dai muka shiga wani ɗaki ɗan ƙub ciki da falo. Ɗakin duk shirgi, ga mata har guda biyar a kwance, banda waɗanda muka tsallake muka shiga. "Ke Iyabo. Ku raɓa ta can lungun kujerar zaki ɗanfi samun sakewa kar a tumurmushe miki yaranki, naga ma basu da rigima sai baccinsu suke yi." Cewar Hajja Mama kenan. Inda ta nunamun na wuce da yarana. A tantagaryar ƙasa na kwanta, na shinfiɗa mayafina na shinfiɗe yaran. Nayi shiru inata kallon sama kawai, so nake inyi tunani akan wani abu ko guda ɗayane, amman koma nace zanyi iyakar abinda nake tunowa hanyar motane kawai inna matsa sai ciwon kai da tashin hankali kuma.Idanu na lumshe na shiga kallon matan dake cuccure a waje guda, sai tusa suke sakewa ɗaki ya cika da wari, ga masu gwarti sai ja da sakewa suke yi. Banci ya ɗaukeni baifi da minti goma ba akayi kiran assatu a masallaci. Kowa saiya tashi. Kafin sallah gidannan ya karaɗe da hacaniya sai girke_girke akeyi matan gidan na abincin saidawa. Hajja Mama ma tuni ta ba da oda an gangama tukwanen girki, ni kuma muna ta wanke farar shinkafar masa ni da wata mata dan zata yini a shekaru" "Jiya kika zo garinne baiwar Allah. Na ganki da yara kuma. Ai yawon bariki ba'a fitowa da yara. Ko gudowa zaki yi ba sai ki bar yaran a wajen ubansu ba. Nifa yarana bakwai haka na tsallako na barsu kuma ni da komawa ganinsu saidai a darussalami" Na dubeta nace. Jiya nazo, yara bani da inda zan ajjiyesune." "Sai dai zasu iya hanaki yin aikinki yadda ya kamata. Koma naga kina da ƙwazo. Sunana Batula kefa?" Iyabo sunana." Muna dai aikinnan tana taɓomin hira haka, dake Batula irin matannanne masu saurin sakewa masu fasa cikinsu ga kowa. Muna gamawa aka tashi injin niƙa. Ni na niƙa shinkafar masarnan nayi mata niƙan daya kamata. Aka saka kanwa da gishiri aka rurrufe. Sannan fa lokacin sallah yayi, masu yin Sallah muka je muka yo, muka dawo, waɗanda suke fashi suka ci gaba da aikinsu. Ina idar da sallah ƴan biyu suka tashi, wata budurwa dake zaune gama wayarta kenan tace. "Wannan yaran ba dai kyau ba gaskiya, gashi sunyi kama sosai" murmushi nayi mata nayi godiya na saɓesu muka fito . Hauwa inason zansai tawul ɗin nabkin ne, yarannan kafin su tsuleni da fitsari." Hauwa ta ɗago tace. "Kawo kuɗin aba yarinya ta karɓo miki" Kuɗin na koma naje na dakko" "Ɗauko kuɗinki ki ɗaureshi a mararki kafin kiji wayam wallahi. Ba'a ajjiye kuɗi sakaka, wallahi har a jikinki sai a lalubeki kina baccin asara a yashe kuɗaɗen. Iyami zo ki karɓo mana famfas maza" Wata yarinyace a guje tazo ta karɓi kuɗin ta tafi. Hauwa ta kaɗa kai tace. "Kin ganta ƴar gaba da fatiha ce, muna zaune uwar tayo cikinta ta haifeta gashi muna morarta" Idanu na zaro zanyi magana ta rufe mun baki da hannunta. "Kije ki kama aiki, ki tambayo Hajja Mama me zakiyi" A wajenta na bar biyu naje na sameta a hakimce tana shan tea da biredi da wainar ƙwai. Hajja Mama mai zanyi kuma?" Saida ta gama mulki tace. "Za'a soma sallamar siyan tuwo ɗumame. Kunu zaku dama ke da Batula ku sassallami masu cin tuwo. Da rana a gidannan anayin ɗanwake. Dake da Rabi'a, da Samira, da Batula, da waccan tsohuwar karuwar zaku dinga yi. Dama suna ƙorafin aikin yana ɗan musu yawa sai ki kama musu. Bazan iya fita dake shagona da yara ba, aikin ki zai zama na gidane kawai. A wata kuɗinki nera dubu goma, kullum kuma kuɗin wajen kwanciya ɗari biyu, in kuma wata zaki biya dubu biyu. Abinci sai kin ture. Ba'aimun wasa da kasuwancina. Bazan hanaki yawonki ko kula maza, ko karuwai ba. Amman a tabbatar an gamamun kasuwancina tsab tukunna. Banda ɗauko cikin shege kuma na gaji da ƴan dakan kuka a cikin gidannan. Iya wannan shine sharaɗina, da zaran kun dama kunu kusha kuci tuwo ku ƙoshi ku samu ƙarfin yin aiki. Hauwa zata fito tuyar masa." Nagode sosai Hajiya, Allah ya sa ma kuɗin albarka." Daga haka na fito muka shiga aiki bayan munci mun ƙoshi. Ƴan biyu sunata jan ciki a tsakar gidan suna wasansu mu kuma munata aikin sakun ɗanwake, su Hauwa suna tuyar masa. Sai da akayi azahar Hajja Mama ta fice da tawagarta zuwa shago. Ni kuma naje nayo Sallah na dawo muka ci gaba da sallamar masu siyan ɗanwake. Abinda na lura salla bata damesu ba a gidan neman kuɗin kawai suka saka a gabansu. "Iyabo ga abincin ranarki ke da yaran" Batula ta miƙo mun ɗanwake yaji mai da yaji, yayi daɗi sosai kuwa, gashi
Chapter 199 · 0% Book details