← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 237 OF 237

Sashe 237

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFIN GA DUK ÆŠAUKACIN MASOYANA

IYABO

Gaga_gaga
Rayuwa taci gaba da shurawa, ina zaune gani ga Dadana ina idda, ganina tare da,ita ya sata farin ciki mai girma.
Bayan kwana hudu da zuwanmu Uwani ta shirya ta ta koma gida. Tafiyar Uwani da sati biyu Alhaji Usman ya turo aka zo aka tafi da su Hassan, ina hawaye na rabu da yaran bayan nayi musu nasiha mai ratsa jiki, kuma na koresu da su dinga kiran Hamma a waya suna gaisheshi kamar yadda zasu kirani. Gwadabe ma ya turo aka ɗaukar mishi yara Bara'u. Hamma kuma ya tafi Sokoto yana ta shirya gida dan tarewata, ni kuma ta nawa ɓangaren inata rarrashin Dada ta bini muje. Amman wallahi tsohuwarnan tace in barta ta mutu a mahaifarta zaifi mata. Su Yafendo ma suka ce bazan ɗauketa ba dole haka na haƙura, sai dai na zage na kashe kuɗi na zuba mata kayan alatu, na jibge mata kayan abinci masu yawan gaske.
Ana saura sati biyu in fita idda na tambayi Yaya Hamma inaso zan shiga Kano zan yi siyayya. A lokacin ya dawo jaɓɓi lamba yayi sati biyu ya sake komawa Sokoto.
Ranar lahadi Uwani na zaune a falonta sai taji sallamata ni da ummi ƙanwarta. Da su Nana
"Iyabo kece da daddare haka da yarana? Allah sarki ashe wannan lokacin zai dawo Iyabo lokacin da zaki ci gaba da ziyartata?"
Uwani ta balbalin duniya. Lallai kin samu duniya sosai irin wannan daula da kika miƙe ƙafarki a ciki haka?"
Hannu ta ban muka tafa. Kafin na nemi waje na zauna.
Kin ganni na shigo siyayya saura sati biyu in fita idda. Uwani amma ina cikin matsala damuwa tayi mun yawa shi kanshi Hamma ya rasa gane kaina. Dan ko jiya sai da ya tambayeni anya kuwa har yanzu ina sonshi.
Soyayya ɗaya ce kuma Hamma nake yima. Amman tausayin Alhaji Usman yayi yawa a zuchiyata. Uwani bawan Allahnnan ya nuna mun ƙauna ya kula dani kamar ƙwai. Wannan kyautatawar tashi itace take hanani sakewa da Yaya Hamma kuma abun sai in dinga ganinshi wani iri. ( Ba kowa ne zai gane halin da nake ciki ba, sai wanda makamancin haka ta taɓa faruwa dashi, ko kuma wani nashi)
Hawayene suka zubo mun. Uwani tace.
"Allah ya kyauta Iyabo. Amma ki sani ya zame miki dole ki dena wannan kuka hakanan da wannan damuwar dan bata da rana.
Sannan kuma abune mai wuya ki iya goge rayuwarki a gidan Usman a zuchiyarki ki yawaita ambaton Allah ki yawaita yi mishi adda'a sai kiga kin samu salama. Yau zamu kwana muna hira kenan hirar yaushe gamo tunda yanzu mun nutsa"
Bayan mun yi sallah munci abinci ummi har ta tafi muna kwance a gado. Uwani na bani labari nima ina bata labari. Labari har ya zagayo take tsokatamun ai gwadabe gashi_gashi ya riƙe kujera, yanzu haka suna kasuwancin magani shi da Bara'u. Wannan labarinne yasa ni kuwa nace gobe mu shirya muje Takai ɗin in je in dubo yara, in ga matan Gwadabe kuma"
Washegari na ɗauki ado na ɗauko sutura mai tsada na saka ga gwal ga komai. Nike tuƙa motar Uwani har Takai. Uwani ta cire waya ta kira Gwadabe ta sanar mishi da zuwanmu.
Nan da nan sai gashi ya zo ya taremu.
"Iko sai Allah tsuntsun soyayya yau kune a Takai. Allahu Akbar"
Cewar Bara'u ba sai naji zanyi kuka ba, da ƙyar na mai da kukan, tuno yadda muke zuwa Takai ni da Gwadabe hajaran majaran, da irin wulaƙancin dana fuskanta a Takai, sai na saki murmushi dana tuno Babala. GWADABE kuwa ya kasa magana sai kallo.
Motar Gwadabe na gaba ina bin bayanshi har cikin gidanshi.
Suna tafe muna binsu har cikin babban falon gidan Gwadaben. Ai kuwa yaran duk sunana, wasu na falon wasu basa cikin falon. Su Kayinde suka zuba mun idanu, da suka gane nice sai suka nufo ni a guje suna ambaton umma, umma"
Zama mu ka yi, Gwadabe ya shiga ciki kiran matanshi. Ni kuma na shiga ƙarema gidan Gwadabe kallo. Ina mamaki yau gani a gidan Gwadabe a matsayin baƙuwarshi
Yarane suka fito su Toye an zama samari sosai
Can sai ga Babala ta fito da fara'arta ta nemi waje ta zauna..
"IYABO barka da arziki kune a tafe?"
Murmushi nayi na tsugunna har ƙasa na gaishe da Babala cike da girmamawa. A mugun kunyace ta amsa mun gaisuwata tare da yi mun jajen jarabawar data sameni.
"Iyabo a yi haƙuri a yafe ni dan kusan duk nice ummul aba'isin faruwar komai. Haƙiƙa na ɗauki darasi naga aya. Na kasa yafe ma kaina gani nake yi nice na jefaki a wannan hali.
Allah sarki Babala wallahi babu komai tun da ban riƙeki ba har cikin raina Allah ya yafemu nima in nayi miki laifi ki yafe mun. Ina su Yaya Hambali kuwa?"
Na É—auke zancan.."
"Hmmm yana can Kano tare da matarshi, tallan zoɓo ma take ɗaura mishi. Gwadabe ma yayi yayi ya jawo wan nashi jikinshi ya bashi jari wallahi mitsiyaciyar matarshi Layla taƙi. Layla yake aure wacce a baya naso Gwadabe ya aura. Duka take yi mishi ta mayar dashi sauna wallahi, sai in fi wata nawa ban sashi a idanuna ba ma" Ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka.
Ajjiyar zuchiya na sauke ina mamaki.
Sai ga Gwadabe da matanshi sun fito.
"Ah maraba lale Anty Iyabo yau ashe muna da manyan baƙi"
Cewar Shafa da fara'arta Hadiza kuwa tayi Magana ta kasa sai kallona kawai take yi ni kuma sai basarwa nake yi.
Nan dai aka zauna, sai ga Sakina ina ganinta na miƙe muka rungume juna cike da fara'ar yaushe gamo.
Mun gaisa naga yara duk sun girma sunata jami'a dan Gwadabe yace bazai aurar dasu ba sai sun gama karatu sun soma aiki tukunna nayi farin ciki sosai da hakan.
Inata mamakin matar Gwadabe dan ko gaisawa bamui ba tana ta haÉ—e rai.
Da za mu tafi nayi ma Shafa da Babala alkhairi na kudi, suma yaran nasu daban, na takwarata kuwa na musamman ne. Bayan mun yi sallar la'asar anci an sha mu kai musu sallama a mutunce.
To a Kano nayi gyaran jiki na yi duk abinda ya dace Uwani ta zagaya dani gidajen da duk su ka sai mun. Sai na kira yaya Hamma a waya mu ka shawarta ina son in zauna a Kano in da hali tunda ga gidajenan dani ni Sokoto ba wani daɗi zatai mun ba. Shi kuma ya nuna mun sana'arshi ta samu kafuwa sosai to sai na haƙura na koma Jaɓɓi lamba bayan na ziyarci su Burodami Debisi.
Ina isa na samu Hamma yayi mun akwati uku shaƙe da kaya na garari. Su Chubu sai shirin rakiyata suke yi.
Ranar dana gama iddata aka tara dangi mota biyu da tawa motar da motar Yaya Hamma akai mana rakiya
Zuwa Kano a maimakon Sokoto tunda na sadaƙar yace can yake son mu zauna sabida kasuwancinshi ya kafu.
Dada ta riƙe hannuna ta dinga yi mun adda'a tana tofa mun. Idanuna a rufe inata rera kukan da bansan na menene ba.
Tafiya yankin azaba.
A gidana na titin mandawari na tare madaidaici mai kyau ginin zamani, gashi yasha tsadaddun kaya wanda duk Yaya Hamma ne yayi mun da taimakon Uwani dan ita ashe ya faÉ—a mata zan tare a Kano É—in tunda na nuna hakan nake so. Nanma aka gama bikin da za'ayi washegari su BaÉ—É—o da Chubu suka juya gida ya rage daga ni sai su Nana. Uwani ma ta tafi tace gobe zata sa a kawo mun kayan kari.
Da daddare na caɓa ado irin na amare ina zaune a falo sai ga Yaya Hamma ya shigo yana sanye cikin farar shadda dinkin malum_malum ga hular zanna a kanshi yanata ƙamshin turare.
Hannunshi shaƙe da ledar kajin amarci.
Miƙewa nai da sassarfa na isa gareshi na faɗa ɗan ƙirjinshi yayi mun riƙon alewar yara sai na saki kuka da naji ɗuminshi. Shi kuwa ya shiga aikin rarrashi. Ya riƙeni dam a jikinshi shafani kawai yake yi yana tambayata.
"Shin mafarkine wannan ko gaske, Iyabona kece wannan a jikina. Tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya dawo mun da hankalin matata. Allah na gode maka.
IYABO zan baki farin ciki fiye da irin wanda Alhaji Usman ya baki. Zan rayu dake ke É—aya tak babu kishiya.
Wannan dare shine dare mafi daraja sai da mu kai wanka uku a wannan daren kunsan iyabo bani da wasa ta wannan fage. Hamma yana kwance yana baccinshi ni kuma na tashi na zauna na zuba mishi idanu ina kallon kyakkyawar fuskarshi.
Ajjiyar zuchiya na sauke kawai
Allah al hakeem kenan
Duk wata cuta da Hama tai mun ban yafe ba Allah shi zai saka mun da izinin Allah

Ƙarshe
Anan iyakar abinda na tsunto muku zai tsaya darasin dake cikin labarin Allah ya bamu ikon amfanuwa da kaɗan daga ciki. Ragowar labarin ku ƙarasheshi a ƙwaƙwalenku
Kusakuran dake ciki Allah ya yafe mini.
Duk waÉ—anda suka sai littafinnan ku sani da izinin Allah Allah zai faranta mutu dan da kuÉ—inku muka saka iyayen marayu dariya kuma sun yi adda'a
Nera biyar banci ba kamar yada na shaida muku hidimar marayu akayi.

Wanne darasi ke kika koya a wannan tafiyar?
Menene babban abinda ya fi burgeki
A cikin mazaje uku da Iyabo tayi zaman aure dasu wa yafi sonta a naku tunanin?

Sai mun sake haÉ—uwa a wata sabuwar tafiyar da izinin Allah
Tafiyar da babu dana sani a cikinta
Alƙalami yafi tokobi
Ƴar mutan kanuri nake cewa daku sai anjima.

Ina godiya masoyana, ina godiya ga dukkan masoyana na faÉ—in duniya waÉ—anda suke bibiyar rubutuna.

Jinjina ga NAMA YA DAHU ROMO ÆŠANYE ÆŠAKIN SHARHI"

JINJINA GA NAMA YA DAHU ROMO ÆŠANYE PAID GROUP

JINJINA GA HAUSA NOVELS GROUP BATI.COM
comments dinku na bani nishaÉ—i.

A group ɗin ɗakin sharhi muna gabatar da programs na mutunci, na zamantakewar aure, tare da ba da shawarwari da izinin Allah. Masu gabatarwa ƙwararrune kuma manyane a shekuru da tunani, da kuma rayuwar gidan aure. Nima ina ɗaya daga cikin shuwagabannin, in kina son ki dinga jin muryata kai tsaye ki kasance dani.
Mai son kasancewa damu a link nan ya shigo muna maraba da ku masoyan asali.

Nagode da jumurin bibiyata da kukai tayi duk da ciwon ido da ya dinga yi mana kutse.
Sai na sake fitowa a wata tafiyar da zaku ji daÉ—inta fiye da wannan
Chapter 237 · 0% Book details