← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 216 OF 237

Sashe 216

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mayafina na saka na fita cikin nutsuwa. Yana cikin mota idanunshi ƙur a ƙofar gidanmu. Wannan karon fararen kayane a jikinshi ɗinkin malum_malum, da hularshi ƴar asali zanna bukar, kunsan akwai zanna habu. Ganin yaƙi fitowa yasa na zagayo na shiga motar Juyowa yayi da kyau yana ƙaremun kallo yana murmushi. "Gimbiya ji nake kamar in tada motarnan in wuce dake gidana duniya ta dena kallemun ke. Babban abinda yafi komai farin ciki shine Alhajina ya bani goyon bayan ƙarin aure ɗari bisa ɗari. Yanzu abinda kawai ya rage shine dana dawo ayi batun aurenmu." Murmushi kawai nake ta yi nutsuwarshi na burgeni sosai. To Alhamdulillah. Da Farko dai ya hanya, ina fatan ka iso lafiya ko?" Idanu ya lumshe sosai kana yaace "Lafiya lau na iso gimbiyata. Ya soyayyata da fatan dai kina killace mun kanki ko?" Sosai ma ai ba kai kaɗai son yai ma kamu ba harda zuchiyar Iyabo. Yanzu dai mu shiga daga ciki ka samu kaci abinci tukunna" Saida ya gama ƙaremun kallo kana yace. "To Shikenan muje. Bari in kashe motar aro" Dariya mu ka yi dukkanmu ya zare keyn motar muka fito. Ledoji ya ciro a bayan both muka shiga gidan tare. Ƴan matan gidan duk suna tsakar gida sabida tsabaragen gulma. Har suna haɗa baki wajen gaisheshi. Ni dai na shige dashi zuwa ciki ya zauna a shinfiɗar da nayi mishi yanata kallona. "Kinsan menene gani nake yi da Alhaji zai mun alfarma da an ɗaura aurennan kafin in koma wajen aikina kinga sai mu koma tare ko?" Ƙarashe zuba mishi abincin nayi na turo gabanshi na nemi waje na zauna. Ba a Gomben kake aiki bane daman?" "Nayi babban laifi ban sanar dake ba ko? A India nake aiki a wani asibitin mahaukata. Inna tafi wata huɗu nake yi kafin in dawo. Amman ina tafiya da mace ɗaya in zan dawo sai in dawo da'ita in ɗauki wacce na bari haka muke yi. Amman ke kam acan zaki zauna tare dani, ba na son ki tambayi dalili kuma" Murmushi nayi a zuchiyata ina ta jujjuya lamarin dai. Yana cikin cin abinci sai ga Batula ta shigo da biyu a hannunta. Suna ganina suka soma zullo. Ƙur yayi musu da fararen idanunshi irin nasu. Hannu ya miƙa Batula ta bashi Usaini. Ni kuma ta ajjiye mun Hassan ɗin. "Barka da zuwa master da fatan ka iso lafiya?" Dariya yayi yace. "A ina na samo suna master ni Usman ɗan Usman?" Batula tace "Master a zuchiyar maman biyu mana. Gaskiya dai kaci sa'a ka warce zuchiyar Iyabo " Kallona yayi yace. "Wai hakane gimbiya abinda ƙawarki tace?" Sosai kuwa abinda ta faɗa hakane" Da dariya da wasa suka gaisa tayi ficewarta. Sai ya bar cin abincin ya shiga wasa da ƴan biyu. "Dr ya fa kamata ka bar yarannan kaci abincinka kar yayi sanyi ko? Kaga kawo shi. Nayi yinƙurin ɗauke Usaini a jikinshi ya hanani fur daga ƙarshe ma yana cin abincin yana basu suna ci. Ni kuma sai nake musu kallon sha'awa. "Kin yi shiru kina ta kallonmu ba dai tunanin tsohon mijinki kike yi ba dai ko? Yaji shiru na zurfafa tunanin da in wuƙa za'a saka mun ni bansan tunanin me nake yi ba. "Gimbiya kina tare dani?" Ya faɗa da ɗan ƙarfi kafin naji me yace na yi saurin kallonshi, sai yaga hawaye fal idanuna. Ƙuramun idanu yayi sosai yana kallona har hawayennan yabar guraben idanuna ya shiga sauka a kumatuna bai dena kallona ba. Da dai yaga kukan yaƙi ci yaƙi cinyewa sai ya lumshe idanunshi ya sake buɗesu a kaina. "Iyabo kamar Baban yarannan yana zuchiyarki kenan fa. Duk da dai dama nima nayi karambanin shigewa rayuwarki, da ma zurfafa akan sonki ba tare da naji tarihinki da asalin abinda ya fito dake ba. Duk da dai Hajja Mama ta faɗamun ke ƴar uwarta ce ta jini aurenki ne daya mutu tasa aka kawoki wajenta shi ya bani ƙarfin guiwa. Zan barki kiyi tunani ki zaɓi abinda yafi miki kyau ni ko tsohon mijinki' Yana dasa aya ya miƙe tsaye hannu yasa a aljihu ya zaro kuɗi ya ajjiyesu a gabana. "Zuwa jibi zamu koma India sai nan da wata huɗu zan shigo najeriya na barki lafiya" Ya saka kai ya wuce. Har ya fita ban iya motsawa ba bansan kukan me nake yi ba gaskiya. Da sauri na miƙe na fice a gidan yana cikin motarshi ya ɗaura kanshi akan sitiyari na buɗe murfin motar na shigo. Baiko ɗago ba idanunshi ma a rufe suke yanata dai karanto adda'a" Wallahi ina sonka so na gaskiya. Karma shaiɗan yayi tasarin rabamu. Batun uban ƴaƴana babu a raina ka yarda dani." "To menene silar zuban hawayenki da har kike ƙoƙarin tayar mun da ciwona uhm?" Wallahi da kai da yaranne kuka bani sha'awa wannan shine silar zubar da hawayena" Ajjiyar zuchiya ya sauke mai nauyi sai lokacin ya ɗago kanshi ya zuba mun idanunshi har sun sauya nauni. "Wai ke kinji irin luguden da zuchiyata take yi kuwa? Ji nayi inna rasaki komai zai iya faruwa dani. Kinsan ni ban iya son abuba Alhajina kullum a cikin yi mun nasiha yake sabida a gaskiya so ya bani wahala sosai bazan ɓoye miki ba" Kafin kayi auren fari kenan ko bayan kayi?" Dariya yayi sosai tare da duba agogon hannunshi. "Ki shiga gida gimbiya zanje hotel in ɗan watsa ruwa in kwanta kaina ma ciwo yake yi kece kuma sila" Hannuna na haɗe waje guda nace. Tuba nake yi ranka shi daɗe aimun afuwa dan Allah. Kaje Allah ya huce gajiya sai yaushe kuma?" Idanu ya lumshe yace. "Sai dare in nazo sallama dake gobe da sassafe zan juya, jibi zamu bar ƙasar kinga Suhaila na buƙatata a kusa da'ita ko?" Ya ƙarashe maganar yana mun dariya. Hakane kam tana buƙatarka. "Kafin in dawo zan turo iyayena ayi komai a gama nan da wata biyu in an ɗaura auren zanyi ƙoƙari in dawo sai in tafi dake kudun kallon ruwa kwaɗo yazo yai mun ƙafa. Amman me kike gani? Bari in nazo da daddare zamu tsaida magana " Da haka mu kai sallama ya tafi. Na dawo na tadda Batula a gaban kayan tanata dubawa kayan tea ne manya manyan gongoni, sai atampa da bayafai da wani turare mai ruwan ja a jikinshi. "Zaki fita ki bar damin kuɗi a yashe sabida rashin hankali?" Ke dai bari ana ta kai wama yake ta kaya. Ke Batula gayennan fa aure yake so muyi faka_faka nan da wata biyu. Ni babbar damuwata shine abubbuwan dana manta na baya. Bazan iya ce miki wacece ni ba wallahi, babu abinda zan iya tunowa" Ajjiyar zuchiya Batula ta sauke tare da dafa ni tace. "Al'amarinki da girma kuma akwai sarƙaƙiya sosai. Amman ni ina ganin kar ki rufi Usman ki faɗa mishi gaskiya amman ki bari ayi auren tukunna gudun kar ki faɗa mishi yanzu yazo ya fasa ko iyayenshi su kawo cikas. Hajja Mama ta riga data sanar mishi ke ƴar ƙanwarta ce. Ta aurar da mata da dama ba tare da sanin danginsu ba dan wasu ma musulunta su ka yi, kuma suna zaune wasunsu a gidan miji. Ni ina ganin karma ki damu muyi ta shirye_shiryen biki kawai kefa kakarki ce ta yanke saƙa wallahi. Dariya mu ka yi harda tafawa. Zuwa bayan isha sai ga kiran Usman bin Usman ya zo yana ƙofar gida. Dama na yi kwalliyata nayi kyau shi kawai nake jira, motar na ɓalle na shiga, wannan karon wankan ƙananan kaya yayi sai yayi yaro dashi. Motar kawai naga ya ja mun hau titi. Ina zamu je ne?" "Kina tsoron kar in sace ki ko?" Dariya mu ka yi duka kafin yace mun wani ɗan waje zamu je mu zauna inda zamu samu nutsuwa da damar gabatar da abinda ya kamata na dangane da bikinmu Wani ɗan gidan abinci ya kaimu muka zauna odar abun sha kawai yayi mana. "To ina jinki me kike ganin ya dace ki tsara ta ɓangarenki? Zasu kawo lefe da sadaki, me kike so daga gareni kuma? Dan har nayi ma Yata magana ta haɗa mun lefe gangariya." Ni dai jikina a mace tiɓis sai nake jin wani raɗaɗi a zuchiyata wanda bansan na menene ba. To ni dai lokacin ne nake tunanin yayi wuri me zai hana a barshi a wata huɗun kafinnan na kammala shirye_shiryena a hankali? " Sai ya haɗe ranshi, ni kuma zuchiyata sai lugude take yi mini. "Wanne irin shirine wannan da ba za'a iya yinshi a wata biyun ba to? Mu da ba yara bane da zamu yi ta yin taɗi ba." Da ƙyar nake danne wani abu dake hankaɗo kanshi a zuchiyata. Kayan ɗaki, da dai abubuwan da ba'a rasaba namu na mata" Dariya yayi mun yace. "Zamu yi magana da Hajja Mama duk abinda ake buƙata zanyi daidai gwargwado. Ni fa ke kaɗai nake buƙata barinma data faɗa mun ke marainiyace ashe mahaifanki duk Allah yayi musu rasuwane. Allah ya jiƙansu da rahama in sha Allah ni zan maye miki gurbinsu" Ameen to nagode" Iyakar abinda na iya cewa kenan kawai sai na ɓalle da kuka kukan da ni bansan na menene ba rayuwata ce naji tayi ƙunci sosai. Shi kuma rarrashina ya dinga yi yana tunanin sabida mahaifanane dana tuna. Haka dai mu kai sallama babu daɗi. Washegari sassafe jirginshi ya ɗaga. Hajja Mama ce ta zaunar dani take mun gargaɗin ko da wasa kar in kuskura in nuna mishi manta rayuwata ta baya nayi in ba haka ba bazai taɓa auren marar asali ba. In barshi a zuwan iyayenane suka rasu in rayu cikin daula in mance da damuwar komai. Ita a tunaninta tsabar azabar da rijalu ƙila suka ganamunne yasa ƙwaƙwalwata ta samu matsala. Bata san al'amarin nawa babba bane ga dai aure a kan aure yanata tunkarowa. A kullum shaƙuwar dake tsakanina da Usman sai sake yaɗuwa take yi, sai na shiga tunanin san tuna wacece ni sai inji rayuwata tayi ƙunci kai wata shari'ar sai a lahira akan wata cutarwar da za'ayi maka. Kamar yadda Usman ya faɗa ya tafi da wata guda aka kawo lefena garin Lagos wajen Hajja Mama. Dangin arziki ne Usman sosai dan ƴan uwanshi sun kasa ɓoye mamakinsu akan irin gidan da yaga
Chapter 216 · 0% Book details