← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 223 OF 237

Sashe 223

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Da sauri ya juyo sai yaga ashe Bara'u ne a bayanshi.
Bai ga Bara'u a cikin daÉ—i ba, kamar yadda shima ba'a cikin daÉ—in yake ba. Juna suka zuba ma idanu cikinsu ko wanne na son jin damuwar É—an uwanshi.
", Gwadabe ya dai na ganka tsaye kana sharar hawaye? Ai godema Allah ya kamata kayi. Kai da ganin su Babala kasan sunyi nadamar abubbuwa da yawa. Komai fa ya lalace kai Layla har zane Yaya Hambali take yi. Dukiyar ma daya tara ta kusan ƙarewa tas in faɗa maka."
Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke. Tare da kallon Bara'u da kyau yace.
"Wani al'amari marar daÉ—i na shirin tunkaroni, da ganin fuskarka kaji labari mummuna Bara'u meke faruwa?"
Murmushi Bara'u yayi kawai ya ja hannun Gwadabe har zuwa ƙofar gidanshi, suka zauna a kututture tare da fuskantar juna.
"Na zaunar da kaine dan gudun kar in yi maka bayani daga tsaye a samu matsala babba.
Amman mu musulmaine dole mu yadda da ƙaddara duk muninta da kaifinta. Asalima rayuwar gabaki ɗayanta jarabawane ranar lahira kuma ranar karɓar sakamakone. Gwadabe Iyabo ashe ɓata tayi an nemeta sama ko ƙasa an rasa. Wallahi Gwadabe da ƙyar na kawo kaina Takai da naji mummunan labarinnan"
Gwadabe bai gama jiba numfashinshi ya ɗauke Bara'u sai ganin Gwadabe yayi lu ya faɗi ƙasa wanwar.
A guje ya shiga cikin gida, Sakina na bakin bambu tana É—iban ruwa. Bara'u ya warce moÉ—ar cike da ruwa ya danna da gudu.
Sakina ta biyoshi a guje dan ganin meke faruwa. Gwadabe ta gani shanshar a ƙasa Bara'u na shafa mishi ruwa a maɗigarshi.
Da sauri ta fito babu ko mayafi.
"Subhanallaah meke faruwa Bara'u "
Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke ya buÉ—e idanunshi yana kallon Bara'u da Sakina da suka tusashi a gaba.
Hawaye ke bin kumatunshi ƙaƙas kamar ƙaramin yaro mai shan mamma in yi muku hausar ƴan Ghana.
"Alhamdulillah. Taso mu shiga daga ciki kaga mutane har sun soma ɗan taruwa kasan ƙauye da gulma."
Gwadabe dai babu kalma zungui_zungui yabi Bara'u da Sakina zuwa cikin gidan. A jikin garu ya jingina.
"Bara'u kace fa Iyabo ta ɓata sai kace wani ƙwallo ɗan mutum ace ya ɓata. Yaushe kuma a ina kaji?"
A mugun ruɗe Gwadabe yake magana yana jijjiga Bara'u. Sakina kuma ta saki salati da tattafa hannaye tare da riƙe haɓa.
"Bangane Iyabo ta ɓata ba. Bara'u kayi mana bayani"
Kai Gwadabe ya dafe tare da É—aga kai sama hawaye sai sharara suke yi ta gefe da gefen fuskarshi.
"Ya Allah. Bara'u zuchiyata fashewa zata yi. Bara'u ka kaini asibiti zan mutu"
Tashin hankali gaga _gaga Bara'u da Sakina suka yi asibitin Takai da Gwadabe. Abu kamar wasa ba sai ƙaramar magana ta ke son zama babba ba. Kafin wayewar gari Gwadabe ya fice a hayyacinshi sosai.
A kusan tsaye Bara'u ya kwana a kanshi.
Sai da safe gidansu Shafa suka samu labarin halin da Gwadabe yake ciki.
Afujajan Shafa ta ƙaraso asibitin ta zo ta samu Gwadabe ya samu bacci Bara'u na zaune a gefen gadon ya zuba tagumi.
"Yaya Bara'u wai me ke damunsh ne haka naga lafiyar Allah muka rabu dashi ya saukeni a gida?"
Ajjiyar zuchiya Bara'u yayi ya dubi Shafa yace.
"Wallahi Shafa iyabo ce ta ɓata aka nemeta aka rasa ta ma jima da ɓatan. Yau na shiga Kano kwatsam na haɗu da ƙaninta shine yake sanar mini halin da ake ciki, anata cigiyarta a gidan rediyo"
Salati Shafa tayi tayi shiru tace.
"Allah sarki duk inda take Allah yasa tana hannu mai kyau. Oh baiwar Allah kenan ko menene silar ɓatan sai Allah"
"Ana dai zargin wai kishiyarta ce tayi mata kurciya ta bazama abun damuwar da goyo a bayanta ga mijin nasu baya nan bai san ma me ake ciki ba'
Ashe Gwadabe ya farka sai ji suka yi yace.
"Allah zai saka mata koma wanene yayi silar ɓatanta.
Na kaÉ—une ainun da wannan labarin na bagatatan."
Bara'u yayi saurin duban Gwadabe yace.
"Gwadabe kayi haƙuri mu bar maganar zuwa ka samu lafiya. Likita yace mun kar ayi wata maganar da zata ɓata maka rai kayi haƙuri kayi shiru ga Shafa.
Ni bara in kira likita yazo"
Yana gama faɗar haka ya miƙe ya fita.
Shafa ta dawo bakin gadon ta zauna suna fuskantar juna.
"Haba Baban Abba in banda abinka ai adda'a ya kamata ka dage mata dashi domin babu abinda yafi ƙarfin Allah. Ita kuma adda'a bata faɗuwa ƙasa banza. Hakika na tausayama Anti Iyabo sosai, na kuma tausaya ma danginta dan ɓatan rai uku bafa wasa bane.
Abinda zamu yi shine tunda Yaya Bara'u yasan ƙauyen da take sai mu ɗunguma muje ayi musu jaje ko babu komai ai ta haifa maka yara har uku, kuma sune kan gidan tunda sune manya"
Shafa ta dinga kwantar ma da Gwadabe hankalinshi har sai da Bara'u da Likita suka shigo tayi shiru.
"Yanzu meke maka ciwo Gwadabe yaya kake jin jikin naka?"
Likita ya jefo mishi tambayar.
"Ina jin jiri sosai daga kwancen da nake, sai matsanancin ciwon kai, ga faÉ—uwar gaba"
"Assha sannu Allah ya sauwaƙe. Dan Allah duk abinda ke zuchiyarka ka daure ka cire ko dan ƙoshin lafiyarka jininka ne ya hau sosai a taƙaice ka kamu da ciwon hawan jini na farat ɗaya a sakamakon jin mummunan labari. Zamu ɗan riƙe ka mu kula da kai tukunna sannan zamu ɗauraka bisa magunguna.
Ku kuma da kuke tare dashi ku kula wajen tausarshi da rarrashin shi."
Likitan dai ya É—anyi gwaje_gwajenshi yace a samu abinci a ba Gwadabe yaci zai sha magani.
Ai kuwa likitan na fita Sakina ta shigo kici_kici da kayan abinci. Shafa ce ta zuba mishi kokko da lafiyayyen ƙosai. Bara'u ya taimaka mishi ya jingina da gadon. Nan aka shiga tata ɓurza dashi, shi yana ya ƙoshi, su suna ya daure ko babu yawa yaci. Ƙosai biyu da kokko rabin kofi yasha da ƙyar, sai maganinshi da yasha, bai jima ba bacci ya sureshi.
"Wallahi jiya ban rintsa ba. Bara'u ai ya kamata mu je mu can ƙauyen da abin ya faru ko?"
Cewar Sakina kenan. Shafa tace.
"Nima nace mishi muje ayi musu jaje sannan a jiyo ko akwai wani labari. Yanzu dai da zaran ya samu lafiya ai sai mu rankaya mu je tunda kai kasan garin.
Kamar dai wasa sai da Gwadabe ya kwana uku a asibiti kafin aka bashi sallama
Meeting ɗin da bai samu halarta ba kenan. A ranar da za'a sallameshi Chairman da kansila Zulƙi suka zo dubiya asibitin
Shigowarsu kenan Da'u da Yaya Halima ma sun shigo duba Gwadaben kuma Babala ce taji labarin a gari shine ta wakiltasu suje su duboshi.
Mamakine ya kashe su ganin yadda Chairman da kanshi shi ya biya kuɗin sallama. Sun dai san Zulƙi abokin ƙuruciyar Gwadabe ne, amman basusan meye alaƙar Gwadabe da Chairman ɗin ba.
Basu samu ganawa da Gwadaben ba dan basu samu kallon arziki ba ya dai amsa musu gaisuwarsu baya ga haka baice komai ba. Da shirun yayi yawa ne sai Halima tace.
"Da'u mu je gida hakanan. Gwadabe Allah ya ƙara sauƙi"
"Ameen nagode, ku gaisa gida"
Jiki a mace suka fita. KuÉ—i ya zaro ya ba Shafa yace ta kai musu
Ta fita ta samu Yaya Halima na share hawaye.
"Yaya wai gashi Baban Abba yace in baku"
Da sauri harda rige_rige wajen karɓar kuɗin Da'u ne yayi nasarar warce kudin. Kwana uku cib basu ɗaura tukunya ba, sai dai abinda aka dafa a gidan aka basu.
"Shafa kice mishi mun gode. Me sunan Æ´ar tamu ne?"
Murmusawa Shafa tayi tace.
"Sunanta Iyabo"
Tare suka sake maimaita sunan.
"Iyabo?"
Sai suka shiga karkaÉ—a kai kawai. A wajen dai Shafa ta koma ta barsu.
To ana sallamar Gwadabe suka rankaya gidan Bara'u. Gwadabe ya mugun matsantama kanshi sosai.
"Gwadabe abinka ya soma zama fa iskanci. Shin ka mance wai Iyabo da mijinta ne? Kafa sauwaƙama kan ka.
Ka daure kaci abincin kaga kayi ma Chairman alƙawarin zaka je ku tattauna zuwa bayan isha a gidanshi. Yanzu dai ga abincinnan ka daure kaci sai mu tafi sallah."
Ganin ran Bara'u ya ɓaci da yawa ne yasa Gwadabe yayi saurin jawo abincin gabanshi ya soma ci.
"Yauwa tsuntsun soyayya ko kaifa. Amman naga jikin naka babu ƙarfi zamu iya tafiya mai nisa gobe kuwa garin fa da bala'in nisa. Ko dai mu bari ka warware da kyau ne?"
"A_a Bara'u jikin fa babu laifi. Jirinma ai kaga da sauƙi"
Ya faɗa da sauri, tare da ƙara ƙwarara kanshi. Alwala suka yi suka fice masallaci sallar magriba.
Ai kuwa ga Gwadabe a sahu ga Da'u. Gabansu kuwa Sukairajune, shi bai ga shigowar Gwadabe ba har sai da aka idar da sallah. Juyowar da zaiyi carab idanunsu ya sarƙe dana juna. Sukairaju yayi tsamo_tsamo sai kallon Gwadabe yake yi ƙaunar ƴan uwantaka na ratsashi. Haƙiƙa suna jin matsananciyar kunyar Gwadabe domin sun san abinda suka yi mishi babu daɗi sun sashi a cikin tsaka mai wuyar fita. Amman dake Allah al hakim ne yau jibi Gwadabe cikin rigar mutunci, su kuwa babu sana'a babu dukiya yanzu ne suka soma daga farko, a yayin da shi kuma Gwadabe likkafarshi taci gaba.
Sum_sum Sukairaju ya fice daga Masallacin ba tare daya kula Gwadaben ba. Shima da idanu kaÉ—ai ya bishi har ya fice yana mamakin ramarshi.
Da'u dai da zai fita sai da ya sake gaishe da Gwadabe da jiki tare da yin godiyar kuÉ—in da Shafa ta kawo musu É—azu kafin ya fita.
Zulƙi ne ya matso kusa dasu sukaita hirarsu a ƙoƙarinsu na kawarma da Gwadabe tunaninshi.
Suna sallacewa suka nufi gidan Chairman dan tattaunawa.
Taron daya haÉ—a da masu jiran kujerar kansilolin ragowar gundumomin kamar dai Gwadabe suka ga junansu aka gaggaisa nan taron ya soma.
"To mu dai fatanmu shine kamar yadda gwamna yace mu zaɓo waɗanda suka cancanta, a namu tunanin mun zaɓo ku. Ya kuma rage naku ku yi abinda har abada tarihi bazai manta daku ba. Ku sani wata amanace ta talakawa zata dawo hannunku. In kuka hau kujerar mulkinnan ku ji tsoron Allah ku yi tsaiwar daka dan ganin kun wakilci Takai wakilci mai kyau"
Charman ya jima sosai yana bayaninshi. Kafin É—ays bayan É—aya Æ´an takarar gundumomin suka soma nasu jawabin dalla_dallah. Taron bai watse ba sai da suka yi liyafar cin abinci tukunna. Bara'u dai shi kaÉ—aine É—an rakiya yau gashi dalili yayi dalili gashi ga Chairman a zaune a inuwa É—aya harma yana cin abincin gidanshi. Allah mai iko"
Washegari suka É—auki hanyar Adamawa amman Bara'u ya ba da shawarar Shafa ta zauna ita da Sakina su dai su tafi, dan tafiyar bata rago bace.
Suna ta casar tafiya a hanya amman Gwadabe hankalinshi da tunaninshi ma basa jikinshi yayi zurfi sosai.
Chapter 223 · 0% Book details