← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 237

Sashe 65

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Jfn7qq4nyMm0prVhnhfVZK

*Ina kuke mata ƴan ƙwalisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haɗaɗɗun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Jfn7qq4nyMm0prVhnhfVZK

*Ina kuke mata ƴan ƙwalisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haɗaɗɗun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*

NAMA YA DAHU...
ROMO ÆŠANYE
LITTAFI NA BIYU
4

Baba Fhatsima ta dubeta a tsanake tace.
"Shikenan ni da kaina zan kwatanta miki yada zaki zauna daram ki wuce wulaƙanci a zuchiyar ɗa namiji. Hadiza a lokacin da Malam yace zai ƙaro aure sai da na kwanta jinya. Amman sabida kirsa irin tamu ta mata ni na haɗa akwatin da Malam ya kaima Asshi. Kuɗin dana samu a hannun malam bana wasa bane. Zuchiya kullum ciwo da zafi suke yi mun Hadiza. Wallahi inna kalli Malam sai inji kamar in ɗura mishi zagi. Amman wallahi ko ɓacin rai baya iya ganewa a fuskata. Horon da nayi mishi na ƙauracema shinfiɗarshine, tunda ya raina iyawata, sai da nasa da kanshi ya gane mahimmancina da kuma banbancina. Duk da ina fishi dashi, saina dukufa shan magunguna ingantattu, musamman tukuɗi da gumbar matan Kanuri da tsuminsu, da shayin su na musamman. Na dinga gyaran kaina dan sake kankaro mutuncin kaina. Ni kishina bana ayi zagi ko bankaura bane. Da duk tsufana Malam har gobe yana mararina Hadiza.
Sallamar su Gwadabe ce ta katse wannan tattaunawa wanda nasan ba Hadiza kaÉ—ai ke karuwa da'ita ba, harda masu karatu. Saurin share hawayenta tayi, wanda karab a idanun Gwadabe.
"Baba yinwa" Cewar Auwala wanda baya jurar yinwa. Dariya duk aka saka mishi. Baba Fhatsima tace.
"Ai kai wacce zata aureka ba zaka barta ta huta da É—aura sanwa ba" Saida ya cusa tuwo loma babba a bakinshi, tun kafin Mammada ya gama zuba musu, kana yace.
"Tabb ai ni tun da jimawa tasan Yaya nake. Kullum naje saita kawo mun shayi da cukui, wataran harda abinci fa." Mammada yace.
"Bayan uban abincin da kake take cikinka dashi kafin ka tafi? Shi yasa cikinka kullum yake ƙara girma. Baba yau daya zarme rijiyar haƙon zinariya da ƙyar aka zaroshi tsabar ƙiba fa" Duka Auwala ya kai mishi, yai maza ya matsa kusa da Gwadabe wanda shi kuma hankalinshi na kan gimbiya Hadiza da yaga tana cikin rashin walwala. Baba Fhatsima tayi Dariya tace.
"Duk ai ya kusa karewa gini kam gobe za'a soma an kawo bulo da yashi, an yi ginshiƙi. Aikin ba wani daɗewa zaiyi ba tunda an riga da an tanaji kudin aikin. Duk kuyi aurenku nima na huta" Gwadabe yace.
"Ai Baba kila fa Auwala ya dinga zamowa cin abinci ɗakinki, baya zage ya kwashi girki a gaban Amarya haka ba" haka dai sukaita raha a tsakaninsu kamar yadda suka saba a koda yaushe. Ana cikin haka Yaya Tasi'u shima ya shigo akayi hirar dashi. Kiran sallar isha ne ya fasa taron. Da Gwadabe ya tashi fita sai ya ajjiye ledar kayan kwalliyar da ya siyo ma Hadiza a gefen ƙafarta ya fita.
"Tashi kiyi Sallah kafin Gwadabe ya kiraki zance, dan zancanku ba ɗaga ƙafa. Yaran zamani kome kuke cewa in kunje wajen zancen oho. Zance ai sai su Ine yanzu dai duk ya ƙare." Hadiza tayi murmushi tace.
"Gobe ma mu kayi da Anty Badi'a zamu je gidajensu mu ganosu, tun bayan biki mu ta ɓangarenmu babu wanda yaje. Shekaran jiya Sauma'iyya suka je gidan Hafsatu."
"Daga gidan mijinta taje, ke yaya akayi kika san taje? Tsegumi" Dariya Hadiza tayi tace.
"Baba asshi ce naji tana faÉ—ama Amaryar Malam. Wai Hafsatu ta aiko mata da kuÉ—i harda soyayyun zabbi" Harara Baba Fhatsima ta doka ma Hadiza ba shiri ta tada kabbarar sallah. Dan babu abinda Baba Fhatsima ta tsana irin gutsiri tsoma" Hadiza tana kan sallayar bata tashi ba Gwadabe ya aiki yaron Amaryar Malam yayi kiranta. Sai da ta kuma gyare_gyaren kwalliyarta kafin ta fita. Baba Fhatsima tana jimantama Hadiza ranar da zata ji labarin bada ita kaÉ—ai Gwadabe yake soyayya ba, kuma akwai yiwuwar ba ma ita kaÉ—ai zai aura ba. Ko da ba'a hade bikin ba, tasan babu wani nisa a tsakani.
Fitowa tayi tsakar gidan tana busa ƙamshi. Amaryar Malam da taci kwalliyarta na zuwa turaka ta bushe da dariya, dama can basa shiri sam da Hadiza. Dan bama su wuce sa'anni ba. Ko kallonsu batayi ba. Harfa ta sha kwanar ɓarayin su Gwadabe ta jiyo Baba Asshi na cewa da Suwaiba.
"Sabida tsabar tayi bandarine fa Malam ya tafi ya ɗauko ɗan ƙanwarshi dan ya haɗasu. Ƙanwar tashi ma da bata da mutunci. Ni dai na gode Allah in Fhatsima ta fini da soyayyar miji, da ɗa mai arziki. Bata fini a surukai ba. Dan masu arzikin gaske ƴaƴana suke aure. Itako Hadiza gidan da za'a sakata ubanta nema ya bayar" karab a kunnen Hadiza, karab kuma a kunnen Baba Fhatsima. Dukkansu kai suka girgiza kawai. Hadiza tayi shigewarta ciki. A bakin dakalin ƙofar ɗakinsu yake zaune. Ga hasken lantarki tanwar ya haske ko'ina. Gardawan malam su biyar suna wajen suna wankin suturunsu, sai Sabitu dake tsaye a ƙofar ɗakinsu kawai dan babu dai Abinda yake yi. Kwana biyunanne ya tsiri yin hakan a daidai lokacin da Gwadabe zai fito ya zauna domun ganawa da Hadiza. Tun daga nesa Gwadabe yake ƙarema Hadiza kallo. Zani daya gani ɗaure a jikinta sai yake ganin kamar iyabo ce ke tawowa, dan Iyabo ta ƙware wajen iya ɗaurin zani sosai, takanyi matuƙar kyau da zani, ƙibarta na daga cikin abinda ke sa ruhinshi ke fisgarshi akan son Iyabo. Isowar Hadiza ce tasa ya dawo hayyacinshi. Zama tayi gefenshi sosai.
"Barkanka da wannan lokacin angon Hadiza mujin mace ɗaya tilo." Murmushi yayi mata kawai, a kullum in ta kirashi da mijin mace ɗaya tilo sai yaji faɗuwar gaba, haka ƙanwar tamu take yawan ce mishi.
"Mijina ni ni kaɗai. Babu wata mace data isa ta rabeka" Da sunyi mishi irin furucinnan sai yaji hankalinshi ya tashi a madadin ya samu nutsuwar kalaminsu. Anya bai cutar da zukatan ƴan matan ba kuwa, lokaci baiyi da zai bayyana musu gaskiya ba kuwa? To wai in ya zayyana musu gaskiya du suka gujeshi ya zaiyi da kunyar waɗanda yake ganin darajarsu a jikin ƴan matan? In kuma suka ritsashi suka ce sai dai ya zaɓi ɗaya, Yaya wacce aka ce tayi haƙuri zata yi? Haƙiƙa yayi kuskure mafi girma da rinjaye, awannan tunanin kamata yayi tun farko zaiyi shi, ba yanzu da wankin hula ya riga ya kaishi dare ba."
"Wai tunanin me kake yi ne Yaya tun ɗazu inata magana fa, bakace komai ba" Ya tsinkayi shagwaɓaɓɓiyar Muryar Hadiza, wanda tasa saida tsigar jikinshi ta tashi, dan wannan yana daga cikin sabon salon da take son fitowa dashi dan mallakar zuchiyar Gwadabe.
"Akwai muhimmiyar maganar da nake son mu yi ni dake. Hadiza banaso ki fassarani da ko wacce iriyar mummunar fassara, ina cikin tsaka mai wuyar fita ne, abinda yasa abinda ya faru ya farun kenan." Shiru tayi tana kallonshi da ƙananun idanunta waɗanda gashi sukaima rumfa. Bayan ta ja numfashi na daƙiƙa sai tace.
"Ina saurarenka, zanyi maka shari'ar gaskiya da gaskiya. FaÉ—amun matsalar dan tuni fuskarka ta nuna matsala zaka faÉ—a mun" Shiru yayi yana shafan sumarshi kanshi.
"Hadiza ba da ke kaɗai nake soyayya ba. Akwai ƙanwar abokina Tamu da ya bani tun kafin in tawo Nijer " Darara dam_dam_dam gabanta yai mummunan tsinkewar daya tunkudo ruwan hawaye nan take suka soma shatata a idanunta. Duk da haka tace.
"Dan Allah kace dani wasane, kar kayi amfani da kishin da akace maka shi yai sanadiyyar mutuwan aurena ya zamema logo. Na roƙeka karka yaudari zuchiyar data saba da rayuwa da sonka." Take hankalin Gwadabe ya kai ƙololuwar tashi, dan bai taɓa tunanin Hadiza zata ɗauki wannan lamarin a yanda ta ɗauka yanzu ba. Da ƙyar ya samu kuzarin ce Mata.
"Wallahi da gaske nake yi Hadiza. Kafin in tawo nan na riga dana amshi soyayyarta. To kuma da nazo nan sai Baba Magaji yace in zaɓi mace a cikin ƴaƴanshi in aura, amman sai yace yafi mun sha'awarki"
"Kenan ba sona kake yi ba, Malam kai ma biyayya? Shikenan ni na hakura kaje ka aureta" Tana gama faɗar haka ta mike fu ta bar barayin. Yayi yinƙurin tareta sai Auwala da shigowarshi barayin kenan ta gefenshi ma Hadiza ta raba ya dakatar da Gwadabe bisa dole ya tsaya."
"Koma me ya haÉ—aku kyaleta ta huce, su mata a cikin irin wannan halin baka iyawa dasu sam." Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke tare da lumshe idanunshi.
"Auwala laifi nayi mata. Tana da dalilin yin fishi dani. Laifinane, dan Allah ka bita ka bata baki a madadina"
"To wannan ma dabarace. Kai jeka bari in shawo maka kanta ka koma ciki ka jirani."
Gwadabe na shiga ɗaki kiran Shafa na shigowa wayarshi. Jiki a mace ya ɗaga wayar, itama yayi mata duk bayanin da yaima Hadiza. Ƙit ta kashe wayarta, ko da ya kuma kira sai yaji a kashe ma wayar baki ɗaya. Dafe kanshi yayi bakinshi na ɗaci, damuwa duk ta haɗu ta dameshi.
Chapter 65 · 0% Book details