Sashe 200
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
ishasshe. Gaga_gaga bamu muka kammala saida ɗanwake ba sai bayan la'asar masu wanke_wanke suka kama aikinsu, mu kuma muka gyare wajen tsab ko wacce tayi wanka suka soma ficewa. Kafin magriba ɗakinmu daga ni sai Baba. Wata babbar matace, tana zaune tanata harhaɗa kuɗin ciniki. "Kina ta gani ana watsewa ko? Sun tafi yawon ɓelɓel yawon raba jiki ma mazan bariki. To rayuwace ta ƴancin kai babu makwaɓi. Nima a shekarun baya babu abinda ni banyi ba. Dan nafi shekara ashirin a garinnan. Silar auren dole ce tasa na tsallake iyayena na shigo Lagos da ƙunshin kayana a ɗankwali. mun dama duniya da dukiya, munyi cuɗanya da mutane manya sosai. Sau biyu inayin aure a garinnan zamanne yaƙi daɗi, gashi ni kuma na saba da riƙe kuɗi sai kawai kiga nayi fitowata. Amman ina baki shawara yadda kika kwaso ƴaƴa haka karki sake kice zaki yi zaman karuwanci da yara a gabanki. Kinga ɗakunan dake jere uku ta hagun ɗakinnan? Duk ɗakin yaran mata irinkine daduro sun ajjiyesu suna musu komai tamkar aurensu suka yi. Kuma fa su suna da matansu a arewa amman kuɗinsu akan waɗannan kilakan yake ƙarewa sune komai nasu. In aure mace take so ta samo miji Hajja Mama na tsaya mata ayi bikin sumul ba tare da iyayenta ma sun sani ba. Tsuru_tsuru nayi ina sauraren abun al'ajabi. Mun jima sosai tana koramin bayanin yadda ake rayuwa a Lagos. Ni dai anayin isha ni da yaran mu ka yi baccinmu harda minshari sai da duku_duku muka sake tashi da aiki. Ni da Batula kamar jiya mukaita aikin siyarma da ƴan cirani ɗumamen tuwonnan. Ga masa daga gefe Hauwa na toyawa. A cikin gidan fa akwai masu abincin siyarwa sosai, kuma ko wacce mai abinci da ma'aikatanta. Hakanne yasa gidan kullum a jaƙale ko ina ruwa, ga tulin wanke_wanke, wanda akasari mazane ake biyansu su dinga yi. "Iyabo goma fa tayi ki daure ki zauna kici abincinku kafin mu ɗaura tukunyar ɗanwake kuma. Sai munje kasuwa mu siyo yaji, yau bamu da yaji da mai. Kayan Hajja Mama basu iso daga Arewa ba.