← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 237

Sashe 30

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

da lodoji. Shigowarsu ke da wuya aka shigo da Gwadabe. Da Burodami Debisi aka kinkimeshi zuwa gado. "Sannu Gwadabe ya jikin, ashe abunda ya faru kenan?" Cewar Burodami Debisi. "Jiki sai godiyar Allah, Iyabo likita yace yana son ganinki" Tashi nayi na nufi ofishin likita. "Duk binciken mu ya tabbatar mana komai nashi lafiya suke. Mun yi hoto har sau biyu bamu ga komai ba. Mun sallameku inaga ku nemi na gargajiya zaifi. Ina mai baku shawarar ku sai mishi keken tuƙa marasa lafiya, yafi muku sauƙi da a dinga kinkimarshi. Ga takaddar sallama, kije ki biya Allah ya ƙara sauƙi" Sai da na share hawayena kana na amshi takaddar bance mishi komai ba na fita. Kuɗin hannuna sai da suka ƙare tas ban tsira da ko ficika ba. Burodami Debisi da Lekan su suka taimakeni wajen ɗaukar Gwadabe muka samu Taxi ta kaimu har ƙofar gida. Baban Nazifi da Yaya Harisu suna tsaye a ƙofar gida su Lekan suka zo suka shige da Gwadabe, na mara musu baya. Tunda muka dawo maƙota sukaita tururuwar shigowa gaishe da Gwadabe, su Iyaa Debisi ma sun tawo kusan dukka gidan, sun kawo abinci da dubu biyar, haka mu kaita karɓar jaje daga mutanen arziki. Babala kuwa a bakin Gude nake jin wai ta koma Takai Laila ma ta je ganin gida. Atampopi na na ɗura a buhu kab harda ma ɗinkakkun bar bari ba, kala huɗu na ware kawai, na ɗauki buhunnan na fita hankali da nutsuwata basa tare dani sam. Siyan wulaƙanci sosai akaima kayan, amman biyan buƙata yafi godon buri, Gwadabe mutum da ɓari ne a wajena. Keken ɗaukar marasa ƙafa ko tsofaffi na siyo ta hannu akan nera dubu ashirin da biyar da ɗari takwas. Ina shigowa gidan kallo ya dawo gareni, ni dai babu wanda na kalla takaina kawai nake yi. Ko Gwadabe yasha ruwan mamakin ganina da wannan wul ciya sosai. Ni dai bance uffanba na tallafeshi na sashi a kan wul ciya ɗinnan. Hawaye ya soma sharewa, ni kuma ina mishi murmushi. "Mala'ikun Allah ku shaida na sama rayuwar Iyabo albarka, kuma na ɗaga mata ƙafafuna domin ta shiga aljanna. Allah yai miki albarka ya kawo mana mafita akan jarabawar da take kanmu" Ameen Gwadabe, ka dena kuka. In sha Allah tunda ina nan kafi ƙarfin zubar da ruwan hawaye." Daga haka muka shiga suntirin bin masu magungunan gargajiya, mu ke nan kullum a tafe, amman babu canji kullum jiya e yau. Tafe tafe sai da mu ka kwashe tsawon wata uku muna abu ɗaya. Dangina da suke ɗan tallafamun suma suka gaji suka watsar. Babala sau biyu kaɗai tazo ta duba Gwadabe, amman ƴan Takai kam sun zazzo sosai. Sakina da Bara'u kam mayar da gidanmu su ka yi kamar aje kasuwa a dawo. Duk wata jigilar zuwa nemo maganin makarin sammun da akaima Gwadabe, tare da Bara'u da Sakina muke zuwa. Abincin da zamu ci Bara'u ke kawo mana. Ayashe da Tamu suma sun mana ƙoƙari sosai. Babbar damuwata ɗaya ce tak har yanzu babu wani sauƙi da aka samu." MRS BUKHARI
Chapter 30 · 0% Book details