Sashe 202
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
GWADABE:. "Me ya faru Bara'u. Wani abunne ya samu Babala kuma, amman naji kana cewa duk gari anata tsogumi?" Gwadabe yayi kasaƙe yana sauraren abinda Bara'u zaice mishi. "Laila ai ba ƙaramar matsiyaciya bace Gwadabe Allah ne kaɗai ya taimakeka ka kubce ma auren Laila fa" Gwadabe yayi dariya yace. "Yauwa nasan za'a runa ai wai an saci zanin mahaukaciya. Ta yashe Yaya Hambalin ko?" Bara'u yace. "Abun ya wuce tunaninka. Asiri tayi ta mallake Hambali Gwadabe. Laila ta dinga mulki tana iskanci. Kaga dai kab su Fudiyo Laila tasa Yaya Hambali ya koresu daga gidanshi. To sai suka garzayo suka sanarma Babala. Batai ƙasa a guiwa ba tasa su Da'u a gaba suka je Kano. Laila ta zage taci mutuncin Babala kuma tasa Yaya Hambali ya koreta ta dawo Takai. Kaji wannan? Bai tsaya iya nan ba Gwadabe tasa Yaya Hambali ya dinga ɓarnatar mata da dukiyarshi ita da Baba Iyatu. Ya dena zuwa Takai, ya dena turoma Babala abinci. Su Da'u su ba jari ba dan tasa an ƙwace komai a hannunsu. Su sun ajjiye matan anan cikin gidanku, su kuma sun bazama neman na kai. Wannan dalilinne ya kwantar da Babala a asibiti. Kai Gwadabe yaita girgizawa yana mamakin wannan lamarin" "Haula da yaranta fa su kuma?" "Wacece wata Haula anaima batun Babala? Ai ya daɗe da rabuwa da Haula, yaran dai marasa auren suna hannun ita Lailan tana gasa musu aya a hannu. Kasan dama ba mutunci bane dasu suna, Layla na koya musu hankali. Wai kai kaga Yaya Hambali yadda ya koma kafin tace? Abun yayi baƙin muni gaskiya rashin imanin yayi yawa. Gwadabe rikici fa da Babala da Baba Iyatu har gaban mai gari. Baba iyatu tayi butulci sosai bata kyauta ma Babala ba gaskiya. Duk da dai bayan faruwar abun Takai ta ɗauka duk inda ka wuce labarin akeyi. Nifa ji nayi ana cewa bata hanyar halak Yaya Hambali ya samu arziki da ɗaukakar ba, wai yana bin ƴan bori. Wallahi ance wai shima har borin yake hawa. Wannan kwalli da yake dumbuzawa a idon shi bafa na lafiya bane ashe. Kai maganganu iri da kala anata rarrabawa a Takai wallahi. Babala ko fitowa bata iyayi sabida kunya. Yaya Halima ma ta ƙare mata reshe ya juye da mujiya kishiyarta ta mallaketa sai yadda tayi da'ita. A wata ruwayar ma cewa akayi Yaya Halima har wanki take ma kishiyar tata." Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. "To Allah ya kiyaye gaba yasa wannan abun daya faru Babala ta sassautamun, ta gane dalilin da yasa naƙi auren Laila" Bara'u ya dafa Gwadabe yace. "Hmm kullum fa a sunturin bin ƙauyuka suke suma suna neman ai musu asirin da Hambali zai rabu da Laila hankalinshi kuma ya dawo jikinshi. Sannan a karya asirin da Kishiyar Yaya Halima tayi mata. Yaya Halima ta manta a shekarun baya har zane kishiyarta take yi, meye batai mata ba? Wanzami baison jarfa. Yanzu labarinnan da nake yi maka da Laila da Baba Iyatu fa suna Umara. Shi kuma Yaya Hambali an yi mishi kiran duniya dan ma a sanar mishi da halin da Babala take ciki, wallahi yaƙi ɗaga wayar fur. Aka tashi Da'u yaje Kanon ma ya kasa ganin Hambalin sam. Jiya saini da naje ne na biya musu kuɗin maganin da aka rubutama ita Babalan. To babu kuɗin komanta ya ƙare har gonarta ta siyar danta dawo da tunanin Hambali amman ina. Tai ta kuka a asibitinnan in faɗa maka. Ina asibitin ban tafi ba Yaya Halima take bata labarin an mata kwatancen wani boka zata je wai ko Allah zaisa a dace. Sai dai basu da kuɗi komansu ya ƙare. A haka dai nayi musu sallama na tafi. Ya suka ƙare oho" Shiru Gwadabe yayi yana mamakin wannan lamari. Sai yaji tausayin Babala ya kamashi abunka da uwa. Hatta su Da'u ya tausaya musu sosai. "Zan ajjiye maka ishasshen kuɗi dan Allah ka kula da komai nata. Kada ka sake kace mata nine. Abincinma zan dinga aiko maka da kuɗin duk wata a dinga siya mata" Motar Zulƙi ce tazo wucewa ganin su Bara'u ne yasa ya tsaya. Tashi suka yi suka nufeshi. "Kaga mai maganin harka Gwadabe mai maganin ɗa'a ashe kai ka shigo garin ma shine babu labari? Nama kira wayarka har sau biyu baka ɗaga ba dan akwai magana ta ƙaruwa gaskiya " Hannu Gwadabe ya bashi suka tafa sunata dariya. "Baka da dama wallahi Zulƙe." "Ai gaskiya ne. Uwargida tana ta yaba canjin da aka samu. Duk manyan mutanen dana haɗaka fa dasu sunata son magani na ba wasu numbarka jiya dan mun yi meeting ne shigowata garin kenan. Gashi dama ko bamu haɗu ba na kiraka a waya dan mu tattauna muhimmiyar magana ne." Gwadabe yace. "Bazai gagaraba. Zuwa gobe da safe zamu shigo kaga maci masa ma mu more. Nima ko awa ɗaya banyi da shigowa garin ba" "To Shikenan hakanma yayi. Bara'u sai kun shigo zan jiraku" Nan su kai sallama, Gwadabe ya samu ya shiga wajen Sakina suna cikin ɗaki suna zazzaune. Hadiza na gefe guda a takure tana cin tuwo. Shafa ma tana nata gefen tana cin nata tuwon. Sakina kuma tana bama jaririyarta nono, sai yara daketa shirmensu dai. Suna ganin Gwadabe suka isa a guje da oyoyo. Tsugunnawa yayi duk suka dafashi ya kalli Toye da su Kahinde yaga yadda suka yi baƙi suka rame, ga ƙuraje bajaja a jikinsu. Kai ya girgiza kawai yana jimantawa Iyabo. "A_a kaga Tsuntsun soyayya maraba da zuwanku. Sai yanzu ka shigo, Bara'u baka shigo dashi yaci tuwon ba" Bara'u yace. "Wanne tuwo ana zaune lafiya. Bari a karɓo kaza mana, ki haɗa musu tea kafin mu dawo. Kaga tsuntsun soyayya kake ko? Tawo muje" Da Sakina da Shafa sunata musu dariya. Hadiza kuwa ta mugun takure kanta. Ko dariyar ma ta kasa yi. Duk yadda Sakina taso tasa Hadiza ta sake amman taƙi fur. A hanyar dawowarsu daga siyo kazane Bara'u ya shiga ba Gwadabe labarin Iyabo. "Kai in kaga irin ƙauyen da tsuntsun soyayya take rayuwa in dai kai kaje nasan ba zaka iya bacci ba Gwadabe. Nifa kaina ranar kasa bacci nayi inata tubkewa da warwarewa. Amman shi sha'anin aure ƙaddarane zallah a cikinshi. Gashi ta haifi yaranta ƴan biyu kyawawa baka gansu ba. Mijin ma baya nan ya tafi kiwon shanu. Amman taji daɗin saƙon dana kai mata nace in jika tayi murmushi ta karɓa tayi godiya. Yaran dana koma ɗakkosu tayi musu tsaraba sosai harda matanka taima tsaraba kuma tace ai musu ma godiya bisa riƙon yara da suke yi. Ni dai lamarin ya dameni gaskiya " Murmmusawa Gwadabe yayi yana goye da hannayenshi a bayanshi yace. "Soyayya ce nayi imanin yake riƙe da Iyabo a wannan Rugga nayi imanin hakan. Nasan Iyabo sama da sanin da taima kanta ita kanta. Fatana shine Allah yasa mijinta yana riƙeta da kyau dan ya more mace, ba fishi, ba ƙorafi, ba hayaniya, ba rainuwa, ita dai kamar ba jinin yarbawaba. Gashi dangin mahaifinta mugayen jarababbune. Allah sarki Iyabo tsuntsun soyayya ƴar a mutu ma soyayya kenan." Dariya Bara'u yayi yace. "Taga ɗan fulani siriri mai siririn hanci fari mai gashi a kwance, ba irin naka gashin duk ƙuda ba" Naushi Gwadabe ya kaima Bara'u yayi saurin kaucewa ya naushi iska. Har suka shiga gida Bara'u na ma Gwadabe dariyar mugunta. Shiko ya mugun haɗe ranshi sai tura tumbinshi yake yi. Kajinnan Sakina ta raba, ta cira ma yara nasu harma sunyi baccinsu ajjiye musu tayi da safe saci. Ta cirama Gwadabe da matanshi, ta cire nata da mijinta. Suna cin kaza suna hirarsu. Sakina ta shiga ciki ta ɗebo tsarabar da Iyabo taima yara ta dure a gaban Gwadabe. "Ga kayannan Gwadabe gara dai ku gani sai kaba matanka su adana a jakarsu, gidan gobe zai haɗa jama'a." Hadiza ta dubi kayan ta haɗiye tsokar da tasa a bakinta ba bare data tauna ba dan baƙin ciki. Bara'u yace. "Wannan atampopin na matanka ne tace a basu. Wannan kuma na yaranne, wannan tace a ɗinka ma takwararta, a goyata dashi. Taji daɗin ganin hoton takwararta fiye da yanda kakr tunani. Taba Sakina nata daban. Nono dai mun shanye, amman akwai soyayyen man shanu da yawa naku na ajjiye. Kaji, ko zabuwane nasa anyi mana miya mun cinye" Gwadabe yayi shiru kome yake tunani oho. Can ya nisa yace. "Allah ya saka mata da mafificin alkhairi. Ku kunji ga fa kaya Iyabo ta aiko muku dashi." Ya dubesu yana karantar yanayinsu. Shafa cikin fara,a tace. "Mungode Allah ya saka da Alkhairi . Takwararta tana godiya. A gaskiya Mamansu Toye tana da kirki da sanin mutuncin mutane. Dole ma ta tsaya aran uban ƴaƴanta gaskiya. Mu bamu iya bata tsarababa ita ta aiko mana dashi. Madallah da Iyabo mutuniyar kirki" Gwadabe take yaji matsayi da soyayyar Shafa ta nunku a zuchiyarshi. Idanu ya lumshe kawai baice komai ba. Hadiza dai sai cin kazarta take yi ko tari batai ba. Bara'u daya lura da hakan sai ya soko ma Gwadabe batun noma" Gwadabe yaba matanshi umarnin bama Sakina gudunmawarsu tun yanzu dan da safe kacamewa gidan zaiyi da mata. Sakina tayi godiya sosai. Nan suka tashi tare dayi musu sallama a ɗakin zaure suka kwana. Gwadabe da ƙyar bacci ya sureshi. Damuwar Iyabo ta addabeshi. Da kuma tunanin irin rashin kyautawar Laila ga Babala duk irin soyayyar da Babala ta nuna mata ita da mahaifiyarta sakamakonta a wajensu kenan? Wani ɓangare na zuchiyarshi yace dashi. "Tsuntsun da yaja ruwa ai shi ruwa kan doka. Ba dai ita take son rufama Laila asiri ba. Ita gashi ta bankaɗa asirinta ai" Da waɗannan tunane_tunanen bacci ya ɗebeshi" Washegari . Aka wayi gari da hada_hadar suna. Mata na ciki suna hidima, su Bara'u na waje suna kiciniyar yanka tunkiyar suna. Ƙanin Bara'u suka bari da ragowar aiki suka nufi gidan Zulƙi dan dukkansu a matse suke da son jin menene Zulƙi yake son ya tattauna da Gwadabe. A falon baƙi suka yada zanzo, aka cika musu gabansu da kayan ciye_ciye da kayan tea. Yau Zulƙi bai ɗauki lokaci ba sai gashi ya fito daga ciki da ƴarshi ƙarama a kafaɗarshi mai shan Nono" "Gwadabe mai maganin harka. An gaisheka likitan maza" Bara'u ya durƙusa ya dinga sheƙa dariya. Da Gwadabe da Zulƙi ma