← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 235 OF 237

Sashe 235

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

IYABO:.
Tare Uwani da Dr suka shigo. Bayan Dr ta gama dubani ta fita Uwani ta soma bama Hajja Mama labarin matsayar da aka tsaida lamarinnan. Ni dai sai cikina ya zuge zawo duk minti biyar sai na faÉ—a banÉ—aki.
Mijin Uwani da kishiyarta ne suka zo yi mana sallama.
A hankali na fita falon na zauna a waje guda muka gaisa cike da girmamawa a mutunce. Su kai mun barka da dawowata cikin hayyacina tare da adda'ar Allah ya kare gaba.
"To mu Hajiya jirginmu zai É—aga ke sai yaushe kenan zamu saka rai dake?"
Uwani tayi dariya tace.
"Ranka shi daÉ—e ni nan ai sai naga abinda ya ture ma buzu naÉ—i, zan zauna da'ita har zuwa a gama komai in sha Allah sai in dawo"
"To ai Shikenan. Amman yaran shago sun kiraki kuwa, ruwa ya shigar miki shago yayi ɓarna sosai gaskiya. Amman nace su kai kayan da ruwa ya taɓa gida a wanke a shanya dai. Na kuma tura musu masu gyara su gyara inda ruwan ya shiga"
"Assha to Allah yasa da abinda ya tare. Basu ko kirani ba gaskiya"
Ni dai nan nayi musu Allah ya tsare hanya na sa kai na koma ciki.
"Iyabo bari in shiga cikin gidan mu gaggaisa tukunna. Wai ni kam kishiyoyinki me suka É—auki duniya ne sunfa fito lokacin da kika faÉ—i a can tsakar gidan fa. Amman banga sun zo dubaki ba, su Sumayya mun musu uziri su mutuwa akayi musu."
Ohon musu Hajja ai babu komai duniyarma nawa take. Wallahi Allah gabaki É—aya komai na cikin duniyarnan ya isheni ya isheni.
Kafin Hajja Mama ta bani amsa Anty Sumayya ta shigo da sallama tare da cewa.
"Imanine yadda da ƙaddara me kyau ko akasin hakan Iyabo. Na sani al'amarinnan babbane sosai, amman ki godema Allah daya dawo dake cikin nutsuwarki zaki ga danginki, ki ga mahaifanki me yafi wannan daɗi ko babu komai yaranki zasu ga mahaifinsu. Ki sani dan suna amfani da sunan Usman duk daren daɗewa za'a samu ko a family da wasu zasu tsokata musu cewar Usman ba mahaifinsu bane. Ko ba'a tsokata musu ba ranar da Usman ya faɗi ya mutu a ranar zasu yi kuka dan dole a fayyace musu gaskiya da gaskiya. Hakan ma ban yi tunanin zai kai tsawon haka ba, nayi imani da a Gombe kuka zauna tare da kishiyoyinki ko su Abida zasu goranta ma yarannan. In ma ba sui ba iyayensu zasu yi. Kinga sai ki shiga tashin hankali dan ko yankaki za'ayi ba zaki ce ga ubansu ba, mu kuma zuchiyarmu a lokacin zata shiga wasi_wasin shi yarsn ma na sunnah ne. Ke komai kika ga ya faru akwai hikma a tattare da faruwar. Ki yi haquri daga ke har Usman din. Shima yana cikin mummunan halin da tunda nake ban taɓa ganinshi a ciki ba."
Nasiha da ban baki kawai ake ta yi mun. Sai nayi kamar na samu nutsuwa dana ga shige da ficen yara sai damuwa ta sake aurena.
Sai zuwa yamma akaita cincirindon zuwa gaisheni tare da gulmace gulmace a madadin su tausaya mana sai abun ya zama wani iri kuma. Suhailat kuwa sai cemun tayi.
"Ashe komai yazo ƙarshe kuma, hankalinki ya dawo jikinki an gano kina da aure. Ƙila ma kina sane dokiya kika zo ci, to dubu ta cika".
Uwani ta dubeta tace.
"E yadda kika faÉ—a haka É—inne baiwar Allah. Sai dai mu gode ma Allah daya nuna mana wannan lokaci kuma. Dukiya kuma ai tari da ta handami iyakar handamarta karfa ki mance Iyabo itace da miji, ko ya baku labarin adadin gidajen da ya sai mata ita da yaranta kuwa?""
Bata dai kula Uwani ba ta fice. A zafafe dan maganar Uwani ta daketa sosai. Duk da bata san Usman akan rashin adalci ba, akan Iyabo sai take ganin zai iya komai ma akace yayi. Yaranshi basu sami damar karatu a waje ba sai Æ´aÆ´an Iyabo harda agololi.
Uwani har yanzu kina nan da halinki"
"Me kike ganin za'a fasa Iyabo. Ya zata zo tana faɗa mana magana. Ke dai kullum a haka zaki ƙare ƴar iska.
Dole Uwani sai da tasa na dara.
Wannan daren cike na kwana da zulumi gami da taraddadi har garin Allah ya waye.
Sukuku nak, gabana kuwa dama shi tunda na dawo hayyacina yake faÉ—uwa.
Ƙarfe biyun rana su Debisi suka iso. Amman Alhaji Usman ya ajjiyesu a can cikin gida ana jiran isowar su Hamma. Su kam sai dab magriba Allah yayi musu karasowa bayan an idar da sallah Alhaji Usman ya shigo da sallama. Ina ganinshi na saki kuka.
"Uwani Hajja Mama kuje falo baƙinmu sun hallara. Inaso zan gana da Iyabo"
Nan suka fice suka bamu waje. Zama yayi a kusa dani yayi shiru sai ajjiyar zuchiya yake yi. Cikin wata murya mai kauri yace.
"Wannan ƙaddarar da girma take. Allah ya bamu dangana baki ɗayanmu Iyabo. Amman me yasa kika boye mun halin da kika samu kanki kuka haɗa baki da Hajja Mama tace ke ƴar ƙanwartace ashe a gari ta tsintoki?"
Muuryata da bakina yana rawa na bashi labarin yadda mu ka yi da Hajja Mama.
Sonka ne ya rufe mun idanuna shi yasa har na amince dan gudun a faÉ—a maka gaskiya ka fasa aurena. Wallahi babu wani nufi mara kyau a tattare dani ka yarda dani wallahi Usman ina sonka so mai tsanani"
Murmushi yayi mun idanunshi cike da hawaye yace.
"Ni ko nasan kina sona,amman ai dawowarki hayyacinki tuni ya ture gwamnatina dan Uwani ta bani labarin soyayyarki da Hamma. Ashe kyakkyawane haka shi yasa Æ´an biyu suka fito kamar larabawa."
Usman... Na ja sunan nashi yayi maza ya runtse idanunshi.
"A_a Iyabo kar ki mun wata kalmar soyayya. Ina neman alfarmarki dan Allah in aurena dake ya ƙare kiji tsoron Allah ki cire ni cak a zuchiyarki kar ki sake ki zauna kiyi tunanina. Sannan zan sake roƙon wata alfarma duk da ba lallai bane in samu ba kuma baki da ikon yanke hukunci ke kaɗai Iyabo in na rasaki na rasa su Hassan zan shiga damuwa mai tarin yawa. Duk da a tunanina ke kike da zaɓi a kanmu ko ni ko Hamma. Nayi imanin in dai hakanne dole ni zaki ɗauka ba Hamma ba, ki rayu tare damu iyabona cinyar sa maganin mai haɗama ki zaɓeni kar ki ga Hamma ki juya mun baya. Zaki mun illa. Inason su Hassan ina son su wallahi...
Na baka su har abada Usman babu wanda ya isa rabaka dasu. Yanzu Usman aurenmu rabawa za'ayi kenan? In dai zabi aka bani na shiga ukuna ya zanyi da rayuwata wa zan É—auka wa zan ajjiye to"
Na fashe da kuka. Mun daÉ—e a haka sosai har sai da Uwani ta shigo ganin halin da muke ciki sai hankalinta ya tashi.
"Kuyi haƙuri dan Allah. Usman ku fito muje"
Ficewa yayi fuu. Uwani tazo ta É—agani muka fito falon
Tsarki ya tabbata ga Allah mai kowa mai komai
Da Yaya Hamma na soma haɗa idanu, na ganshi ya goge sosai ya zama ɗan birni sai dai ramarshi data ƙaru da ɗan duhu da yayi. Ga Baɗɗo, ga Amaduyal, ga Yafendo A'i. Ta ɓangarensu Burodami Debisi kuwa. anty Ramata, Burodami Kokodeen, Burodami Debisi, da Iyaa Beji ne suka tawo. In taka in isa gabansu ni dai na kasa. Hamma ne kaɗai ya miƙe ya iso gareni ya tsaya a gabana.
Usman ya hadiye yawu tare da yin gyaran murya.
Baɗɗo ce ta ƙaraso muka rungume junanmu sai kuka, ɗakin ya cika da koke koken mata a haka su Hassan Anty Sumayya ta shigo dasu.
Nan kallo ya koma garesu tsugunnawa Hamma yayi yasa goshinshi a ƙasa yayi sujjadar godiya ga Allah daya nuna mishi wannan rana.

Zan barku anan kuka yaci ƙarfina

A tunanin ku auren waye dahir a kan Iyabo ne?
Shin zaɓin za'a bata kamar yadda Usman yake fara da buri?
To wa Iyabo zata zaɓa a tsakanin Usman da Hamma. Yaranta uku da Usman, yaranta biyu da Hamma.
Usman yayi mata so zallah, ya inganta rayuwarta da rayuwar yaranta, tayi rayuwar farin ciki tare dashi.
Hamma ya sota a baya ya sai da shanu har biyu domin farin cikin Iyabo, wanda a wajen bafullace babu abinda ya kai shanu daraja, kuma shekara sha bakwai yana zaune yaƙi aure sabida Alaja Iyabo, bugu da ƙari gashi ɗan uwanta na jini.
Shin wa zata É—auka wa zata bari?
MRS BUKHARI

**Anty Ramlex Me kayan Da'a,ingantattu,fitattu,kuma shahararru*
Na zo muku da albishir na Promo Promo Promo💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽

Abun da kuka Dade Kuna nema....,hakika dogon Jira ya kare.....Ga abunda kuke bege gaba gare ku💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽ba sai kunyi godiya ba menene amfanin zaman tare😌🤫😉

Ina Uwargida me son sabunta martabarta a wurin Oga,Ina amaren bana masu son su mallaki zuciyar ango,Ina zawarawa da suka shirya gyaran abun cikin buje,domin farfado da mutuntakarsu........ku matso kusa......

Hajiya ta sauke farashi,me kike jira........

Babban set na promo
~#20k~#15k👌🏼
🎯 _dambun zabuwa
🎯tsumin bugenta shakaf
🎯Gumbar Madara me Sanya megida Santi da dalalar yawu
🎯Hadin dabino da cukwui hadin basarakiya
🎯Tsugunno me sirri_

*Karamin set*~#15k~#10k💃🏽
📯Herbal for vaginal infection
📯Tsimin bujenta shakaf
📯Gumbar Madara da hadin dabino.
📯Hadin dabino da cukwui (manta uwa)
📯Tsugunno me sirri

🚚Muna aika kaya ko Ina a fadin Nigeria da kewaye.
📞Ku tuntubeni a wnn numbern 07069722234
Anty Ramlex taku ce🥰
NAMA YA DAHU....
ROMO ƊAÑYE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA HUÆŠU

19

DA SADAUKAR DA WANNAN SHAFIN GAREKA MIJINA ABIN ALFAHARI MASOYI MAI KAMA DA ZUMA. BUKHARI IBRAHIM LADAN.
Chapter 235 · 0% Book details