← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 237

Sashe 70

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Gwadabe.
Ana gobe Gwadabe zai kama hanyar Najeriya. Sun sha hira ainun da Hadiza da ƙyar ta barshi ya samu ya shiga ciki yaci gaba da shirya kayan tafiya. Kishine ɗamfare a ƙirjin Hadiza dan ita gabaki ɗaya a tunaninta Gwadabe baibai kawai ya ninketa amman wajen Shafa yake son zuwa. Shadda dalleliya da ƴan kunne Hadiza ta bayar a kaima Babala, ta bada agogo mai kyau tace ya kaima Shafa. Anty Badi'a kuma ta ba da takalmi da mayafi tace akaima Babala. Yaya Tasi'u kuma kuɗi ya bayar akai mata, sai ƙarin guziri da yaba Gwadabe. Sassafe kuwa Mammada ya rakashi tashar mota. Motarsu ta ɗaga zuwa Najeriya. A garin Kano ta dabo tumbin giwa Gwadabe ya sauka. Misalin ƙarfe tara na dare dake motarsu ta samu matsala a hanya sun daɗe a yashe a titi sosai.
Sakkowarshi daga mota ita ta kara mishi damuwar rasa Iyabo da yayi a rayuwarshi. Gashi dare yayi, kuma bazai taɓa iya taka kafarshi zuwa gidan Yaya Hambali ba. Bashi da zaɓin daya wuce ya nemi gidan kwana a tasha, gobe sassafe yana son ya leƙa gidansu Iyabo ko Allah zai yi ko juna su gani, su gaisa kafin ya tafi.
"Malam muna da ɗakin saukar baƙi in kana da buƙata. In kuma a Kano tafiyarka ta ƙare akwai tasi da Bus a bakin tasha zata kai ka duk inda kake buƙata. Cewar wani ɗan yuniyon.
"Inada buƙatar ɗakin, Takai zan wuce zuwa gobe da safe dan Allah"
"Nera hamsin kuÉ—in kwana, in bawali zaka yi a banÉ—aki kuma nera biyar, ba haya nera goma, wanka nera ashirin, ruwan zafi ma ashirin." Wani É—an yuniyon dinne yace.
"Haruna ka fiye surutu, ka É—auki jakarshi dallah ka rakashi masauki" Wanda aka kira Haruna ya tuntsure da dariya yace.
"Ai gara muyi gwari_gwari dai." Jakar kayan Gwadabe ya saɓa a bayanshi yace.
"Biyoni muje in kai ka" A baya Gwadabe ya bishi zuwa can cikin tashar, wani gida mai kama dana masu zaman banza suka shiga. Maza da mata, da ƴan daudu ne a cakuɗe suna caca, masu ƙidan garaya kuma sai kiɗa suke yi, ga masu shan tabar sigari, ga masu cin goro da tomtom kowa dai da abinda yakeyi. Ƙyauran wani ɗaki Haruna ya buɗe suka shiga. Matasane a ciki fin su takwas, wasu sunyi bacci, wasu na bacci, wasu abinci suke ci. Tabarmace malala a ɗakin, sai kayi matashin kai da buhun kayanka. Gwadabe bai gama ƙarema dakin kallo ba Haruna ya miƙo mishi hannunshi. Nera hamsin ya bashi.
"To ka raɓa ta can lungun ka kwanta. Kana buƙatar abinci ne?'
"E ina buƙata, amman tuwo nake so" Haruna yace.
"Tuwo miyar kukace kaɗai tayi ragowa. Ko wacce malmala nera ashirin ce, nama kuma ko wanne tsoka nera goma, man shanu ko wanne cokali nera biyar" Dariya Gwadabe yayi, duk da damuwar da yake ciki. Shima harunan dariya yayi. Nera ɗari ya miƙa mishi.
"To a haÉ—a komai da komai na É—ari harda ruwan sha"
Zaman Gwadabe ke da wuya sai ga kiran wayar Shafa.
"Assalamu alaikum Shafa barka da dare, har izuwa irin wannan lokacin baki yi bacci ba?" Ɗan murmusawa tayi, cikin taushi da zaƙin murya tace.
"Na kasa baccin inata jiran kiranka kace mun ka isa Takai in samu nutsuwar ruhi tukunna. Jin shiru ne yasa nace dai bari in nemeka"
ÆŠan murmushin wahala yayi mata yace.
"Ayya. Kin ganni a Kano bamu daÉ—e da shigowa ba ma. Sai zuwa gobe in Allah ya kaimu zan karasa takai É—in." Iska ta fesar daga bakinta.
"To Allah ya nuna mana. Bari in barka ka samu ka huta, zuwa safiya in ka isa Takai mayi waya" Bai bata amsaba ƙit wayar ta ɗauke chaji ya ƙare, a ajjihu ya wurga wayar ya samu ya gyara zaman ƙatuwar jakar buhunshi. Wata budurwace ta shigo mishi da tuwo. Bayan ya gama ci kuma sai yayi jigum a zaune yanata faman tunanin yadda za'ayi gobe kafin tafiyarshi yaga Iyabo ko da basu yi magana ba. Wata zuchiyar tace dashi."ƙila ma tana can gidan mijinta ta mance dakai" take gabanshi ya tattake ya faɗi. Da wannan zulumin ya kwana. Sassafe bayan sallar asuba ya fice a tashar bayan yaba Haruna ajjiyar jakar kayanshi. Kai tsaye motar layin su Iyabo ya shiga. Tun daga hango gidan damuwarshi ta sake yin tsanani, bugun zuchiyarshi yaci gaba da ƙarfi. Iyaa Debisi ya hango tana ma yara masu kawo niƙa niƙan wani abu haka kamar gero, kamar dawa. Yana isa wajen ta kalleshi ta zuba mishi harara harda tsaƙi, ta mayar da hankali a kan niƙanta. Shi ko ƙiƙam yayi yana jiran ta kashe injin ɗin su gaisa. Amman bayan fa gaisuwar baisan me zai soma cewa ba. Ya

NAMA YA DAHU....
ROMO ÆŠANYE
BOOK 2

6
Chapter 70 · 0% Book details