← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 237

Sashe 53

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

16 Kwanon da aka ajjiye mishi ya jawo. Tuwon ɓula ya gani da miyar bushasshiyar karkashi. A tsanake ya soma ci, wannan tuwo ya bashi mamaki matuƙa dan a ido bashi da kyan gani, amman a baki akwai daɗi sosai. Zama ya gyara yaci gaba da kantara loma. Wannan budurwar dake kwance a gadon bono ce ta yi miƙa ta tashi zaune tana salati. Wankar tarwaɗace kyakkyawa ma'abociyar siririyar fuska da siririn hanci, laɓɓanta suna da ɗan girma kuma a ɗane suke, haƙorinta biyu manya na gaba a waje suke ko da bakinta a rufe yake. Masu irin wannan haƙorin ana ce musu masu haƙorin zomo. Leɓenta baƙine wukul duk da ya fahimci duk mata da yaran gidan bakinsu duk baƙaƙene kuma kamar wani abun suke yi dan leɓen ya zama haka. Bata da idanu manya ƙanana ne idanunta kamar an huda sakwara, ga gashin ido da yaima idanun rumfa, in ba zaro idanun tayi ba ma baka isa ka ga ƙwayar idanun ba." Ganin Gwadabe a zaune yasa ta rarami mayafi ta rufe jikinta ruf. "Kayi haƙuri bansan kana ciki ba" Ta yi magana muryarta na rawa. A gaggauce ta gaisheshi ta fita. Itama doguwace mai kauri yar duma_duma fatar jikinta luwai_luwai dashi gwanin ban sha'awa, ga mazaunai ɓaka_baƙa. Iyabo ce ta dawo mishi rai, da irin yanda in ta yi walliyar ɗinkin buba da zani take burgeshi, da yanda in ya kallli tudun mazaunanta ta bata yake ɗimaucewa. Ajjiyar zuchiya ya sauke a fili yace. "Ina miki fatan samun namiji lafiyye wanda zai kula dake, ki huta a gidan mijinki irin hutawar da kika rasa a gidana. Allah ka sa jin daɗi da nutsuwa a rayuwar Iyabo ta gaba. " Gabaki ɗaya abincin sai ya fice mishi a kanshi ma, rufe kwanon tuwon yayi ya sha ruwa. Yana zaune ƙwalam wannan basamudiyar budurwar ta sake shigowa dan doguwace ingarma. "Baba tace in ka gama in raka ka shashen samarin gidan ka je ka yi wanka ka huta" Ledar ɗan kayanshi kala biyu ya cacuma ya soke a hammata, baice mata komai ba ya biyo bayanta suka fito. Iyayen gidan basa tsakar gidan, sai tsirarin yara matasa masu wasa kawai. Tiryan_tiryan yana biye da'ita har zuwa wata ƙofa da suka shiga yaga ɗakuna kusan bakwai a jere, da ba haya mara ƙofa sai labulen buhu yana kallosu, sai durom biyu na ruwa, da ƴan butoci, da bokiti. Wani ɗaki ta tura ta shiga. "Bismillahi ka shigo" Bayanta yabi zuwa cikin ɗakin. Katifun yayi ne guda huɗu a jere, sai akwatunan ƙarfe suma guda huɗunne, ginine na jar laka, ba fulasta ba komai, ƙasan ɗakin ma ba daɓe ba komai, rairayin ƙasa ne takota ina sai ƴar tabarma da ke shimfiɗe, saman ɗakin kuma jinka ce, sai ƙwan lantarki guda ɗaya jol. "To bayan gida yana waje, akwai botiki, da ruwa zaka iya watsa ruwa. Lokacin sallah ma yayi sai ka sami malam a waje" "Nagode sosai, sai dai bansan sunanki ba har yanzu." Ya faɗa yana ƴar dariya. "Sunana Hadiza" "Ke yar Ine ce?" Ya tambayeta. "E yarta ce ni" Sallama tayi mishi ta fita. Shi kuma ya shiga kewaye yayi wanka tare da ɗauro alwala. Farin yadi ya saka, wanda ya cire kuma ya saka a botiki ya zuba ruwa, kafin ya fita waje wajen Malam. A ƙofar gidan Malam yai musu limanci. Bayan an idar da sallah almajirai sai suka soma karatu. "Gwadabe ga allo da tawada ka iya rubutu ko?" Sai da Gwadabe ya amshi allo da tawada da alƙalami yace. "E na iya Baba, a can Takai ma makarantar allon mu ka yi, sai dai karatun baiyi zurfi ba, banfi izifi huɗu ba" "Hakane na sani Gwadabe. To yanzu daga farkon izifi huɗun zamu soma. Yau ka bar rubutun kayi muraja'a yau da gobe, jibi kuma sai ka soma rubutun allo. Bana son wasa da karatu. Sannan ka zama jajirtacce sai Allah ya dafa maka. Na sani mahaifiyarka bata da daɗi, iyayenmu kansu sun sha yin kuka da'ita. In banda fitina ta Babala ina ita ina kafewa sai ɗanta ya auri ɓarauniya sabida Allah fa?" Ana cikin haka sai ga su Auwala, da Mammada. Baba Magaji ya gabatar musu da Gwadabe, sannan ya mikashi ga Auwala akan zuwa gobe zai soma fita tare dasu. Su Auwala suka karɓeshi hannu bibbiyu, kuma su kai maraba da shi. Baba Magaji yaranshi maza su rai goma sha ɗaya ne ras. Uku daga ciki sun yi aure, suna cikin gidan tare da iyalansu, tara kuma kowanne yana neman kudi, amman shida a ciki kowanne da budurwarshi da tsayayyar magana. Ukun yarane. Washe gari Gwadabe yabi zugar su Auwala zuwa can garin Ɗan Issa inda anan ya ga dandazon dubban al'umma masu haƙan zinariya. Tun daga nesa dai ya hango tudun laka kawai, sai da suka isa wajen ya ga dubban al'umma. Da rijiyoin haƙon zinariya sama da ɗari. Mammada ne ya ja hannun Gwadabe ya kaishi ga shugaba mai kula da ƴan ƙwadagon wajen ya sanar dashi malam ne yace a kawo shi ya dinga ganin aiki kafin a hankali kuma ya shiga ayari. To Alhamdulillah haka rayuwar Gwadabe taci gaba da tafiya, da safe su hau abun hawa zuwa ɗan Issa, da yamma su dawo gida, su ɗau karatu daga magriba zuwa taran dare, da asuba bayan sun yi sallah kuma zasu yi muraji'a kafin kuma su karya su tafi nema. Duk dabdala a ɗakin Baba Fhatsima Gwadabe yake yinta. Mace mai kawaici da son jama'a kenan. A cikin sati guda da Gwadabe yayi a gidan Baba Magaji, ya fahimci ana buga kishi sosai da sosai tsakanin matan Baba Magaji, yaran ma suna taɓawa dan ko wacce ta jaye yaranta, sun haɗe kawunansu isu_isu. Ko wani abune ya faru da ɗan wani ɗakin, sai aita rurrufewa sai dai in na alkhairi ne, ko dan fahari a fito tsakar gida a faɗeshi. Baba Suwaiba da Amaryar Malam sune suka fi gwabza kishi a tsakankaninsu, kasancewar sunfi Baba Fhatsima da Baba Asshi karancin shekaru, sune Baba Magaji ya aura a baya_baya. Dan Amaryar malam yarinyace da bata wuce shekarun Hadiza ba. Yaranta uku duk maza, sune ƙananu sosai a gidan. Fitinarta tafi ta kowa a cikin matan Baba Magaji, sabida tana ganin ai itace Amarya. Su kuma sauran matan kishinsu yafi tsananta akan Baba Fhatsima da yaran ɗakinta da suka kasance manya, masu jam ragamar komai a gidan. Yaya Tasi'u shine Babban yaron Baba Magaji, babban ɗan kasuwane da yake harkar riɗi da gero, kuma yana kiwon tsuntsaye masu darajar gaske, dangin su ɗawusu, da gigs, da Aku, da dai manyan tsuntsaye na ƙasashe da dama. Kasancewar shine Babba shike ciyar da iyalan gidan baki ɗaya, kuma shi ke yi ma yaran gidan Aure, da duk abinda uba yake yi ma ƴaƴanshi. To kasancewar Yaya Tasi'u ya fito a ɗakin Baba Fhatsima sai yaran ɗakin Baba Fhatsima suka zama yara daban a cikin gidan, yana basu kulawa ta musamman, Baba Fhatsima kullum a cikin shigar daraja take. Kuma matar Yaya Tasi'u mai Suna Badi'a tana yawan yin dabgen kaza ta ciko kwano ta kawo ma Baba Fhatsima. Ko Shi Yaya Tasi'un yasa ayo mata miyar kaji cikin tukunya, sai dai su dinga ci, dan ko abincin ɓarayin bata ci, daga can barayin Yaya Tasi'u ake kawo mata ishasshen lafiyayyen abinci. Ko da Sallah Yaya Tasi'u shi ke ma su malam da iyayen nashi mata layya. To ko akan ragon layyar duk shekara sai an samu yamutsi kan na Baba Fhatsima yafi na saurn matan gidan girma da ƙoshi. Haka dai ake wannan rayuwa a wannan gida. Ranar da Gwadabe ya cika sati guda bayan sun tashi daga karatun dare sai Malam ya zaunar dashi. "Gwadabe banyi maka batun mace bane dama nace bari in bari ka nitsa. To kaga akwai ƴan mata a gidana da yawa, duk da bakwai daga ciki am sa lokacin bikinsu. To shine nace ga Hadiza nan ina ganin kamar tafi sauran yaran hankali kasancewar bazawarace ita. Wata biyar kenan da mutuwar auren nata. A halin yanzu dai bata soma fita zance ba, in dai kana ganin tayi maka sai kayi ƙoƙari ku sasanta kanku. In kuma batayi ba, kar kaji nauyi ka faɗamun wacce tayi ma kai ko wacce tayi ma tana cikin waɗanda za'a aurar ne, zan iya baka ita, shi wancan yayi haƙuri. In kuma dukka basu yi maka ba to Shikenan sai in taya ka da adda'ar Allah ya kawo maka wacce zata zame maka alkhairi. Duk da dai mun soma maganar da Fhatsima, Tasi'u da kanshi sai yayi sha'awar maka Hadiza tunda dukkanku Zaurawane. Amman kaje kayi tunani. Gwadabe take zufa ta keto mishi, zuchiyarshi ta shiga harbawa da ƙarfi. Shi a halinnan da yake ciki na alhini da damuwar rashin Iyabo. Ina shi ina wata soyayya? Ta ina ma zai soma wata soyayya, baya jin akwai wata mace da zai iya bata zuchiyarshi harta samu gurbi. To taya zai kuɓutar da kanshi daga wannan tayi na Baba Magaji? Kuma ko yaya ya nuna baya son ko ɗaya daga cikin yaranshi tabbas bazai ji daɗi ba. Kuma shima nauyi da kunyar Baba Fhatsima zata iya hanashi zaman ƙasar. Gashi har ya soma sakewa, ya soma jin daɗin sabon wajen aikinshi, kuma Alhamdulillah shima harya soma shiga rijiyar tono, duk da yanda akaita tsoratashi, da irin yanda ake samun haɗarin ɗaruruwan mutane su rasa ransu ta dalilin rubtawar ƙasa, amman yasa a ranshi tunda anayi, shima zaiyi in sha Allah sai yayi kuɗi. Tunda yanzu zumuncin ma sai kana da hannu da shuni akeyi da kai. "Gwadabe kar ka damu, na baka sati ɗaya kaje ka yi tunani da kyau. Kuma ka kalli yaran da kyau ka zaɓi ka darje, in yaso shekara mai zuwa sai a haɗa auren naku dana su Mammada ayita ta ƙare. Akwai babban filina gashi can, a cikin filin almajiraina suke wanki, da duk wasu harkoki. To anan zaku zauna dukkanku, Tasi'u zai gina ma kowa ciki da falo_falo" Da haka Gwadabe ya tafi ya bar Baba Magaji akan zasu haɗu nan da sati mai zuwa yaji wacce ya zaɓa. Jikinshi a mace ya shiga cikin gidan. Ɗakin Baba Fhatsima kai tsaye ya shiga. Anan ya tarar da Auwala da Mammada suna zaune da abinci a gabansu,
Chapter 53 · 0% Book details