Sashe 208
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
mantuwa. Ke yarinya ke kika iya shigowa Lagos. Ke daga gani ƴar albarka ce kin rabu da iyayenki lafiya." Ni dai tashi nayi na koma, yana tsaye inda na barshi. Assalamu alaikum" Nayi mishi sallama ya amsa a hankali. "Kiyi haƙuri zaki ce na fiye naci ko? Wallahi baki mance komai ba so nake in sake dai ganinkine" Murmushi nayi, shima murmushin yake yi mun. Mun sake jimawa muna hira kafin dai na samu da ƙyar ya tafi nima na shige gida. Kuɗin daya bani na miƙa ma Hajja Mama. "Kuɗin Bala kawai zaki cire ki bani. Ki adana kuɗinki, a cikin ledojinnan dai a zazzage in zaɓa" Na ƙirgo kuɗin Bala na bata. Hauwa ma na bata kuɗin data aramun kana na zazzage ledojinnan. Ledar farko kayan kwalliyane da turaruka. Leda ta biyu kazace gashasshiya, sai cake da lemukan kwali. Ɗayar ledar kuma biskit ne manyan da alawa kala_kala. Kayan kwalliyar Hajja Mama ta ɗiba kawai, kazar ma tace ba zata ci ba. "Yaya kuka yi dashi to?" Cewa yayi shi aurena zaiyi. Amman na faɗa mishi da so samune inaso in yaye yarannan tukunna. Sai yace shi ta ɓangarenshi ai babu wata matsala" "Da kinsan waye shi ƙila da in yau tace a ɗaura auren zaki yadda. Wallahi ni da farko nayi tunanin ko sha'awarki ce kawai yake yi, duk da nasan ba mutumin banza bane gashi da kulawa da iyali. Ai kinanan na haɗa ma matarshi akwatunan suna kuɗi ya kashe mata sosai da sosai. Ki nutsu ki kamashi, ɗan kiran waya, ɗan tura saƙon Barka da da safiyannan, dan kirsa da kisisinannan duk kar kiyi wasa kinji ko" To Hajja Mama in sha Allah. Na kuma gode sosai." Na kwashe kayana ɗan ƙwalam da maƙulashenmu muka ci ni da su Hauwa, ƴan biyu kuwa sunyi baccinsu. Kunga wayar ɗaya bani, tashi ce ma ya zare sim ɗin ya mayar da nawa." Batula ta fisge wayar tace. "Black berry razor? Tabb wannan wayar ta manyace sosai. Gaskiya Ghali yayi miki babban kamu" "Ku mu kwanta kar gobe mu kasa tashi" Ni dai har su kai barci idanuna biyu ras sai juyi nake yi ina tuno Usman ina murmushi. Bansan sanda bacci ya kwasheni ba sai ji kiran sallah kawai nayi. Ina miƙewa sai ga kira ya shigo wayar. Lambar naketa kallo kafin na ɗauka na kara a kunnena" "Amincin Allah ya tabbata a gareki gimbiya. Da fatan kin tashi lafiya ko?" Idanu na lumshe kana nace. Ameen tare da kai. Da fatan kaima ka wayi gari cikin ƙoshin lafiya?" "Uhm lafiya ba lafiya ba dai" Dariya mu ka yi duka kafin ya ɗaura da cewa. "To cikin tunaninki na kwana. Yadda kikasan lokacin aurena na fari. Juyi fa na dingayi ina tunaninki da furfurata. Gashi bazan samu damar tsayawa kamar yadda na alƙauranta miki ba. Da asufa suka suka ni daga can Gombe yarona ba lafiya sun kwana yana suma. To shine nake son inje inga halin da yake ciki. Duk mun shiga tashin hankali." Assha Ubangiji Allah ya bashi lafiya. Yarone ƙarami?" "Uhm jinjirine ma, uwar ta kirani sai kuka take yi. To zan dai wuce zuwa anjima inna sauka zamu yi waya. Ki shafa mun kan yarana sai anjima" Sallama mu ka yi na sauke wayar a kunnena nayi saurin tashi na ɗauro alwala na yi sallah. Biyu suka far mun da tsotso da ƙyar na yakicesu na nufi bakin aikina. Yau dai cikin farin ciki sosai na wuni zuchiyata fes. Minti_minti sai Usman da murmushinshi ya faɗo mun. Gashi har magriba tayi bai kirani ba balle inji yaya ya samu masu jiki. Ina zaune ina cin shinkafa da miya da latas Batula ta dawo daga unguwa hannunta riƙe da leda ta nemi waje ta zauna. "Kin ko kira Dr a waya kinji ya mai jikin?" Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace. A_a tsoron kira nake yi ko yana tare da matarshi kinga ai ba zata ji daɗi ba ko? Amman tun ɗazu nake jiran wayar tashi" "A_a ba haka za'ayi ba to. Ki rubuta mishi saƙo ki tura mishi zaifi sauƙi" Ai kamar gara kiran wayar ma ko. Kinga bana son haddasa wata fitinar bari dai in kira" Na danna lambarshi na kirashi. Ai kuwa ringing biyu sai ya ɗaga. Wata ajjiyar zuchiya ya sauke mun kafin yace. "Ai da harna soma fargabar ko dai ni kaɗai nake kiɗana da rawanane ashe ba haka bane" Murmushi nayi mishi nace. Ba haka bane, ya mai jikin ka sameshi, da fatan ka sauka lafiya?" "Jikin da sauƙi yanzu na baro asibiti. Dama na barine inna gama magana da Alhajinmu inna fito in kiraki kafin in wuce gida, sai kika rigani" Daga haka muka ɓalle da hira dai, kafin daga bisani mu kai sallama. Sai yanzu hankalina ya kwanta. Batula na kamu da yawa wallahi" Dariya tayi mun. "Ai dole ki kamu Hajiya. Kinga muci kaza ki ajjiye wannan jiƙaƙƙiyar shinkafar. Ko ba shinkafar Anty bace? Ai bata iya girki ba ku da kuke siya kuna ƙoƙari. Ni dai ta baje mana kwaɗayi mu kai tayi. Gaga_gaga al'amura suka ci gaba da kankama a cikin kwana goma ni da Usman mu ka yi wani irin shaƙuwa na mamaki. Na fahimci yana mugun son soyayya ashe gaskiya ne da akace dattijai mayun soyayya ne. Yau mun wayi gari ina da babban baƙo a hanya. Tun safe ni da Batula muke ta girki dan ya sanar mun ƙarfe taran safe jirginsu zai sauka kuma abincina yake son ci. Wannan karon jallof ɗin couscous nayi mishi mai wadatar kayan lambu da anta. Sai soɓo mai abarba da kankana. Taran nayi ya kirani yace jirginsu ya sauka. To Shikenan ganinan zuwa ni da ƙawata Batula zata yi mun rakiya, zata taya ni dakko maka yaranka" "To tunda hakan kika tsara amman da ai gidan zan shigo kawai ma ba sai anga matata na sunturi a hotel ba ko?" Sai kunya ta kamani nace mai. To Shikenan bari in sanarma Hajja Mama, sai ka iso" Ina ajjiye wayar na shiga uwar ɗakin Hajja Mama na sanar mata yadda mu ka yi da Dr" "Wannan gidan namu zai shigo? Lallai Dr ke kam yana ji dake. Shi da ko unguwarnan tamu baya iya shigowa sai gashi Dr yau shine zai zauna a ɗakina? To mu yanzu zamu tafi shago in ya iso ki shigo dashi cikin uwarɗakina. Amman yana tafiya ki kullemun kar aimun sace_sacen da aka saba" Kwaɗo da mabuɗin ta bani suka fice a gidan. Sake gyara uwarɗakin nayi duk da dai fes yake nice harda kunna turaren tsinke. Awa biyu sai ga waya yana ƙofar gida in fito in mishi iso.