← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 205 OF 237

Sashe 205

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Gari ya waye. Kamar kullum matan gida suna ta hada_hadar data zame musu jiki.
Yau Jabu zata fito gobene, jibi ne shirun dai yayi yawa. Yafendo tana zaune tana burga nono tace.
"BaÉ—É—o je ki dubo Æ´ar uwartaki, yau ko gaisuwar safen data saba zuwa ban ganta ba. Allah dai yasa lafiya"
BaÉ—É—o ta tashi tsulum daga burgar madarar da take yi. Dama itama Æ´ar uwar tata take ta tunani a zuchiyarta. Tunda ta tashi sai take ta jin faÉ—uwar gaba.
Tana buɗe labulen ɗakin sai taga jabu bata ciki. Ta ƙarema ɗakin kallo komai yananan tsab har gado a lailaye yake, ga ɗankwalin zaninta a saman kujera.
Juyowa tayi ta sanar ma Yafendo bata cikin ɗakin ƙila ko ta fita ne.
"Kota fita fa kika ce? Tunda Jabu ta shigo gidannan take aure bata taɓa fita daidai da maƙota ba tare da ta sanar dani ba. Kuma kin duba banɗaki ko tana ciki?"
"A_a Yafendo bata ciki, sabida su Hassan ma basa cikin É—akin"
Shiru Yafendo tayi. Jikinta dana BaÉ—É—o duk sai ya mutu. Baddo tana tsaye ta kasa komawa kan aikinta take ita sai taji ma ba zata iya fita tallar nonon ba. Dan tuni jikinta ya bata akwai matsala.
Tsulum Yafendo ta miƙe dama da mayafi a jikinta ta dubi Baɗɗo tace.
"Taho muje BaÉ—É—o."
A gurguje BaÉ—É—o ta zare mayafin dake jikin Safiya tabi Yafendo a baya. Sukaita zuba sauri har dai suka isa gidan Dada.
Babu fa Jabu babu dalilinta.
"Adda Jabu bata zo gidannan ba?"
Dada ta miƙe tace.
"A_a rabona da'ita tun jiya da daddare dai bayan ta sallami Æ´an makaranta. Wani abunne?"
Ta ƙarashe maganar a raunace sosai.
Yafendo bata tsaya mata bayani ba ta figi BaÉ—É—o suka soma bi gidajen Æ´an uwa ko Allah zaisa a dace.
Amman duk inda akaje sai aga batanan. Jikinsu a sanyaye suka dawo gidan Dada.
Tana zaune tayi tagumi tunda suka fita gabanta ke dokawa.
"Yaya wai lafiya kuyi mun bayani mana wai?"
Yafendo ta zauna daɓas ta bata labarin abinda ke wakana.
Ƙirjinta ta dafe tace.
"Duk yadda akayi dai wata matsalarce. Amman zan shirya in tafi can Kano ko ta tafi can É—in.
Ku kwantar da hankalinku ƙila Kano ta tafi, wala Allah kota gaji da zaman ruga, ko kuma damuwar rashin mijinta."
Dada dai batai ƙasa a guiwa ba washe gari ta tafi Kano sassafe. Anan ma dai Yafendo taci gaba da shiga jejuna ko Allah zaisa taga Iyabo.
Cikin dare Dada ta isa Kano. Har Iyaa Debisi ta rufe shago sai gata.
"Daso kece da daddarennan kuma ke kaÉ—ai babu É—an rakiya?"
Murmushin dole tayi tace.
"Toyosi nice kin ganni"
"Maraba da zuwa, sannu da hanya"
Haka dai suka shiga ciki. Bayan Dada ta rama sallolinta sai suka sake gaggaisawa harma da matan gida.
"Toyo Iyabo bata zo gidannan bane?"
Iyaa Debisi ta dubeta da kyau ta fahimci akwai fa matsala, sai tace.
"Bata zo ba. Amman za'a iya duba gidan Uwani ko tana can. Wani sa'in in ta shigo gari a gidan Uwani take sauka. Ince dai lafiya ko Daso?"
"Bafa lafiya ba gaskiya. Yarinyarnan ce dai da sassafe surukarta tazo nemanta wajena. Sannan an karaÉ—e duk inda ya dace ace an sameta ba'a sameta ba acan. Shine nace bari inzo in duba ko tazo"
Ai da jin haka Iyaa Debisi ta shiga ihu tana kwakwazon kiran tashiga uku Daso ta salwantar mata da iyabonta. Kafin kuce kwabo gidan ya cika da matan gidan da samarin gidan. Nan akabar Dada da maimaicin zance. Da Dada, da iyaa Kokodeen, da Iyaa Debisi, da Lekan a daren suka nufi gidan Uwani. Har ta yi bacci taji bugun ƙofa yaƙi ƙarewa ga yarbanci anata yarawa. Jikinta na rawa ta buɗe data fahimci muryar Iyaa Debisi ta jiyo.
"Iyaa Debisi kune a darennan, Dada kune?"
Jikin Uwani ya mutu murus. Iyaa Debisi tace.
"Uwani ko Iyabo tazo gidanki kuwa?"
"A_a bata zo ba, ai bata jima da komawa ba"
Dada tace.
"Kuma ba kuyi waya ta faÉ—a miki inda zata tafi ba?"
Uwani jikinta na rawa sai kawai ta fashe da kuka. Su iyaa Kokodeen suma ai sai suka sau kuka. A darennan hankula sun tashi fiye da tunanin mai karatu.
Da Uwani aka kwasa zuwa can gidansu Iyaa Debisi. Kwanan zaune suka yi anata adda'a. Su Debisi dasu Bose, Burodami Kokodeen duk a daren Iyaa Debisi ta tasosu.
Washe gari sassafe suka sake rankaya harda uwani akayi Jaɓɓi lamba.
Wallahi zancan dai É—ayane babu Jabu babu labarinta.
A wannan gaɓar har Dada ta fita hayyacinta ta kwanta jinya. Uwani ce tace zata je Takai in sha Allah ko Iyabo ta tafi can duk da bata tunanin zata je.
Iyaa Debisi ce ta hanata tace.
"Iyabo ba zata taɓa zuwa Takai ba Uwani ni nasan Iyabo. Abinda za'ayi kawai shine akai report ofishin ƴan sanda, a yi sanarwa a gidan rediyo ko Allah zai sa a dace. Ni damuwata ga goyon yara har biyu. Daso anya kuwa ba kishiyarta bace tayi mata agumu ta cillataba kuwa?"
Carab Uwani tace.
"Ai babu tantama itace tayi mata wani abun baƙar mitsiyaciya makira. Da wanne irin asirine batai ma Iyabo ba. Balle tana ganin Iyabo ta haifi maza, yaranma ba kifesu akayi a ciki ba"
Fashewa da kuka tayi ta kasa ƙarashe zancan nata.
Gaga_gaga rikici dai sai ya zama gagarumi su Debisi sune har rugar su Hama. Ai kuwa Hama taci bugu sosai, da ƙyar maƙota suka amsheta. Gaga_gaga akaita tabka shari'a a gaban mai gari. To kunsam sha'ani irin wannan basu da wata hujja na cewar Hama ce taima Iyabo asiri. Kuma ko da kotu zasu je basu da hujjar itace tayi, duk da dai a baya su uwani da Baɗɗo sun kama abubbuwan asiri, shima ba hujja bace da za'a shiga kotu akanshi ba.
Maigari ya ba dangin Iyabo haƙuri ya haɗa da rarrashinsu dai haka dole aka fallawama Allah. Kwanansu Iyaa Debisi tara a Jaɓɓi lamba ana abu ɗaya kafin daga bisani suka koma.
Dada jikinta yayi mugun tsananin da bata ko iya gane wake kanta.
Haka su Uwani suka koma gida basu da yadda suka iya. Sai adda'a kawai suke bin Iyabo dashi. Uwani na shago haka siddan sai ta fashe da kuka. Haka ma iyaa Debisi take yi. Burodami Debisi kuwa kamar zaiyi hauka, shine wancan ofishin Æ´an sandan, shine wannan haka yaita sintiri amman jikakeyi shiru malam yaci shirwa.
Chapter 205 · 0% Book details