← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 237

Sashe 80

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

mu ka yi kamar yadda ta umarcemu. Cikin sakewa p.a ta soma yi mana bayanin da tuni ya kwance lissafi da notikan kaina. Uwani kuma sai hararar p.a take yi. "To harkace ta arziki tasa na kira ku. Matsawar kuka amince da abinda na kawo muku wahalarku tazo ƙarshe. Ai kamarku kun girmi gidan aiki sai dai a haɗaku da manyan alhazzai, ko manyan hajiyoyi da zaku dinga ban gisiri in baka manda. Ku ba yara bane kun dai gane wannan lissafin ai " Uwani ta balbalin ta miƙe cikin jaraba da nasifa tana nuna p.a "Mu rasa a ƙasar da zamu yi iskanci har sai mun zo Riyahd a inda muke jin ƙamshin ɗakin Allah. Kuma har kike mana tayin maɗigo? Ta Allah ba taki ba Allah ya tsaremu da sharri irin naki tur da tsufa da furfurarki dattijuwar biri. Iyabo muje kinji kafin in hallasa in kashe matsiyaciya." Jikina a mace na miƙe muka fice. Fitar da tayi dai_dai da dawowar Hajiya Babba da tarin mata. Matan aure da ƙananun yara da ƴan bana bakwai. "Sannu da dawowa Hajiya Babba" Uwani ta faɗa a tsorace wani kallon uku saura kwata tai mana dai dai fitowar pa. "Ince dai lafiya ko?" A'a ba lafiya akwai gagarumar matsala" Nayi maza nace. Kallonmu tayi, ta kalli jama'arta da su kuma daka gansu a galabaice suke. P.ai ki ji da waɗannan ayi musu yadda ya dace. Ku kuma mujenku." A baya muka bita izuwa inda take ganawa da baƙinta. Labarta mata halin da Uwani take ciki nayi, da halin da nake ciki a nawa gidan aikin. Tare da roƙon a sake mana gidan aiki, kuma ta taimaka a zubar da cikin jikin Uwani. "Lallai na ɗebo jagwal, ko kuma in kiraku da ƙaƙai. Kusa kunnuwa da kyau a garinnan ganin maganin zubar da ciki ai aikine jajazur. Za a iya kamaku ma matsawar kuka zubar da cikinnan. Wata shida da kama aikinku sai tarin matsaloli. Shi wanda ya ɗibga miki cikin yasan abinda ya aikata kin faɗa mishi?" MRS BUKHARI Tofa wasa farin girki.
Chapter 80 · 0% Book details