Sashe 36
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk yanda Burodami Debisi yaso ni da shi mu samu keɓewa Yemisi ta kulle wannan ƙofar a tsakaninmu. Ta cikin idanunshi nake iya karanto labaran dake cikin zuchiyarshi. A haka na wuni cur a waje ɗaya tamkar mutum mutumi. Maƙotanmu da ƴan uwanmu yarbawa su kai ta shigowa jajanta ma Iyaa. Da ƙyar cikin tursasawa da lallami Burodami Debisi yasa na sa lomar abinci a bakina. Har zuwa wannan lokacin hawaye bai zubo mun ba fa, face ruhina dake gasuwa, haƙiƙa kuka rahamane. Sai dab magriba Burodami Debisi ya shigo hannunshi riƙe da baƙar leda shaƙe da yankakkun kayan marmari ya miƙo mun. Harara matarshi ta watsa mana ta dubemu daga sama har kasa ta buga tsaki. Hannu nasa na amshi ledar nayi godiya ciki_ciki, dan wallahi ko magana akayi mun sai in ji kamar in sa hannu a ka inta kwarmata ihu. Ga mita da Iyaa take ta faman yi da kutuntumama Gwadabe da Babala ashariya. Dan da ƙyar Alfa Kulle ya hanata wai ita sai taje ta ɗebo yara ta dawo dasu. Ni kuma wallahi a wannan lokacin har yaran bana son gani, da duk abinda ya danganci Gwadabe. Iyaa ce ta shigo tai ta ma Yemisi faɗa ita da Burodami ashe saɓani suka samu har ta kai da duk haƙurinshi da kau da kanshi sai da ya ɗaga hannu ya mareta. Ita kuma tana taƙamar soja ce ita shine ta rama, rikicin daya tilasta mata baro gida a daren jiya. Nasiha tayi musu sosai, ya ɗauki matarshi suka koma gida. Fitarsu ke da wuya sai ga uwani da Hajiyarta sun yi sallama idar da sallana kenan ban tashi akan sallayar ba ma, ina jan carbi na amsa sallamarsu. "Hajiya kune da magriba haka a tafe, lamarin Iyabo ya tasoki ko?" Cewar iyaa dake gyara zamanta. Hajiya ta kalleni cikin tausayi tace. "Yanzu sai da aka sako yarinyarnan Toyosi duk irin faɗi tashin da tasha, amman dangin mijinnan nata sai da suka ɗauketa akan yaranta?, jiya Tabalbalin take faɗamun samuwar lafiyar mijin fa." Baki Iyaa ta taɓe tace. "Ai tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan duka. Ni Hajiya ina murna da mutuwar aurennan, domin in banda wahala babu abunda take sha a wannan gida. Sai da ta game mishi jinya ta sai da komai nata ɗakinta daga robobi sai tukwane fa, shine zai sako mana ita. Ko da yake kiyi haƙuri Hajiya ku Hausawa baku fiye riƙe aure ba" Gaggaisawa mu ka yi, Uwani ta matso inda nake, su Iyaa ma suna hirarsu ta manya. "Yanzu a wanne hali shi Gwadaben yake sai Allah. Nayi imani duk inda yake cike yake da tashin hankali babu mamaki in akace yana gadon asibiti ma. Amman Iyabo me yasa kika baro su Toye? Kinsan fa wuya zasu sha ƙila ma a mayar dasu ƙauye kinga shikenan an kashe musu rayuwa" Inata ƙoƙarin ganin ƙwalla ta zubo a idanuna amman ina, abu yaci tura, idona ya soye. Sai da na sauke ajjiyar zuchiya nace. Gara su yi zamansu a dangin mahaifinsu zai fi. Wuya bata kisa Uwani da wuya na kisa mu yaran yarbawa da tun muna ƙanana zamu dinga mutuwa, ke kinsan irin gwale_gwalen da muka sha. Gobe asubar fari garin zan bari, kinga in na tafi bazan sake waiwayo garin Kano ba, na barta har abada. Kinga zanyi irin tafiyarnan ai bai dace in tafi da yaran mutane ba. In Gwadabe ya ga yaran a kusa dashi a ƙalla zai ji sanyi" Na ƙarashe maganar a raunace. Ƙirji Uwani ta dafe tace. "Ni Uwani Tabalbalin ina zaki koma to iyabo?" Can Adamawa wajen mahaifiyata nake son in je in rayu cikin ƙannena, domin in samu kafaɗar da zan jingina in yi kuka. Ita kanta Dada akwai wata boyayyar damuwa wacce take cin ruhinta ainun, tun tasowata da wannan ƙuncin nake ganinta. Baki ga yanda take ta ramewa ba Uwani" Uwani dai bata so ba, amman babu yanda ta'iya dole haka mu kai sallama. "Iyabo ni ko duk randa na dawo daga Canada, zan zo Iyaa ta bani adireshinki ko a bangon duniya kike zan ziyarceki. Sannan dan Allah ki kwantar da hankalinki ki rungumi ƙaddararki da zaran kin samu mane mi kiyi aurenki kema ko Allah zai sa ki samu nitsuwa." Nagode sosai Allah ya ƙaddara saduwarmu. Kya dinga leƙa yaran in kin samu lokaci." Na sake magana a raunace. Basu suka tafi ba sai wajen taran dare su kai mana sallama bayan sunci Amala. Inayin sallar isha na naɗe a gado bana son ma Iyaa ta cakaleni da faɗa ko hargaginta, fruit ɗin da Burodami ya kaqo mun shi naci. Wajajen goman dare Alfa Kulle ya kawo mun adireshin rugar da mahaifiyata take da inkiyar shi mijin nata da take aure Mahaifin su Baɗɗo. "Tashi ki zauna Iyabo mu tattauna kinga gobe asubar fari ya kamata ki kama hanya dan tafiyarki mai nisan gaske ce. Kece baki sani ba, sanda muka je ƙauyannan kina yarinya ƙarama" Miƙewa nayi daga kwance na zauna kamar yadda ta uwarceni. "To tunda kin nace sai kin koma hannun mahaifiyarki ai shikenan, bazan hana ki ba. Amman fa...." Sai tayi shiru akwai abunda take son sanar dani, amman kuma kamar bata son faɗe ko nauyi yake yi mata ne ni dai ban sani ba. Sai kawai ta ɓige da yi mun nasiha tare da cewa. "Mijin Uwarki ance jarababbene sosai, dan haka sai ki kula kar ki je ki haɗata rigima dashi a wannan gidan yawa, ga kishiyoyi" Ni dai da Toh" kawai nake amsata harta gama na koma na kwanta. Tsawon wannan dare tunanuka ne barkatai sukaita kai komo a ƙwaƙwalwata da tunanin irin rayuwar da zan fuskanta a rugar da mahaifiyata take, da irin karɓar da shi kanshi mijin nata zeyi mini. Gefe ɗaya kuma tunanin Gwadabe da yaran duk ya addabeni, wayata a can gidan na baro mishi abarshi dan bana son damuwa. Washe gari sassafe na kintsa tsab, Iyaa ta ɗan harhaɗa mun tsarabar Kano, da ƴan canjina. Iyaa Kokodeen kuma ta kawo kuɗin mota nera dubu biyar ta ce in ji Burodami kokodeen yace a bani na mota. Matan gida mai ishirin mai hamsin sai aka gagganɗa mun, nayi musu sallama. Ina fita sai ga Burodami Debisi a mashin bespa, hawa nayi ya kaini tashar mota inda na samu motar Adamawa, na ci sa'a ma motar zata shiga har ƙaramar hukumar GIRAI, daga girai in na sauka sai in kuma hawa motar wata rugar kuma, kafin na sake hawa motar asalin rugar da Dada take Tafiya ce bata wasa ba a gabanmu. Dubu biyar Debisi ya bani tare da miƙo mun wata jakar leda. Nagode sosai Allah ya bar zumunci. Allah ya ƙaddara saduwarmu" Idanu ya lumshe yace. "Ki gaishe mun da Dada sosai. Sai na zo in sha Allah " Sallama mu ka yi ya figi besparshi ya fice. Hanyar da yabi na bi da kallo ni kaina bansan tunanin da nake yi ba. Mu biyu ne rak a motar ni da wata bafulatana mai yara biyu, kuma a seat ɗin tsakiyar Bus muke, Bus ɗin babbace sosai mai layi huɗu ce zata ci mutum goma sha huɗu harda direba. Ga motar ragwargwajajjiya ce soai. Mu dai muna zaune jigum. Ita bafulatana ta kusa dani sai wasa take da yaranta suna yara yaren fullanci. Sai lokacin hawaye ya ɓalle mun dana tuno da nawa yaran. Shikenan su da hawa jikina kuma ya ƙare, haka suma zasu taso ba a hannuna ba, kamarr yadda nima na taso ba'a hannun mahaifiyata ba. Suma haka zan haifo musu ƴan uba ko? Kamar yadda Dada ta haifo su Baɗɗo. Kukane sosai ya ciyoni, dole na saka fuskata tsakankanin cinyoyina na yi mai isata ba tare da Bafulatanar kusa dani ta san halin da nake ciki ba. Shigowar wasu fasinjojinne yasa na share hawayena na ɗago. Suma fulaninne amman maza, harda sarƙar fulani mai duwatsu kala kala a wuya da hannunsu, ga gashi sun tara sosai a kawunansu, ga sandunansu da takalmin roba, sai ƙosai da biredi suke ci suna korawa da lemun limca na kwalba. Murmushi ne ya suɓuce mini kawai. Da ɗaya da ɗaya aketa taruwa a cikin motar, kujerar da nake zaune naci sa'a duk mata ne mu huɗu a kujerar, dukkansu da gani fulanin usil ne, gasu da yara a hannu ga goyo raɓe_raɓe, tun kafin motar mu ta tashi suke ta aikin ciye_ciye. Kasancewar sammako duk muka bugo a tashar duk suke takaryawa masu abincin tasha sai ciniki suke zabgawa. Ni ko ko ruwa bana sha'awar sha balle inci abinci, yinwarma da kanta ta hutasshe da tumbina. Sai da rana ta fito ƙal kafin motarmu ta cika tab, nan aka shiga binmu muna biyan kuɗin mota. Dubu ɗaɗɗaya da ɗari biyar kuɗin motar haka muka bayar, waɗanda suke zaune a injin ɗari biyar. Motarmu ta fita daga cikin tasha ta hau lafiyayyen titi. In banda hayaƙi da jijjiga babu abunda motarnan take yi. Ji kake tututu_tuturtu, gashi bata da gudu sam. Kaina na bakin taga ina kallon mutanen dake tafe a ƙasa ɗaiɗaiku. Wasu kasuwannin ƙauye da gani zasu je ciyo kasuwa, yayinda wasu kuma suka fito neman kuɗi, wasu tallace a kansu maza da mata, yara da manya. Tun ina ganin mutane har na soma ganin bishiyoyi. Jama'ar motarmu kuwa sai hirar nishaɗi da jin daɗi suke yi, yayin da wasu suke gyangyaɗi, a yayin wasu suke ciye_ciyensu, wasu kuma suna kame kamar ni haka. Tafiyace miƙaƙƙiya mu kai ta ta faman yinta. Da azahar tayi muka tsaya a wani gidan mai mu kai sallah a masallacin gidan man. Aka firfito kowa na sayen abunda zaici, dan direba yace ba zai sake tsaiwa ba sai mun isa inda zamu sauka. Masu fitsari nayi, masu ba haya nayi. Gurasa da ƙuli na siya na ashirin, na sha ruwa a randar masallaci, nayi komawata cikin mota. Kai mun ɓata lokaci sosai a wannan gidan mai kafin mu ka kama hanya. Mune har bayan la'asar bamu isa ba, sai yamma sakaliya sai gamu a ƙaramar hukumar girei Allah ya iso damu. Ƙauyan abun sha'awa, fulani makiyaya sunata wucewa da garkunan shanayensu zasu koma gida, shanayen manya lafiyayyu gwanin sha'awa, masu tallar nono mata suma sai wucewa suke da ƙoransu a ɗoɗɗore a kawunansu. Sakkowa mu ka yi kowa ƙafafuwa