← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 237

Sashe 54

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da dukkan halama shi suke jira su ci abinci, dan tun zuwansu suke cin abinci a tare. Hadiza, da Ine suma abincin suke cii daga can kusa da gadonsu na bono. "Yaya Gwadabe ya aikin?" Cewar Ine kenan. Sai da ya gaishe da Baba Fhatsima kana ya amsa Ine. Hadiza ta kalleshi da murmushi a fuskarta tace. "Yaya Gwadabe da safe naje nemanka ɓarayinku ban sameku ba yau kun fita da wuri ko?" "Sa hannu Malam muna ci kana amsa musu tambayoyinsu. In wanna yaranne sai mu kai sha ɗayan dare ba mu ci abinci ba" Dariya duka suka yi, dan Auwala baya wasa da harkar cin abinci. Baba Fhatsima tace. "Ato da gaskiyarshi ai. Maza kuci ku samu ku yi wanka sai ku kwanta. Allah dai ya sama nema albarka." Suna cin abincin ana hira baki ɗayansu a haka dai suka ƙare cin abincin. Sai ga Yaya Tasi'u ya shigo. "Kuna nan ba? Anzo a cinye ma Baba ɗan naman nata ba? Baba Yarannan ya kamata a matso da maganar aurensu, a samu suma su mallaki iyalansu, su dena zuwa suna cinye miki kayan daɗi" Ɗan darawa su ka yi, duk suka miƙe suka gaggaisa, Yaya Tasi'u yace. "Gwadabe ya ciwon jikin? Mammada ya faɗa mun ranar daka shiga rijiyar haƙon zinariya kasa bacci kayi, jikinka yaita ciwo?" Kai Gwadabe ya sosa yace. "Wallahu Yaya Tasi'u ai naji jiki sosai. Amman dai yanzu ina ɗan taɓa aikin, ciwon jikin yana ja baya" "E dama a hankali zai bi jikinka. Kama yi ƙoƙari ni naga jarumtarka sosai, dan wannan aikin bana malalata bane." Baba Fhatsima tace. "Ni kaina na ga juriyarshi sosai. Allah yayi muku albarka dukanku Allah ya baku abinda kuke nema duniya da lahira" Da "Ameen" Suka amsa dukkansu. Hadiza tace. "Yaya maganar kuɗin angon baka bamu ba, kar mu rasa ɗinkin" tsaki Yaya Tasi'u yayi yace. "Ana maganar kayan gado dasu katifa yayi kuɗi. Ku ta ango ma kuke yi ko? To kuje dai wajen Antynku Badi'a zata baku atampopin ta siya muku, dan ni ban bata ko sisi ba. Kunga ni an hutasheni, sai in yima Mamana" Nan suka yi mishi godiya. Baba Fhatsima tace "Ai Babannan ( haka Take kiranshi, kasancewarshi ɗan fari kuma mai sunan Mahaifinta) Babu abunda zamu ce da Badi'a sai dai muce Allah ya saka mata da Alkhairi. Tana yi mun abinda ko su Hadiza iyaka kenan. Yarinyace adala. Ina ma su Auwala fatan Allah yasa yaran da zasu auro mana su kasance masu hankali. Sai kaga zumunci ya sake ƙarfi sosai. Kuma naji daɗin yadda Malam ya yanke hukuncin ware su wadannan yaran a gida daban. Ƙila suma kansu su Sabitu su daure ayi zumuncin duka tare da matansu. Kuma kuyi ƙoƙarin haɗe kawunan yaranku waje guda, kar ku sake a raba muku kan yara. Ni bana jin daɗin irin yanda kowa yake jaye ɗanshi jikinshi kaɗai." Auwala yace. "Tabb ni kuma Baba gani nake yi wannan haɗemu da za'yi waje guda ba zai haifar da ɗa mai ido ba. Sabitu da baya ko iya gaishe da mutane cikin daɗin rai. In fa zai gaishemu kamar zai haɗiyi zuchiya haka yake yi, dan ƙaniyarshi dan yasan kashi zan bashi in baiyi gaisuwar bane. Ni wallahi bana son wannn haɗemun da za'ayi" Yaya Tasi'u yace. "Gaskiya ne za'a iya samun rikici sosai, musamman dag ɓangaren su matan da za'a auro bare. Mun tattauna da Malam sosai akan matalolin da ka iya faruwa. Mum kuma yi magana akan irin nasarorin da zasu iya faruwa. Dan a wannan karon Malam ya shirya ɓatawa da duk wanda ya nemi ƙetare umarnin abinda zai gindaya. I zuwa yanzu ya kamata ace an watsar da duk abinda ya shige, a fuskanci rayuwa. Malam bashi da wani buri daya wuce yaga kan iyakanshi a haɗe. To matsalar Baba Asshi itace zata fi kawo matsala acikin lamarin. Amman Baba shi fa malam so yake filin Ɗan Abhuja dake jikin filin da malam ya bayar a gina, ya siya a faɗaɗa harni da Usman, da Jamilu duk mu koma can, sai ya ware ku kuma daban, muma daban. Ni a matsayina na babba sai in kula dasu baki ɗaya" Cikin damuwa da tunanin rashin yiyuwar haɗin kai ga iyalan Malam Baba Fhatsima tace. "Tab aikin da Malam ya ɗebo babbane sosai. Kuma abun zai yi matuƙar wahala asamu abinda akeso. Sai dai zamui ta adda'a kamar yadda muka kwashe shekaru sama da hamsin muna yi. Malam ya matsantama kanshi da damuwa, da tunanin abinda zai dawo mishi da farin ciki da haɗin kan iyalinshi. Akan ɗan wani dalilin da bai kai an kirashi dalili ba duk wannan abun yaketa faruwa, har waɗanda aka auro a baya_baya suma suka shigo da nasu fitinar. Amman in sha Allah komai zai zo ƙarshe a kwana a tashi" Sun jima sosai anata tattaunawa sai kusan sha ɗaya su kai sallama da Baba Fhatsima, su Auwala suka nufi shashensu, Yaya Tasi'u ma ya nufi nashi ɓarayin. A daren wannan rana Gwadabe ya kasa runtsawa, duk da tarin gajiyar wahalar aikin daya kwaso. Kwakwalwarshi sai hasko mishi hotunan ƴan matan gidan kawai take yi. Da wannan tunani ya wayi safiya, suna kan shirin fita Hadiza ta kawo musu abincin karin kumallo. Kunu ne a jug, sai ɗunamen tuwon ɓula da lafiyayyar miyar kuɓewa ɗanya. Da idanu Gwadabe ya bita bayan ta gaishesu tana shirin ficewa. "Hadiza" Auwala ya kirayi sunanta hakan yasa ta dawo cikin ɗakin. Komanta da sanyi take yi, kuma yanayinta na nuna halamar kunya tsantsa. "Ga kayanmu kala bibbiyu ki wanke mana, Gwadabe bata kuɗin sabulu, ko kai ko Mammada" Gwadabe ne ya zaro sefa ya miƙa mata, tasa hannu ta amsa. Auwala kuma ya bata kayan nasu daya cusa a cikin wando ɗaya. Kafin su dawo Hadiza ta wanke musu kayannan tas, harma ta yi musu kwalima ta haɗa da zannuwan katifunsu du ta wanke. Dama su kan yi ma yayyen nasu hakan lokaci zuwa lokaci. Wanki dama suke yi musu kasancewar su basu da lokacin kansu. Yau samarin gidan a mugun gajiye suka shigo sharkab_sharkab da zufa, hakanne ma yasa basu shigarma Baba Fhatsima ɗaki a haka ba suka nufi shashensu. Anan suka tarar da sabitu yana kutuntumama Hadiza zagi tare da faɗin kalma marar daɗi a kanta. "Ƴar iska dama naji labarin ƙazamin kishine irinna gado yasa aka sakoki ai. Dama yaushe zaku iya zaman aure, yara an sangartaku, an ɗaure muku ƙugu, an ɗauraku akan bigiren kishi" Karab a kunnen su Gwadabe. Sabitu na ganinsu yazo da sauri zai wuce, Auwala yayi zafin naman riko hannunshi ya fincikoshi ya dawo gabanshi. "Ai ba ka zazzageta ka tafi a kyauta ba. Dan Allah sai munje gaban Malam yaji duk abinda ya haɗaku har ka zaɓi cin zarafin mahaifiyarmu da shi kanshi Malam ɗin. Kai dai Sabitu baka ƙaunar buɗe idanu ka ga muna rayuwa kyakkyawa. Wannan ciwon hassadar ne ya hanaka ci gaba sam, kuma gashi munfi ƙarfinka nesa ba kusa ba. Hadiza wuce muje gaban Malam. Da ƙarfin damtse Auwala ya figi Sabitu suka ratso tsakar gidan iyayen nasu, duk suna baje a tsakar gida suna shan iska. Baba Asshi taga Auwala riƙe cab da Sabitu, ba shiri ta cire hannunta a cikin abincin da take ci ta bi bayansu har da gudunta, daga ita sai fallen zani babu ko ɗan dires a jikinta. Baba Fhatsima ganin harda Hadiza aka fita yasa itama ta miƙe ta rufa musu baya."
Chapter 54 · 0% Book details