← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 237

Sashe 81

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

*Ina kuke mata ƴan ƙwalisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haɗaɗɗun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
Masu neman ƙarin bayani saiku tuntuɓeta
07082649563 whats app number kira 07036028230
NAMA YA DAHU....
ROMO ÆŠANYE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

9
"E ya sani, harma ya bani kuÉ—aÉ—e yace inna tafi kar in dawo dan in matarshi ta fahimci shi yaimun ciki zata kashemu dukka" Dariya Hajiya Babba ta kwashe dashi ta É—auki waya ta daddanna, jim kaÉ—an ta soma larabci tana faÉ—a ta inda take shiga ba tanan take fita ba. Ajjiye wayar tayi tana tsaki.
"Ku tashi ku bani waje, yace zai kawo miki maganin zubar da cikin zuwa gobe. Sai ki zauna da shirinki. Ke kuma zan duba lamarinki, ku tashi kuje" Ni na tallafama Uwani ta miƙe jikkunanmu a mugun mace, haka wunin wannan ranar ya kasance mana cikin tubka da warwarar al'amura. Yaya Hamma na tuno da irin kishinshi. Take na lumshe idanuna hawaye suka gangaro mun. Yarana na kuma tunowa da ubansu. Take murmushi ya suɓuce mun. Takaddar da Khalifa ya bani na ciro a ledar kayana na farketa. Kuɗine sababbi suka zubo masu yawa a mimmiƙe. Uwani ta dubeni tace.
"Wannan kuÉ—aÉ—en fa Iyabo?"
Hmmm Saurayin da nake faɗa miki Khalifa na gidan da nake shine ya bani da suka saukeni a ƙofar gidannan. Uwani baki bani labarin wuyar aikin gidan larabawa ba." Ɗan murmushin dole tayi mun tace.
"Sawun giwa ne ya take na raƙumi. Amman duk wata azaba ta tabbata a aiki a gidan larabawa. Wuni guda cur mutum a tsaye kamar jaki. Sallah ma sai kayi da gaske kake ƙwacewa kayi. Iyabo abun babu sauƙi ni duk ƙasar ta isheni gida nake son komawa. Hafizu kuma baya nan yana can Canada ko a wanne irin hali yake sai Allah. Dan ba mui waya dashi ba hajiyarmu ce take faɗa mun. Sai hankalina ya koma gida. Ya kamata ki kira Burodami Debisi kema ai." Baki na taɓe nace.
Wannan rayuwa cike take da ƙalubale Uwani. Sai yanzu nake dana sanin ƙin bin shawarar Yaya Hamma da Burodami. Yaya Hamma har shanu ya siyar ya bani jari in dinga zuwa kano ina sare_sare amman wallahi naƙi fur, sabida ni manyan kuɗi nake hari. Uwani shekara na zagayowa ni dai zan tafi gida magana ta gaskiya, da dai na samu ƴan kuɗaɗen juya kasuwanci, da ɗan kuɗin da zan saima Dada ɗan gidan da zata zauna shikenan ni daman ba wani abun nake nema ba. Bani number Burodami in kira ko zan sameshi" Jakarta ta buɗe na hango kuɗi sosai a saman jakar, takaddar da na rubuta lambar ta miƙo mun, na daddana number, na kira ta ƙaraci ringing babu wanda ya ɗaga, na sake gwadawa bata sauya zane ba.
Anƙi ɗaga wayar Uwani, zuwa gobe na sake gwadawa .
Washe gari da safe muna kan karyawa sai hira aketayi a ɗakin. P.a ce ta leƙo tai kiranmu baki ɗaya ni da Uwani.
"Tashi muje Iyabo. Kinsan halin almurar matarnan bata da daɗi sam." Tashi nayi ina lashe hannuna muka je muka sameta da wani mutumi a zaune a kujera. Ashe shine wanda yaima Uwani ciki. Magani Hajiya Babba ta miƙo ma Uwani a farar leda. Jikinta na rawa ta amsa.
"Ga maganinan na zubar da ciki. Ɗaya zaki sha, sai ki tura biyu gabanki. Ki jirayi zubar jini minti talatin da sha. Sannan ya bada kuɗi wanda har yafi ƙarfin kuɗin da nake binku ke da ƴar uwarki. Amman ki sani sisin kwabo ba zaki gani ba, wanda ya baki ma in kika bani haɗawa zanyi in karɓe. Ku shirya Zan mai da ku Jidda kuci gaba da zama. Dan yana buƙatar kiyi nesa da garin da yake, dake da wanda ma ya sanki. Dan haka kuje ku ɗebo kayanku yanzu mu wuce, kamfani bata binku ko sisi, sai kuje ku nemi kuɗi a Jidda." Kasa magana mu ka yi dan takaici, da mamakin zalunci irinna Hajiya Babba. Haka muka ɗakko kayanmu, mu kai Sallama dasu Hadiza, nan muka kama hanyar Jidda.
A wannan gida na Jidda anan muka ga abubbuwa na tashin hankali, anan muka ga masu ciki iri daban daban. Yaranmu sun zama wasu ƙananun ƴan iska, yarinya ƙarama da buɗaɗɗen idanu. Sai girke_girke wasu daga cikinsu suke ta faman yi. Abun mamakin ma abincin gida Najeriya suke dafawa, dangin dambu, shinkafa da wake. Can gefe kuma ga wasu tsofaffin mata sai ƙulla gyaɗa soyayya da aya suke yi. Sai yima Hajiya Babba sannu da zuwa suke yi. Ni dai ina riƙe da hannun uwani dam. Duk inda Hajiya Babba ta cire ƙafa anan muke ɗora tamu har zuwa wani ɗaki mai cike da kayan more rayuwa. Sai wasu dilolin kaya a zube a tsakar ɗakin da halama na siyarwane. Wata tsohuwar ƴar duniya muka tarar a kwance tana waya sai zabga larabci take yi tana dariya. Bayan ta ajjiye wayar ta dubi Hajiya Babba tace.
"WaÉ—annan sune matan da kika ce zaki kawo É—in" Hajiya Babba tace.
"Gasunan kin gansu. Duk abinda kike ganin ya dace a kansu ki zartar kawai. Kinga me juna biyun ita dai za a iya jefata a kasuwanci dan Abu Khadija ya faɗamun ya bata wadatattun kuɗin da zata lura da lafiyarta. Ita waccan ko gidan aiki ne sai ki jefata, Allah bashi in ta tara kuɗinta ko kasuwancin tura kaya Najeriya ne sai ta soma itama. Tunda dai sun biya kamfani kuɗinta. Ga fasfo ɗinsu nan" Ta zuge jakarta ta ciro ta miƙa ma wannan mata. Kallonmu tayi tace.
"Ke me juna biyu, kina da sha'awar kasuwancin tura gumama gida Najeriya ire iren dogayen riguna haka?" Ta nuna mata na zube a tsakar É—akin. Kana ta É—aura da cewa.
"Harkace mai riba sosai, domin a Najeriya da tsada ake siyen dila. Da sai ki soma ko da da dila ɗaya ne kina turawa gida. Da zaran kinga harkar ta karɓeki sai ki dulmiya kuɗi a dama dake. Ga harkar zannuwan gado, ga harkar barguna ma itama tana tafiya( Anty Zee me zanin gado ana magana) ga atampa ƴar leda matan Najeriya na sonta sosai." Uwani dai ita damuwarta cikin dake jikinta ne, kuma a zahiri tana son taimakon iyayenta sosai. Kuma tasan mahaifiyarta ƴar kasuwace zata tsaya tsayin daka ta siyar da kaya in an tura mata yadda ya kamata.
"To Hajiya kamar yadda kika ce sai in soma da dilar gumamar mu jarraba. Itama ƙawata bata buƙatar gidan aiki. Tana da kuɗi inma ba zasu isa ba, in nawa zai kai a sai mana dila biyu shikenan sai a siya mana. Mahaifiyata zata dinga siyar mana ana turo kuɗi muna tura wasu kayan." Hajiyarnan tace.
"To da zafi _zafi ake dukan ƙarfe tunda dai da kuɗaɗenku dilolima akwaisu iri da kala a gidannan. Zan kaiku ku zaɓa sai ayi batun kuɗi. Sabida jirgin kayan ana ɗan samun jinkiri zaki ga bai isa da wuri ba. Kuma za a iya saro muku kaya daga can gida Najeriya kuma kuci kasuwarsu. Zaku fi ganin afkin kuɗin."
Nan dai Uwani ta fito da kuɗi aka haɗa da nawa duk muka ɗungume kuɗi muka bata. Ashe wannan shine somin shigarmu cikin tarin tulin matsaloli. A taƙaice dai ashe damfara ce kawai Hajiya Babba ta haɗa domin ta karɓe wannan kuɗi da shi Abu Khadija da yaima Uwani ciki ya ambata mata ya ba ita Uwani. Gashi a gidan haya ake biya, kai zaka sai abinci da kuɗinka, kai zaka sai sabulun wanki da abun goge baki."
Uwani dai tana kwance tana jinyar jikinta dan ta sha ciwon cikin da harna fidda rai da ci gaban rayuwarta. Cikin hikimar Allah kuma sai ya tashi kafaɗunta a cikin kwana na goma da zuwanmu gidan. Abinci bashi nake karɓa mana a wajen masu abincin gidan. Ƴan cirani babu irin waɗanda babu a gidan. Har mabarata mata da ƙananan yara akwai. A kwana na goma sha biyu sai gani a titi ina faɗin sabil_sabil ina kuka. Hajiya Zuwaira macece maras mutunci da rashin tausayi a hakan tazo take tambayarmu kuɗin hayar ɗaki wai kwana goma_goma ake biya. Watsi tayi mana da ƴar jakar kayan namu. Sai Fati wata yarinyace ta taimaka mana muka dawo ɗakinta.
"Sai fa haƙuri. Amman me zai hana ku nemi gidan aiki. Tunda dai ba zaku iya irin rayuwar da mu muke yi ba, muma ƙaddara da wahalar aiki a gidan larabawa ne ya ja mana, kuma sai ka fi shekara nawa baka tara wani abun arziki ba. Ai ina ganin zai fi muku ko?" Ina sharar hawaye nace.
Na amince zan tafi gidan aikin Fati. In shekara ta zagayo sai mu koma ƙasarmu abinda muka tara Allah ya amfana." Nan muka amince Hajiya Zuwaira ta sama mana gidan aiki. A can wani gari me nisa. Ni na soma tafiya wannan karon. Gidan wasu tsofaffin miji da mata aka kaini. Gidan akwai tarin aiki, ga tsofaffinnan da tsari, gasu da yawan yin baƙi. Haka na kama aiki ka'in da na'in kullum mafarkina bai wuce in buɗe idanuna in ganni a gida Najeriya ba. Ga dakon soyayyar Yaya Hamma da zuchiyata take ta faman ɗawainiya dashi. Duk tarin gajiya da tarin matsaloli daidai da sakan zuchiyata bata taɓa barin tunanin Yaya Hamma ba. ( Ina kira ga mata masu tsallake ƙasarsu su tafi wata ƙasar da zummar yin aiki. Ku sani in kinga wata taje ta samu kuɗi baki san irin sana'ar da take yi ba harta samu wannan kuɗin ba. Wasu har rasa rayukansu suke yi. Wallahi babu iriyar azabar da ba'a ganawa waɗannan mata masu barin ƙasarsu zuwa wata ƙasar. In baizo kanki bane kawai zaki ga kamar duk waɗannan abubbuwan basa faruwa. Amman akwai da yawa waɗanda suka shiga tarin matsalolin daya dama na su Iyabo ya shanye. Amman fa bance ba'a dacewa ba. Wasu suna iya zuwa saudiyya su ƙaraci rayuwarsu a gidan aiki ɗaya ba tare da sun sake ba. Kuma in har za a rabu ma kiga iyayen gidan sunyi ma ƴar aiki kyautuka na alfarma. Ƙalilanne masu dacewa da hakan. Da yawan yaranmu in suka tafi lalacewa suke yi su shiga harkar banza. Ke uwa, ko miji kuna gida gaho damuwarku ayi muku gini, a dinga turo muku kuɗi. Baku damu da halin da yaranku suke ciki ba. Kuma da yawan agait agait ɗinnan da yawansu basu da kirki cuta da ha'inci kawai suka saka a gaba. Da kin taɓasu sai suce suma hakan akayi musu. Ƙalilanne daga cikinsu zuchiyarsu take a tsabtace.)
Gaga_gaga haka rayuwar tayi ta faman tafiya. Aiki kamar zai kasheni. Ba hutu, ga ciwon baya mai tsananin gaske da nake fama dashi. Musamman wayewar garinnan ta yau. Nama kasa miƙewa sallar asuba ma sai a zaune nayi. Gashi uwar ɗakina yarinyarta dake aure a Madina suna gidannan ita da yaranta huɗu tazo duba mahaifiyarta. In miƙe tsaye fa na kasa. Wallahi Allah sai da rarrafe na samu na fito. Ina ganin Uwar ɗakina na fashe da kuka nake cakuɗa mata larabci ina kwatanta mata zanje gida bayana ba lafiya. Hankalinta ya tashi. Take ta taso ƴarta aka ɗaukeni zuwa gida. A lokacin watana biyu da zuwa gidan kenan. Da ƴan kuɗaɗena a lalita dasu nake kwana kuma dasu nake tashi.
Fati ce ta samu tawul da ruwa ta dinga dannamun bayan nawa, wanda a wannan lokacin har kumburi yayi. Ta mulke mun bayan da man zafi. Sai sannu wani ɗan daudu yake yi mun ƙawar Fatyne.
"Subhanallaah ni kam ku rufa mun asiri kar ki mutu muna ɗakinnan ki jaza muna jafa i" Haƙorana suna kakkarwa nace dashi.
Dama mutuwar zata zo ta É—aukeni kaga shikenan nima na huta." Sai yayi shiru, can kuma yace .
"Kinma ci abinci kuwa" Kai na girgiza mishi halamar A'a.
"Kawo kuÉ—i a haÉ—o miki tea ki É—umama cikinki, sai a É—an haÉ—o miki da farfesu" Gudun kar susan akwai kuÉ—i a jikina, domin na fahimci rayuwar Saudiyya ba wanda yake yarda da kowa sai nace.
Faty Ki ranta mun, dana samu dama_dama zan baki kuɗinki dan Allah" Cikin minti talatin sai gata da shayi me kauri da farfesun kaza, naci sa a na samu naman ƙirji. A daddafe na sha farfesun, na haɗa da tea. Magungunan ciwon jiki ta ɓaɓɓallo mun na watsasu. Cikin ikon Allah sai bacci ya ɗaukeni. Bani na farka ba sai da duhu ya rufa, dana miƙe tsaye sai naji da dama inji mutan nijar suka ce da dama. Alwala na ɗauro a ƙaramin toilet dake cikin ɗakin. Raak'a ɗaya na iyayi a tsaye, dana yi ruku'u kasa ɗagowa nayi sai zarcewa sujuda nayi, sabida ji nake dana tankwara bayan wani ƙashin ka iya ɓallewa in shiga uku.
Chapter 81 · 0% Book details