← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 237

Sashe 32

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

10 Duk wannan ƙibar tawa da kuka ji labarinta, wallahi ta zuge sosai, na gama ramewa na fice a hayyacina sosai. Shi kanshi Gwadabe yafi tausayina fiye da kanshi. Bara'u kullum a cikin jinjina ma ƙoƙarina gami da amanaa suke yi. A kullum roƙona shine Allah ya ba Gwadabe lafiya, ya yanke mishi wannan zaman. In zaman cikin ya isheshi shi da kanshi yake tuƙa kekenshi ya fita ƙwar gida ya sha iska. Mun gama siyar da komai namu kuɗin ya ƙare a magani, ɗakina goduwar kujer da kafet kaɗai ya rage, sai tarkacen kwanuka da katifa , itama sabida Gwadabe na barta Wata rana ina zaune ina wankin kayana dana yara sai ga Uwani ta shigo, Gwadabe kuma yana ƙofar gida ya ɗan fita shan iska "Uwar biyu wanki kike yi ne?" Wallahi kuwa, daga ina haka na ganki afujajan?" Na tambayeta tare da kallonta. Sai da ta cire mayafinta kana tace. "Hmm wata harkar arziki na samo Iyabo. Kin ganni daga cikin gari nake gidan Hajiya salamatu, wata matace dake kai ƴan mata da matan aure ƙashashen larabawa ko ƙasashen turawa. Amman kafinnan na samo miki maganin karya sihiri garanti, daga cikin ayayoyin Qur'ani mai girma. Bari in karanto miki, muddin kuka riƙe wannan da izinin Allah kuka yazo ƙarshe a cikin kwana na bakwai Gwadabe zai miƙe da ƙafafuwanshi." Ina jin haka na zabur na saki wanki. Na juyo na zuba mata idanu. Dan Allah faɗi ina saurarenki Uwani" Dariya tayi tace. "Ɗakko biro da takadda ina faɗa miki kina rubutawa, da izinin Allah waraka ta zo." Da sauri ba shiri na yago takadda, na ɗakko fensirin Toye na dawo. "Da farko zaki samu ruwanki mai tsabta. Sai ganyen magarya koraye bushewar inuwa guda bakwai. Sai a karanta suratul fatiha a cikin ruwan da aka zuba magaryan, a dinga karantawa numfashin baki na komawa cikin ruwan Sai a karanta Ayatul kursiyyu ( aya ta 255 na cikin suratul baƙara). Sai a karanta suratul a'afaaf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122. Sai a karanta yunus daga kan aya ta 79 zuwa kan ta 82. Suratul kafirun ƙafa ɗaya. Falaƙi da nasi ƙafa uku_uku Sai a karanta wannan adda'ar. Allahumma rabban nas,azhibil ba'as ashfi wa antash shafila shifa'a illa shifa'uk shafi'un la tugadiru sakaman Ƙafa uku za'a karanta. Sannan za'a iya karawa da wannan adda'ar "Bismillahi urkika min kulli shai'in yu'uziyaks wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urkika Shima ƙafa uku In sha Allah ta'ala idan aka karanta wadannan kuma mutum ya dinga sha sau biyu a rana safe da yamma, yana kuma wanka dashi a waje mai tsabta, ko kokuma a jiƙa tawul a goge jikin marar lafiyan da ruwan maganin. Da izinin Allah cikin sati ɗaya mutum zai warke in dai sihirine a jikinshi. ( Kuma zaku iya jarabawa. Wasu malaman sun ce yana da kyau wanda yake da lafiyarshi ma yayi, domin hakan ka iya zama rigakafi kafi magani kareshi. Wallahu mista'al) Wawuyar ajjiyar zuchiya na sauke tare da yaƙinin sauƙi ya zo ma Gwadabe. Duk da abaya masu magani sun bamu wasu mayuka tare da tofin ayoyin Allah a ciki mun yi amfani dasu da dama. Wasu kuma mu da kanmu muka zubar dasu, dan ganin shirka ta shiga cikin lamarin, amman wannan sai naji na samu nutsuwa dasu ainun. Nagode sosai ƙawata Allah dai ya bar zumunci. Bari ki ga da zafi zafi ake dukan ƙarfe bari in wanko ganyen magaryana, ina da ruwan sama cikin robar fenti sai in yi dashi. Sai fa na gama zan samu nutsuwa." Da sauri na je na ɗebo ganyen magarya adadin na buƙatar na wanko, na kinkimo ruwa da Qur'ani izu shittin. "Af na mance sai an daddaka ganyan magaryar ake zubawa." Cewar Uwani kenan. Da haanzari na ɗauko turmi na daka na zuba a cikin ruwan da bismillahi. Sai da muka kammala na samu nutsuwa har na sauke ajjiyar zuchiya. Daki na kai ruwan maganin na adana kana na fito." "To bani labarin abinda ya kai ki gidan Hajiya Salamatu, uwar shige_shige Uwani" "Wallahi Iyabo ƙasar zan bari zan tafi nemo kuɗi. Amman shekara biyu kawai zan yi in dawo" Zare idanu nayi ina dubanta da mamaki. Ƙasar fa kika ce, to aurenki da yaranki a hannun wa zaki barsu Uwani?" Ajjiyar zuchiya ta sauke tace.."Hafizu zai lura dasu Iyabo. Wannan talauci namu yayi yawa. Duk abinda Hafizu fa ya soma babu albarka sam a ciki. Kuma shi ba jari ba. Ke yanzu haka maganar da nake yi miki ma ina gidanmu fa da yaran. An koremu a gidn haya ko ince miki an watso mana kayanmu tsakiyar layi da ranar Allah. To Hafizun ma shi ya bani shawarar ko zan nemi aikatau na ƙasashe da ake zuwa, ƙanwarshi ma yanzu haka tana Canada a gidan aiki, shima in ya samu tare zamu tafi. Ni fa Iyabo wallahi tafiya zanyi. Su Hajiya ma basu san me ake ciki ba. Babbar damuwar shine ita Hajiya Salamatu tace sai dai in ajjiye dubu Hamsin da kuma ni zan yi ma kaina fasfo. In kuma ba haka ba duk zata yi mun amman zan kai wata shida kafin in gama biyan kuɗin da duk ta kashe mun. In kuma na yi fasfo na ajjiye dubu hamshin, da zaran na tafi a cikin wata biyu zan gama biyan kuɗin girji" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. To amman babu wani haɗari a cikin tafiyar dai ko. Kuma ina fatan bata ɓarauniyar hanya za'a tura ku ba Uwani, kuma kin tabbatar Shekara biyun zaki yi ki dawo, kuma zaki iya kare mutuncinki a matsayinki na matar aure, bahaushiya ƴar Najeriya, najeriyarma Arewa?" "To Iyabo ina kyautata zaton hakan. Ke kinga mata aure masu tafiya kuwa? Wallahi sun fi ƴan matan yawa, harda dattijai fa baki gani ba. Kuma ba ta ɓarauniyar hanya zamu bi ba, ta hazo zamu keta " Shiru nayi ina ɗan nazari. Kafin ince da'ita wani abun sai ga Gwadabe ya shigo akan kekenshi. Wannan dalilin yasa dole muka katse hirar tamu. Uwani tai mana sallama ta tafi. Tun daga ranar na soma ba Gwadabe ruwan addu'o'in nan safe da yamma, haka kullum sai na goge mishi jikinshi da ruwan maganin. Allah al Hakim cikin kwana na tara da rana kawai sai ƙafar Gwadabe ta motsa kamar da wasa. "Iyabo ƙafata na motsawa" Na ji ya faɗa cikin zabari. Kafin ma in ƙaraso inda yake harya miƙe tsaye. Suddajar godiya ga mahalicci mu ka yi a tare. Muna ɗagowa Gwadabe ya rungumeni tsam a jikinshi yana shafar bayana, tare da sama rayuwata albarka. "Iyabo kinga ikon Allah ko? Haƙiƙa na sake tsinkewa da lamarin Ubangiji Allah. Allah na gode maka daka bani lafiya. Ya Allah dukkanmin mai ruwa da tsaki akan wannan rashin tafiyar tawa ya Allah ka nuna mishi iyakarshi" Ni kuma sai amsawa da ameen nake yi. Ko yara da suka shigo suka ga Abbansu akan ƙafafunshi sai suka shiga murna harda tsalle. Rungumesu yayi dukkansu. Farin ciki da jin daɗi bazai misaltuba, bazai rubutu ba balle har mai karatu ya fahimta" Bara'u shine mutum na farko daya samu labarin warakar Gwadabe. Ni kuma ta ɓangarena Uwani na soma sanarma, kafin na sanar da gida. Na leƙa tsakar gida duk suna tsakar gidan ko wacce tana aikin girki nace. Ku ta ya mu murna Allah ya ba Gwadabe lafiya, ciwo ya warke" "Warkewa fa kika ce Iyabo?" Cewar Gude, kafin in bata amsa Gwadabe ya fito tsakar gidan. Ai sai suka riƙe bakinsu. "Allah ya bani lafiya haka tace. Gani akan ƙafafuna. Godiya ta tabbata ga Allah" Yana faɗar haka ya koma ciki riƙe da ƴan biyu. A masallaci abun sha'awa Gwadabe yayo sallar magriba, bashi ya shigo gida ba sai bayan isha sabida mutane sun baibayeshi ana mishi barka. Hatta su Baban Nazifi a masallaci suka haɗu da Gwadabe, kamar yadda ya labarta mun sun yi mamakin ganinshi akan ƙafafunshi. Ƙafa mai daɗi yau sai ga Gwadabe a bayan gida yana yin wanka da kanshi, Allah abun godiya ne A daren ranar Gwadabe yasha labarai sosai. Hira mu kai ta zabgawa muna murna da farin ciki. Furucin Babala yananan ɗamfare a zuchiyata ya zame mun ciwo. Na yi alkawarin washe gari zamana a gidan Gwadabe yazo ƙarshe kenan. Har yayi bacci idanuna biyu ina tunanin inda zan nufa in na bar gidan Gwadabe. Wata zuchiyar tace mun. "Ga mahaifiyarki da kike ganin kamar tana da wani ciwo a zuchiyarta me zai hana ki koma hannunta da zama. Tunda yanzu kin mallaki hankalinki?" Idanuna na lumshe wasu siraran hawaye suka gangaro kumatuna. Na jima ina karanta wasiƙar jaki kafin na daure na taso na fito falo na ɗaura alwala na soma Sallah. Bani na tsagaita da sallar ba har sai da naji kiran sallar farko tukunna. Takun fitowar Gwadabe na jiyo. Ƙura ma ƙofar ɗakin idanu nayi. Shine ya fito yana saye da jallabiyya fara. Idanu ya ƙuramun yana sakarmun murmushi me kyau da tsayawa a rai. Take zuchiyata ta sake yin rauni ainun. Ruwan hawaye suka ɓallo daga idanuna zuwa kumatuttukana. Tsugunnowa Gwadabe yayi a gabana, ya shiga share mun hawayen nawa. Abun mamaki ruwan hawayen sam sun ƙi ƙarewa. "Iyabo na yi tunanin hawayen farin cikin ganina akan ƙafafuwana kike yi ai. Amman na fahimci akwai ciwo mai raɗaɗi dake damun ruhinki. Faɗa mun menene matsalar? Naso in kwanta dake daren jiya, ko dan kewar juna da muka yi, amman na rasa gane dalilin da yasa kika kasa bani kan ki, mu raya daren da yake cike dam da farin ciki. Daren da babu daren da zai iya tureshi a ƙwaƙwalenmu" Kuka na fashe dashi mai gunji, na rasa yanda zan yi da raina. Zugi zuchiyata take ta tayi mun. Gwadabe cike ruhina yake dam da farin cikin samun warakarka. Gefen zuchiyata kuma cike da fargabar yanda rayuwata zata koma bayan rabuwarmu. Gwadabe ya zama dole mu rabu, muddin muna son juna so na gaskiya. Mu ɗauka rabuwarmu itama ƙaddarace. Har abada sonka zaita wanzuwa a cikin rayuwata, kullum sake halittar sabo za'ayi. Ta yiwu rabuwarmu ka iya kawo ƙarshen numfashina, ko ya zama silar kamuwa da wani ciwon da zai ta cin naman jikina har sai ya kaini ga kushewa. Amman Gwadabe na sani har duniya ta naɗe
Chapter 32 · 0% Book details