Sashe 167
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
hakan. Nera dubu hamsin na ara a hannun Yaya Hamma munyi zan bashi da zaran na soma saida kaya shi zan soma ware ma kuɗinshi. Na haɗa kan kuɗi masu yawa na ba Uwani. Yaya Hamma ya bata dubu biyar na mota. Tai mana sallama ta tafi da uban man Shanu data siya a hannun Baɗɗo. Haka dai ranar ta zama ta tarihi Yaya Hamma yana gida tare dani, sai jefin azahar sai ga Yafendo da kayan magunguna ta leƙo ta bani tare da yi mun bayanin yadda zanyi amfani dasu. Godiya nayi mata. "Wannan yaro yau baka fita kiwon ba ko? Ka kyauta gara ka zauna ka kula da'ita zuwa gobe ka fita Allah ya ƙara sauƙi" Ni dai babu kunya na ƙunshe Yaya Hamma a ɗaki har sallar Isha a ɗaki yayi ta. A takaice dai sai washe gari Hama ta karɓi miji. Alhamdulillah jikina yayi sauƙi a cikin kwana biyar komai ya zama tarihi, sai ciwon laulayi mai zafi. Duk abinda nasa a bakina sai ya dawo. Madarar shanu kaɗai nake iya sha itace abincina daga tatsota in shata da duminta ko dafawa bana so ayi. Rayuwar tai ta shurawa, makarantata ta sake cika da ɗalibai, cinikin kayan yara har abun mamaki yake bani. Dan cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kayan suka ƙare. Ta bangaren Cubu laulayin nata yayi sauƙi sabida cikin ya tasa. A kullum a hidima nake da Dada duk wani abun daɗi inaba Baɗɗo ta dafa akai mata tai ta sa mun albarka, ga sutura da nake dinka mata. Amaduyal kuwa ya tsaya tsayin daka wajen kulawa da kiwo har duka shanu biyun mata suna ɗauke da juna biyu. Tumakaina kuwa du biyun sun haihu, ɗayar mai laya ta haifi yara uku, ɗayar kuma farar yaro ɗaya ta haifa jal. Haka dai rayuwar tai ta matsawa, ina cikin dangina anata zumunci inata ƙoƙarin yin zumunci dasu. Daso ce sau biyu na taɓa zuwa gidanta, dan ita tana yawan kawo ma Hama ziyara. A haka ne Yafendo ta fahimci kamar Daso ita ke rura wutar rikici a tsakanina da Hama. Sai tai ma tubkaar hanci ta hanyar sanar da Yafendona halin da ake ciki. Ita kuma Yafendo taima Daso tas tunda dama ta san Daso taso Hamma sosai, sai ta saka mata dokar ba zata hanata zuwa gidan ba amman indai tazo iyakarta ɗakin Yafendo. Gaga_gaga anata cuɗa rayuwar. Yau kwanciyar hankali, gobe akasin haka. MRS BUKHARI