Sashe 177
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
GWADABE
Ya isa asibitin farkawar Hadiza kenan, tana kukan cikinta na mata ciwo"
"Dole zai miki ciwo É—inki akayi miki Hadiza kibi a hankali." Cewar Anti Badi'a. Suna cikin wannan maganar Gwadabe ya shigo shi da Mammada da abinci.
"Hadiza sannu da jikin" Cewar Mammada kenan. Gwadabe ya karasa kusa da gadon ya dubeta cikin so yace.
"Yaya jikin naki Hadizata, ya sabuwar Baby da muka samu? Wannan Baby ta bamu wahala sosai.
Sannu Anti Badi'a ina kwana?"
Ya ƙarashe maganar da gaishe da Anti Badi'a.
"Lafiya lau Gwadabe. Mammada sannunku fa da haƙuri"
"Yauwa Anti Badi'a. Sannu da kwanan asibiti.Ni zan leƙa Malam zan kai mishi abinci, ina zuwa dan ba jimawa zamu yi ba"
Hadiza bata gane me suke nufi ba sam dake a cikin zafin ciwo take. Ma'aikatan jinyar aka kira suka sake mata allurar bacci ta sake komawa bacci. Huduba Gwadabe yayi ma jaririyar da sunan Babala.
"Gata Anti Badi'a nayi mata huɗuba da sunan mahaifiyata Hauwa Ai mata alkunya da Mami. Ni zanje in duba malam daga can zamu wuce. Amman Shafa zata zo ta zauna dan lallai ana matuƙar buƙatarki a can gidan"
Jaririyar ya miƙa mata ya zaro kuɗi wadatattu ya ajjiye mata ya nufi ward ɗin maza.
Al'amarin jikin malam ya girmama ba'a buƙatar kowa ya shiga ɗakin ma da yake. Abun jawo numfashine a bakinshi, da wasu robobi da ma'aikatan aikin jinyane kaɗai zasu iya sanin menene ( Khadija maidoki ana magana) suke sagale a jikin malam. Kuma likitoci sun tabbatar musu malam ya shiga koma sai dai aita tayashi da adda'a domun ba lallai bane ya tashi. Amman aita mishi adda'a. Ba'a shiga ɗakin sai dai ka hangoshi ta taga yana kwance, lokaci guda Malam ya rame ya zuge saiya sake tsayi da haske sosai.
Jikin su Gwadabe a sanyaye hankali kuma a tashe suka bar Asibitin tare da Amaryar Malam suka tawo gidan tana buƙatar zuwa gida ƴan uwanta sunata kiran wayarta duk sun cika ɗakinta bata nan.
Zuwa yamma sakaliya sai gasu Babala da su Goggo Iyatu da Goshi, da Yaya Hambali, da Yaya Halima, sai Yaya Haula.
Jim kaÉ—an da zuwansu sai ga su Bara'u suma sun iso.
Abun mamaki a cikin taron mata Gwadabe ya kwashi su Bara'u suka je yima su Babala ta'aziyya. Babala ta yi maza ta fice a ɗakin ma baki ɗaya. Goggo Iyatu ce kaɗai ta amsa gaisuwarshi itama a wulaƙance.
Yaya Hambali kuwa ko da Gwadabe ya miƙa mishi hannu bai karɓi hannun ba. Yaya Tasi'u dake kusa dashi yace.
"Haba Alhaji Hambali menene yayi zafi haka shi ba wuta ba. Yanzu yaronnan ba zaku sarara mishi ya samu yaci gaba da zumunci daku ba, ina laifin wanda ya gaisheka ko da bare ne balle jininka?"
Murmushi Gwadabe yayi yace.
"Ai babu komai Yaya Tasi'u. Yaya Hambali kayi haƙuri in sha Allah bazan sake ba ma" Iyakar abinda Gwadabe yace kenan. Kunsan masu kuɗi da saurin hasala sai Yaya Hambali yace.
"Mitsiyaci kar Allah yasa ka sake. Kai ni inka kuma nuna ka sanni ma bazan yafe maka ba. ÆŠan iska wanne irin baÆ™in ciki da tashin hankali ne baka sa Babala a ciki ba. Sanadiyyar baÆ™in cikinka har hawan jini saida ya kama mana uwa. Æace ka bani waje"
Bara'u ne ya É—aga Gwadabe suka koma tabarma matasa irinsu, yayi jigum yama rasa ta cewa. Yana sha'awar yaga ya shiga cikin Æ´an uwanshi ayi wasa ayi dariya tare.shin sai yaushe wannan lokacin zai zo ne? Shikenan shi bashi da damar da zai ko da gaishe da Babala ta amsa mishi, wannan rayuwa wannan tashin hankali da mi yai kamane?