Sashe 109
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
18 Dana sunkuya sai naji sanyi sosai yana busowa ta ƙasan gadajen marasa lafiya. Nayi maza na cire hijabina na sake lulluɓema Dada kanta dashi, na gyara mata kwanciyarta, ko fulo babu a gadon. Dama jar abayace a jikina mayafinta yana ɗaure a kaina saina cire mayafin nayi yafe irinna takari mazauna saudiyya. Nayi zamana a gefen katifar Dada. Likitocine suka shigo ward ɗin, suna bi gado_gado suna duba marasa lafiya tafe_tafe har suka iso namu wajen. Fayal din Dada suka buɗe suka ɗan duba. Suka auna bugun zuchiyarta, da zafin jiki, sai wata allura da suka ƙara mata a cikin ruwan dake ɗaure a hannunta. Ruwan sai yafi minti biyar yake ɗigowa. "Sannu ko Allah ya bata lafiya. Gobe za'ayi sallama sosai a ɗakin zaku samu gado da safe. Amman ya kamata ku nemo bargo wanda zaku yi amfani dashi sabida akwai sanyi sosai. Sannan ƙarfe biyu ruwan dake ɗaure a hannunta zai ƙare, to zaki iya nemana a office ko?" Godiya nayi ma Daktan suka wuce zuwa gadonsu Sumayya. Sai ga Baɗɗo ta dawo. Baɗɗo zo ga abinci kici naga kamar jego kikeyo ko naga goyonki ƙaramine" Ta zauna ta soma cin abincin kenan muka hango Yaya Hamma da kaya niƙi _niƙi, bargone, tabarmane, da bakko ɗauke da filas na ruwan zafi dana abinci. Da sauri na tareshi a hanya na amshi bargon. Murmushi mai taushi ya sakarmun yana ƙaremun kallo. Nima murmushin na sakar mishi har saida haƙoran makkana suka fito. Sannu da dawowa Yaya Hamma" "Sannu Jabuna" Ƙarasawa mu ka yi. Yaya Hamma da kanshi ya shinfiɗa mana tabarma a gefen katifar Dada. Bargon daya kawo saina rufa ma Dada na cire na asibitin nass a gefe dan wanda ya kawo da gani yafi ɗumi. Abinci ya ciro a cikin bakkonnan. Filas ɗin ruwan kuma ya miƙo mun na ajjiye a gefe. Harda gwangwanin madarar gari kwalin lipton, sai sigar kwali mai zaki, wasu na kiranta mai iyali. Da ruwan Swan na gora manya biyu sai kofuna, da robobin cin abinci, da lokali. Allah ya saka da Alkhairi sannu da ƙoƙari a darennan ka koma gida Yaya Hamma?" "Ai dole in koma, tunda kinga mun fito hankali ba a kwance ba ba'a ɗakko komai ba. Dole ana buƙatar bargo tabarma, abinci shima dole aci. Baɗɗo zuba muku abincin kuci. Ni zanje wajen maza a waje in zauna. Jabu in kinci abinci ki sameni a waje" To Shikenan Yaya Hamma mun gode ƙwarai" Baɗɗo ta zuba mana jallof ɗin taliya da wake taji bushasshen kifi. "Aradun Allah ba Hama bace tayi wannan abincin ba. Ai mu tuwo muke ci kullum. Ko ita tayi ai ba zata bari Hamma ya kawo miki ba." Bayan na kai nomar taliyarnan bakina sai nace. Me yasa kikace haka Baɗɗo?" "Adda Jabu Hama macece mai mugun kishi kasancewarta fulanin Camaron. Daga can suka yi ƙaura suka dawo Banyo. Tunda labarin soyayyarki ke da Yaya Hamma ya faso cikin Jaɓɓi hatta ni Hama zaman gugar jigida muke yi. Adda Daso kuma bayan tafiyarki ta dinga kunno da maganganu iri_iri, suka ɗinke da Hama. Har wajen Malami suka je, wai a ɗauke hankalin Yaya Hamma daga gareki. Dan ya shiga kewa da damuwar rashinki sosai. Wannan ramewar da kika ga yayi duk na tunaninki ne. Saboda ke ya sai salula burinshi kawai yaji labarinki. Ya sake ninka hidimar da yake yima Dada duk sabida ke." Baki na riƙe ina mai cike da mamakin Daso. Da mamakin irin son da Yaya Hamma yake yi mini, son da kunya da ƙauyanci suka hana a furta mun. Amman ina kyautata zaton a darennan zai sanar dani tunda dai nadawo. Ke Baɗɗo kinsan abinda kike faɗe kuwa. Dason da ita za'a haɗa baki dan a cire ma Yaya Hamma sona tana jinina, kikace sun ɗinke da Hama?" "Nasan abinda nake faɗa Adda. Adda Daso bata sati sai tazo wajen Hama, haka itama Hama bata kwana biyu sai taje gidan Adda Dason. Su shiga ɗaki suita ƙus_ƙus" Kai na jinjina nace. Dason tayi aure kenan?" "Ta yi aure a Girei har da ƴarta mace Meramu" Ajjiyar zuchiya na sauke. Da naji a inda tayi auren. To amman ke yaya akayi kikasan sunje wajen malami dan a ɗauke hankalin Yaya Hamma a kaina?" "Adda wallahi sunje. A bakin ƙawar Adda Daso naji wannan labarin. Wajen zamanmu ɗaya inda muke kai nono. Ni ina siyar da nono zalla, ita kuma tana siyar da dambu, da fura" Hmmm to ta Allah ba tasu ba. In Allah ya ƙaddari zamu yi zaman aure ni da Yaya Hamma, Babu wani mahalukin daya isa ya shiga tsakaninmu. Haka in Allah bai nufa ba, duk yadda muka kai ga son hakan to bazai yiwu ba." "Hakane Adda Jabu. Yaya Hamma gaskiya yana sonki sosai. Kuma yana da sauƙin kai duk da Hama tana tunzurashi wasu lokutan " Haka dai muka gama cin abincinmu, tana bani labari. Bari inje in sami Yaya Hamma ina zuwa. Ki dinga lura da Dada." Miƙewa nayi na fice daga ɗakin. A takure a wani benci na hango Yaya Hamma yana saye da wata koriyar suwaita ya tuttura hannayenshi duka biyu a ajjihun rigar. Yana hangoni ya miƙe. Muƙu_muƙun sanyi akeyi musamman a wajennan, cikin dake akwai numfarfashi da yawa sanyin bai kai na wajen ba. Isowa nayi inda yake da sallama a bakina. "Ameen wa'alaikis salam babbar mace, ina mai farin cikin sake yin tozali dake a lokacin da banyi zato ba balle tsammani. Dan mafarkaina a kanki nuna mun suke yi kamar kin barni har abadane ɗauke da nauyin da babu wata mace da zata iya sauke mun face ke. Barka da shigowa najeriya" idanu muka ƙurama juna. Wallahi soyayya duniya ne, jina nake tamkar akan yaya Hamma na soma soyayya a kab rayuwa. Son da nake yi mishi a yanzu ya doke son da nayi ma Burodami Debisi. Kazalika ya doke son da nayi ma Gwadabe. Illahirin jikina amsa saƙon soyayyar Yaya Hamma yake yi wanda yake isarmun ta cikin fararen idanunshi. ( Iyabo yau bake ba bacci dan su Khadija maidoki , m Farida Ammar, ummu nabeeha, maman yasser, maman Twins, Uwal matasa da sauransu sun isheki. Mamanmu Hajara Aliyu dai bansan ko zata yi muku uziri ba) A tarihi ansan Fulani da jarumta wajen nuna soyayyarsu ga mace, hakanne yasa kafin saurayi ya samu matar aure dole saiya fito filin shaɗi ya nuna jarumtarshi kafin ya samu abokiyar rayuwa. Matansu kuma sunfi son jarumi ba lusari ba, jarumin da zai fito filin daga ya nuna bajintarshi. "A ina alƙawarin da kikai mun ya kwana. Ina fatan babu wanda kika mallakama zuchiyarki?" Idanu na lumshe bansan sanda nace dashi. Babu wanda na bashi damar samun gurbi a zuchiyata Yaya Hamma. Na kasance mai girmamaka fiye da tunaninka." Wajen zama ya nuna mun da hannunshi. Dariya nayi mishi na zauna, shima ya zauna muna fuskantar juna. "Bani labarin tafiya, da fatan kunci nasarar samun abinda aka fita nema ko?" Alhamdulillah abinda akaje nema an samo. Da ba dan na shigo na tarar da Dada babu yadda take ba, dama da maganar siyan gida zan yi. In ɗauketa daga cikin wahalar da take ciki. To Allah Allah ya yanke mata wahalarta, sai dai muyi fatan Allah ya bata lafiya " "Ameen. Ba dai sayen gida ba, sai dai sayen fili ko? Yuguda yana harkar gini koshi zai gina mata ɗan ɗakin da zata yi rayuwarta, da ɗakin du Cubu. Yusufu shi yana can gidan yana kiwo shi Baffa bazai bari ya dawo hannun Dada ba." Dubanshi nayi nace. Filin yana iya kaiwa nawa Yaya Hamma? Dan da so samune so nake kafin a sallami Dada an gama komai sai ta tare a gidanta in Allah ya tashi kafaɗarta, dan nasan ba zata amince ta bar mahaifarta ba". Dariya yayi mun yace. " Tab ai mutuwace kaɗai zata iya raba Dada da Jaɓɓi lamba In akwai kuɗi a hannunki filaye akwaisu, me gari zan samu ya nuna mun filayen dake ƙasa sai mu siya yasa hannu a baki takaddarki, filin baya wahala har masu saye ake nema. Ko filin dubu talatin ya isa a fitar da ɗakuna uku da tsakar gida da banɗaki" Abinka da ƙauye ni kuma a lokacin akwai kuɗi a jikina sai nace. To a nema mun guda biyu a waje daban daban Yaya Hamma zan siya" Kallona yayi yace. "Me zaki yi da biyun?" Nima shi nake kallo nace. Inaso zan ginane in ajjiye a matsayin kadara kudun kar kuɗin su lalace" Sai yayi murmushi ya fuskanceni da kyau yace. "In kina jin maganata A'a ba zaki siya ba. In kadara kike so ki sai shanu ko awaki ki ba Amaduyal ko Yusufu su dinga kaɗasu jeji suna miki kiwonsu. Yanzu zaki zama Hajiya. Fili ko gida a ƙauye irin namu bashi da wata daraja. Abin kiwonki kuwa kullum daraja suke sake yi, kuma ko da yaushe kika matsu zaki siyar da abunki ki karɓi kuɗinki ba tare da wani ma yasan halin da kike ciki ba" Jinjina kai nayi, na kuma yi na,am da wannan shawarar. Shirune ya biyo baya na wasu lokuta. Ko wanne cikinmu da abinda yake juya tunaninshi. "Jabu" Naji ya ambaci sunana da wata iriyar muryar data tayar da tsigar jikina, wata kasalace ta sakko mun da ƙyar na samu zarafin amsawa a hankali. "Yanzu in ɗan ƙauye kamata yace zai aure ki kina ƴar birni kuma Hajiya zaki bashi dama ya aureki?" Wayyo Allah daɗi inji ɓarawon takanɗa a raina nace anzo wajen. A fili kuma nace. Me zai hana in aureshi matsawar yayi mun? Zaman birni, da zuwa Saudiyya ba hujja bace da zan riƙe wacce zata nesantani da abinda nake so ba." Shiru yayi yana nazari can sai ya furta. "Ina sonki Jabu. Tun lokacin da labarin mutuwar aurenki yazo kunnena naji kin kwanta mun a raina. Tsoro da fargaba su suka hanani fasa wannan sirrin. Amman abun mamaki labarin sonki da nake yi ya karaɗe Jaɓɓi. Jabu zaki iya aurena kiyi rayuwa dani kamar yadda matanmu suke rayuwa damu, zaki girmamani ki yi mun biyayya kamar yadda matanmu ke yi?" I danuna na lumshe sanyi da nitsuwa suka ratsa zuchiyata da dukkan rassan jikina. Allah kawai nake ambato a zuchiyata. Yaya Hamma tabbas nima ina sonka, mu ba