← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 237

Sashe 94

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dare babu rana, cikin Sallah ko cikin aikin bautar da nake yi babu lokacin da adda'a take barin bakina. Ina kwance akan sallaya bayan na gama ƙiyamul laili, sai naji kamar a mafarki ana rabani da suturuna dai haka. Kasancewar jikina ko da yaushe a tsamane yake da kafirar gajiya, dole baccina zai kasance mai nauyi, kuma dama bana yi ma da wuri shi baccin. Wallah duk abubuwa da sukaita wakana cikin mafarkina nake jinsu a nawa wautar. Ashe a zahirance suke faruwa dani ni Iyabo. Dare mafi baƙi a gareni, jin hannu da bakin Kariya a inda bai dace ba shi ya dawo dani na kasance a farke. Kaina yaso tarwatsewa baki ɗaya ma. Wuƙa ta zaro a rigar Mamanta ƴar ƙarama, sai kawai ta tsaga mun gefen fuskata. Ko zafi banji ba, dan tafasar da zuchiyata take yi kan abinda take aikatawa dani yafi mun zafi, fiye da yankan wuƙar. "Bana so kice komai. In kika yi yinƙurin yi mun gaddama kasheki zanyi in tona rami in burneki a gona. Kibi umarnina in ƴantaki" To a gaskiya na tsorata da kalamin Kariya, kuma ba barazanace take yi mun ba da gaske take nufin zata kasheni. Maganganun Faty ne suka dawo kaina da labarin yanda wasu daga zuwa gidan aiki ba a sake jin ɗuriyarsu har abada, sai dai iyayensu dake gida najeriya suji shiru. Idanuna a runtse harta gama komai. Kuma abu mafi wahala da ɗaga hankali shine umartata da tayi kan in yi mata sak abubuwan da tayi mun. Naso in turje, sai tayi sauri ta zaro wuƙarnan ta sake kawo mun yanka. Cikin zafin nama na kauce. Babu shiri na soma yi mata abinda take so. Allah ya ga zuchiyata ina mai ƙyamatar dukkan abinda nayi ma Kariya, da dukkan wanda tayi mun. Tun daga wannan rana saina samu rangwame, yawan aiki sai ya ragu mun. Ni dai a kullum ina roƙon Allah akan ya kawo mun mafita, ya kuɓutar dani daga wannan rayuwa baƙa. Nan fa gaga _gaga al"amura suka ci gaba da tafiya a baibai, har wata biyu ta cika. Sai na ke tambayar Kariya yaushe iyayen gidana zasu zo su ɗaukeni ne?. A lokacin muna banɗaki inai mata wanka. Buɗar bakinta sai cewa tayi. "Na siye ki a hannunsu kamar yadda suka faɗa mini suma siyanki suka yi. Abinda nake so dake shine ki cire tunani da mafarkin Najeriya a ranki, ke da Najeriya har abada" Ai sai kuka, sai zazzaɓi, daga zazzaɓi sai babbar jinyar da hatta abinci sai Kariya ta bani a baki. Kuma ta kira likitansu yazo ya dubani. Sati na biyu cur idanuna kullum cikin danshi suke. Wata rana ina aiki a kitchen Kariya ta shigo take sanar dani zasu je Umara in zauna in kula da gidan. Harta juya cikin tsoro nace. Uridu an azhabu ma'akum ila Umara billah. ( Inaso in biku umara dan Allah) Ƙur ta yi mun da idanunta, da Allah ya ɗaurani a kanta sai ta amince mun. Cikin murna na sako kayan jikina na bisu. Muna tafe a mota ina kallon gari, ina lure da komai ina sassaka amala a ko wanne kallon kan titi. Tafiyar bata wasa bace, cikin amincewar ubangijina sai gani a Ka'aba har a jikinta. Kuka na fashe dashi inata roƙon Allah yafiya dan gani nake yi Allah bazai yafe mun kan ƙazantar da ake sani yi dan dole ba. Adda'a nayi na maimaita babu iyaka. Zuchiyata saita samu salama da nutsuwa yau na yi umara gani a ɗakin Allah. A hotel ɗin wajen Harami muka kwana kafin kuma muka koma gida. Naga ƴan ƙasata najeriya, nayi magana dasu na samu farin ciki. Na barbaza idanu ko Allah zaisa in ga wanda na sani a kamfaninmu amman Allah bai haɗamu ba. Amman na samu nutsuwa a zuchiyata in sha Allah na kawo kukana gindin maganin. Allah cikin ikonshi kwana biyu da dawowarmu Umara, da daddare na zage na yima Kariya abinda tafi so, sai murna da daɗi take ji, Allah sai ya matsi bakinta tace. "Zan miki duk abinda zai faranta miki. Zan iya miki komai. Da hikima nace da'ita. Inason ki kaini kamfani zan tura da kaya Najeriya akwai masu tafiya, kuma zan tura ma ƴan uwana da kuɗi" Allah mai yin yadda ya so, sai ta amince ba tare da tayi tunanin komai ba. Ni kuwa a cikin daren na haɗe kayana tsab a wani ƙaton akwati ko tsinke ban bari ba. Kuɗaɗena dama suna ɗamare a marata. Na mance ban faɗa muku ba har setin ɗan kunne da sarƙa, awarwaro, zobe, chain ɗin ƙafa Kariya ta sai mun masu darajar gaske. Washe gari sassafe ta kira uwar ɗakina wannan tsohuwa data kawoni, ita tai mata kwatancen kamfani. Ta kira wani saurayinta ya zo da mota ya kwashemu, da tarin kayana dan na samu alkhairi sosai a gidan. Tafiya muke, ni dai adda'ace kawai a bakina, gabana sai yankewa yake yana ta fa faɗuwa gani nake kamar za'a samu matsala. Tafiyace ashe bana wasa ba a gabanmu, a hanya mu ka yi azahar muka yi la'asar. Muna zaune a wani ƙauye gidan cin abinci sai ga kiran wayar Aliya. Ina jiyo duk abinda take faɗa dan a lokacin harshena na larabci yayi ƙarfi sosai. Sai hantar cikina ta soma tsittsinkewa dan tsoro, gudawa ta taru a cikina. Wani irin mugun kallo Kariya ta watsa mun bayan ta ajjiye wayar. Babu abinda nake ambato sai Allah, nasan shi ne kaɗai zai taimakeni a kan duk tsananin da zan shiga. "Me yasa kike tunanin ni zaki yaudara ki gudu?" Ta furta da harshen larabci. Sai da na ambaci Allah kafin na ɗaure fuskata nace. Na sanar dake komai tun kafin mu fito. Kaya zan tura Najeriya a ajjiyemun. Kuma a hakanma zanje in yi siyayyar kaya in haɗama wacce zata tafi duk a tafi mun dasu. Ba guduwa zanyi ba" Na ƙarashe maganar tawa da sarƙewar harshe. Ta dai nuna kamar ta gamsu da bayanina tunda har muka kama hanya. Bamu muka iso ƙofar gidan da muke ba sai wajajen 1 na dare. Muna isowa wata mota itama tana parker wa kamar tare muke. Faty ce naga ta fito a motar tana tangaɗi kamar mai jin bacci. Da sauri na ɓalle murfin motar na fito. Na sakko da bataliyar kayayyakina. Faty tana hangoni sai ta zo tana fara'a. Bansan sanda na rungumeta muka saka kuka dukanmmu ba. Ashe Saleem da saurayin Faty sun iso daf damu bamu sani ba ma. "Iyabo kice kika ƙare haka, ashe kina raye Hajiya tace kin mutu?" Murmushi nayi nace da'ita. Ban mutu ba ina raye, mummunan hannu na faɗa amman Allah ya kuɓutar dani." Ba sai na jiyo na dubi Kariya nace da'ita. Ni na dawo gida kenan babu ni ba ƙasar Saudiyya ma baki ɗaya Najeriya zan koma" Ranar naga tashin hankali dan Kariya sai ta soma daddannamun ashariya tana fincikata kan lallai sai mun koma. In ba haka ba zata kira askarawa su zo su kamani. Da rikici yaƙi ya ƙare sai Salim ya mun nuni da in koma gefe. To a lokacin har matan gidan namu sun soma fitowa. Cikin hukuncin Allah sai ga Uwani itama ta fito sai raba idanu take. Karab muka haɗa idanu mu kai ma juna murmushin farin ciki. Tana ɗingishi ta ƙaraso kusa dani muka riƙe hannun juna gam tamkar ance za a farraƙamu. Rikici fa ya kai har Hajiya ta fito. Tana ganina itama fa tace. "Baki isa ki koma mun cikin gida ba. Sai dai ki nemi inda dare yayi miki. Har ke Uwani kar wacce ta koma mun cikin gida" Tana faɗar haka sai tace da Kariya karta yarda ta tusani gaba sai mun koma" "Ku shiga mota dake da ƴar uwar taki zan kai ku gidana" Cewar Salim wanda ranshi ya gama ɓaci. Faty ce ta ja hannuna muka wuce ni kuma ina riƙe da hannun uwani dama. "Uwani bari in ɗebo miki kayanki, tunda muguwar matarnan ba barinki zata yi ki shiga ba" Faty amman dake zamu tafi ko? Ni fa tsoro nake ji, kuma wallahi Najeriya zan koma" Ƙur ta dubemu can kuma tace. "Shikenan zan biku har saina tabbatar kun tafi Najeriya sai in dawo, yanzu dai ina zuwa" Nan ta tafi ta barmu, ni ai saina haɗe kaina da guiwata na dinga dirzar kuka kamar raina zai fita, Uwani ma sai shessheƙa take yi. Kayanmu su Salim suka lode a bayan Bot, Faty ta shigo mota muka ɗauki hanya. Salim sai roƙona yake yi akan in daure in yi shiru ya'isa haka. Amman ina wani baƙin ciki da nadamar zuwa ƙasar ke turniƙeni. Duk mun lalace mun faɗa balaoi iri da kala. Tafiyar da mu ka yi bata wuce tafiyar awa ɗaya ba sai gamu a wani katafaren rusheshen gida, mai yalwar filin tsakar gida. Salim na gaba muna biye dashi a baya har zuwa cikin babban falon gidan, inda ya kasance matattarar ɗakunan gidan, da ƙafar bene da zata sada me hawa izuwa sama. Babu kowa a falon a lokacin da muka shiga. Har ya kama ƙafar benen sai ya soma kiran sunan Atika, Atika. Allahu Akbar sai ga wata ƴar burkina fasu ta tawo a guje har tana tuntuɓe jikinta da uniform na masu aiki. Yace ta haɗo shayi da abinci ta kawo mana ɗakinshi. Nan muka haura tiryan_tiryan har izuwa ɗakinshi daya kasance madaidaicin ciki da falo mai shaƙe da kayan alatu. A irin kujerarsu mai daɗin zama muka zauna duk a takure ni da Uwani Faty kuwa a cinyar saurayinta ma tayi zamanta tana yi mishi raɗa a kunne. "Ku saki jikin ku nan gidanki ne ƙawata. Ummi da Abi sun fita, gobe zan haɗaku dasu ku gaisa." Mun gode sosai Allah ya saka da Alkhairi. Faty kema babu abinda zamu ce dake sai godiya" Na faɗa jikina a sanyaye sosai. Waje saurayin Faty da Salim suka bamu, mu kai wanka muka kintsa, na rama sallolin da suke kaina. Sai ga shayi da shinkafa da romon nama Atika ta kawo mana. Bayan munci ne Faty tace. "Yaya akayi Hajiya tace damu kin mutu Iyabo?" Ɗan dariyar takaici nayi musu nacce. Sabida ta siyar dani ba. Kuma ta basu uwarnin karsu sake su barni in fita ko ƙofar gidane. Duk da inna fitan bansan
Chapter 94 · 0% Book details