← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 237

Sashe 157

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

ba zata dawo ba saiya sake mata kayan ɗakinta kab. Sai garashi take yi sunata cin kuɗinshi" Jim nayi ina nazarin maganganun Baɗɗo. Kullum sai yaje wajen Hama? Maza mutananmu kenan. A zahiri nace. "Ita Dason dawa take wannan hirar?" "Da Sadiyan Yafendo A'i suke hira. Har tana faɗa mata wai hatta dukan Hama da Adda Uwani tayi ashe sai da Yaya Hamma ya ba Hama dubu goma wai kuɗin magani" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Hmm wannan a wajen namiji ba komai bane Baɗɗo. Babu komai. Ina mamakin yadda Daso ƙiri_ƙiri ta zama maƙiyiyata akan kawai Yaya Hamma." Zuwa bayan Isha su Baɗɗo duk suka watse bayan sunci tuwon biki, yaran ma Yafendo ta kama hannunsu suka tafi tare Tuwon da nayi ma sai dai su Dada su ci da safe dan ko buɗeshi ba ai ba, sun samu na gidan biki mai nama. Ni dai ina tsakar gida jigum nayi zurfi a cikin tuntuntuni sai ga sallamar Yaya Hamma. Ɗagowa nayi na kalleshi, shima ni ɗin yake kallo. Sai wani murmushi yake yi mun. Ni kuwa haushi murmushin ya ƙaramun. Sannu da zuwa" Iyakar abinda na ce dashi kenan. Sai ya sha jinin jikinshi, ya fuskanci raina a ɓace yake. "Dada fa?" Tana ciki, yanzu ta shiga" Sai ya kutsa kai cikin ɗakin. Ya daɗe a ciki kafin ya fito yace in taso muje. Sallama nayi musu na bishi muka tafi. Tun fa a hanya yake magiyar in faɗa mishi menene ya ɓata mun rai. Amman amsa ɗaya nake bashi cewar babu komai. A haka har muka iso gidan. Matan gidan suna tsakar gida, tare da matan maƙota da nake ma karatu. Suna ganina suka soma murnar ganina. Haƙuri na basu akan sui haƙuri sai gobe zamu yi karatu, duk na sallamesu suka tafi gidajensu. A ɗakin Yafendo na samu Yaya Hamma tana mishi maganar Hama. Da naji haka saina gaisheta na fice abina na jirashi a ƙofar lungunmu harya iso muka shiga. Ina shiga ɗakin sai gabana ya yanke ya faɗi haka. Cikin dauriya muka sha tea da balangu da masa dai mu kai shirin kwanciya. Baccin da bai yiwu ba kenan fa. Irin na daren jiya sai abinda ya ƙaru dan ɗakin har jijjiga naji yanayi ƙasa na zubowa. Wannan yanayi sai ya zame mun jiki, ni da bacci sai na rana, kuma sai dai in wuni a tsakar gida ko wajen Yafendo dai. Mu'amalar aure ba sai ta gagara ba. Sai mun haɗu zuwa gobe kuma✍🏻 Mrs Bukhari
Chapter 157 · 0% Book details