← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 237

Sashe 7

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A game da abinda ya faru a gida can Kano ne kafin mu tawo. To da Yaya Hambali, da su Yaya Harisu duk sun amince akan Yaya Hambali ya tashe mu a gidanshi mu yi nesa dashi. To Babala tace dai a barta tayi shawara da su Goggo Iyatu. To kinsan Goggo Iyatu kusan ita take sake zuga Babala akan ki. Sabida Laila ƴar wajenta da Allah bai yi mun yi aure ba kamar yanda suka tsara tun muna tsumman goyo. To kinji abinda ya ɗaga hankalina kenan, tunda nasan bani da kuɗin da zan iya kama mana ko ɗaki ɗaya, balle ciki da falo." Ƙur na zuba mishi idanu. Gwadabe duk abinda Allah yayi a kan mu me kyau ne. Allah ba zai ba danginka ikon tozarta mu ba da ikon Allah. Kayi haƙuri jarumina duk a akaina ake yi ma hakan." Murmushi yayi gwanin tausayi yace. "A tunaninsu matsa mun lamba da zasu ci gaba da yi, shi zai sa aurenki ya sire mun. Billa aurenki kullum sake zame mun yake yi kamar yau aka ɗaura iyabo na. Kema ki ƙara haƙuri wata rana sai labari . Sannan ina da babban albishirin da na cancanci garjejen farin goro ɗan shagamu. Allah ya nufa nima na zama matuƙin Babbar mota na tashi daga karen mota. Ma'ana an mallakamun mota." Sakina ce ta shigo hannunta riƙe da langa da kofin silver ta dure shi a gabana. "Sakko ki ci abinci ki yi wanka mu samu mu koma gidan biki, yau biki zai ƙare Amarya zata kwana a ɗakinta" Godiya na yi ma Sakina. "Gwadabe Bara'u yana ƙwar gida wai kaje ku tafi" Da sauri ya miƙe, mu kai sallama ya fice dan yanzu za'a ɗaura auren ƴar autar tasu. Ni ko a gurguje na karya na yi wanka zuchiyata fal murna na san a ƙalla zamu samu sassauci daga talaucin dake addabarmu. , Sakina ta yi ma Toye wanka. Leshin ankon bikin Bose da mu ka yi wata shida daya wuce na saka. Leshi ne me tsada, dan ko sanda aka fitar da leshin na cire raina da yi, amman Gwadabe sai da ya je ya ciyo bashi yai mun domin ya fitar dani kunyar dangina, leshin ya sha ɗinkin buba da zani, na saka sarƙa fashion me kyau wacce Gwadabe ya siya mun a legas da suka je. Mayafina da takalmina ma sababbine wanda matar Tamu ta aiko mun daga Habuja, da naso in bari sai na haihu in yi fitar suna dashi. Gwadabe ne ya ƙi yarda yace lallai sai dai in sa a bikin gidansu nima in fito da kyau, dan su Yaya Haula suma sun yi ɗinke_ɗinken biki kala uku_uku. Ni kuma bamu da kuɗi leshin da na sa basu san na ɗinka ba, tunda mu ka yi bikin na ɓiyeshi a ƙasan akwati abunka da tattali irin na talaka. Fitowa nayi shar dani har ƴar hoda da jan baki na murza. Toye kuma riga da wandon Atampa na saka mishi da hular ashoke irin na yarenmu. Sakina ta riƙe mishi hannu muka nufi gidan bikin. Ƙofar gidan taƙi wutuwa sabida tsabaragen dandazon maza ƴan ɗaurin Aure, sai maƙota muka faɗa akan in an sassauta ma shiga cikin gidan. Sai wajajen kusan azahar ƙofar gidan ya sarara da mutane muka samu muka shiga cikin gidan. Da Laila na soma haɗa idanu, sai naga ta shiga ƙarame kayan jikina kallo har kirjinta na hawa da sauka irin na tashin hankali. Ni mamakine ma ya kamani. Ban bi ta kanta ba kai tsaye shiyyar Babala na wuce domin in sake gaishesu. Kowa na cikin ɗakin kallona yake yi baki a sake, Yaya Haula kuwa tsabar kallona da ta shagala tana yi sai da ta zuba ruwan miya a ƙafarta mai zafi kafin ta dawo hayyacinta. Koddibuwace babba a jikinta, amman leshina ya tsole mata idanu. Yaya Halima kuwa wuyana take ta kallo kawai. A tsarge na gaggsishesu bi da bi, suka amsa a daddaƙile in da sabo na riga dana saba tuni. Na ɗan zauna jim sai ga Amarya ta shigo ɗakin ita da ƙawayenta su su biyu. Ta tsugunna ta gaisa da kowa amman kallo wannan ban isheta ba. Sauwama Amarya an sha kyau" na ce mata ina ɗan yaƙe. In kun tanka yarinyarnan ta tanka. Abunda ya kawota ta yi ta fice da ƙawayenta. Bayan na zauna kamar na awa ɗaya haka sai na koma tsakar gida, dan naga atana alwalar sallar azahar. Ɗakin ƙanwar mahaifiyar Sakina anan nayi Sallah, mu ka ci tuwo da Sakina, na koma tsakar gida muka shiga rabon tuwo ka'in da na'in. Ban zauna ba sai da aka gama rabon abinci kab tukunna. Zuwa bayan laa'asar kuma dangin ango suka tawo da fantimotin aure, daga nan kuma zasu tafi da Amarya. Ayarin su Asiya na bi mu kai ta fita da kayan ɗakin Amarya ana sakawa a mota. Su Yaya Haula da Zuwaira harda su a ƴan kai Amarya, mutane sai da suka cika Bus guda, sai ƙaramar motar Amarya da ƴan ƙawayenta. Muna shiga cikin gida muka tsaida sanwar tuwon dare ba mu muka nitsa ba sai wajen takwas na dare, sai lokacin na samu kaina na galabaita sosai, marata ciwo take yi mun tun rana haka na kwana da ciwon marar nan. Da sassafe muka kuma tashi da aikin gyaran gida da karin kumallo. Kokko da ƙosai mu ka yi, bayan an kammala karyawa baƙi suka shiga haramar komawa garinsu, sai wanka akeyi. Sai da mu ka yi wanke_wanke muka share wajen tas kafin na samu bokiti na samu ruwan wanka mu ka yi ni da Toye. Gwadabe ne ya neme ni a tsakar gida ya same ni. "Ki hanzarta ki shirya yanzu zamu kama hanyar Kano. Ana mun lodi a mota zamu kai kayan Legas." Ajjiyar zuchiya na sauke nace. A shirye nake ni kam tsab. "To ki shiga ki yi sallama da matan gidan, sai ki same ni a ɗakin Babala" Yana faɗar haka ya juya da sauri. Ni kuma na shiga bin ɗakuna inai musu sallamar zamu koma, har na iso ɗakin Babala na shiga da sallama. Su Yaya Hambali duk suna ɗakin, waje guda na samu na raɓe. Babala dake magana taci gaba da magana. " Kai wannan yaron ka yi haƙuri ka bar Gwadabe ya zauna a tare da ku. Dan ina buƙatar a dinga sa mun idanu akan dukkan motsinshi. Amman ya dinga biyanka haya a shekara, in yaso sai ka kama shago da kuɗin ka dinga tara dabinon naka a ciki. Kai kuma Gwadabe duk shekara ka dinga bashi nera dubu ashirin kuɗin hayar ɗakinshi. Dan in ma baka bashin ba akan matarka zai ƙare. Gara ka ba ɗan uwanka dan babu irin hidimar da bai ma rayuwarka ba. Shi ya cicciɓaka har ka kai wannan matsayin. Ke kuma Iyabo zan gargaɗeki duk randa kika sake yi musu gwale a tsakar gida, ni na basu umarnin su watso miki da kayanki waje. In shi kin shanyeshi sai abunda kike so yake yi, to ni na sha tabara na sha yaseen ke har da lahaula duk na haɗa na sha na fi ƙarfin Oremi ma uwar bokayen yarbawa balle ke karan kaɗa miya. Ni dai kaina na ƙasa numfashi mai ƙarfi na saka fesarwa, in tashi in fita ina jin tsoron fassarar da zasu yi mun, in ci gaba da zama zuchiyata ta buga, hawaye na soma zubarwa. Yaya Hambali da su Harisu ransu yai fari fes dan jin irin hukuncin da Babala ta yanke mana. "To Shikenan Babala dan kin sa baki ne zan barsu su biya haya, amman da ko hayar basu isa na basu ba, dan dubu ishirin ɗaki ɗaya zai iya kama musu. Babala ki faɗa mishi na bashi sati ɗaya ya biya kuɗin haya, dan haya zata soma daga yau. Ban yarda kuma a sake sa mun kaset ɗin yarbawa a gidana ba." Ni sabida tsabar mamaki daskarewa nayi a zaune ina jin ikon Allah. Gwadabe kuwa kasaƙe yayi in wannan yayi magana sai ya juya ya kalleshi, har sai da suka gama maganar tsab yace. "To na ji Babala zan dinga biyan kuɗin hayan kamar yanda kika gindaya mun in sha Allah. Yaya Hambali kayi haƙuri a bisa dakatar da kai da na yi. Kuma in sha Allah in akwai wata doka ma da kakeson gindaya mana, zamu yi ƙoƙarin ganin mun bi, ai kai ubane ba wa a gareni ba. Babala shikenan inason mu tafi ana ma motarmu lodi legas zan wuce a yau ɗinnan?" Babala ta yi murmushi tace. "Me kake ci na baka na zuba, yanzu zan sallameku ai." Baki ta kada ta kira Laila har sau biyu kafin ta amsa daga uwar ɗakin Babala. Fitowa tayi tana wata irin tafiya ta jan hankali. Kallonta nayi inason in karanci yanayinta, ita kuma idanuwanta akan Gwadabe suke. "Kin gama haɗe kayan tafiyar naki dai ince?" Babala ta tambayeta, sai da ta yi murmushi har da sin da kai kafin tace. "Na gama haɗawa tun jiya Babala" "To ki fito da fantimotanki zaku wuce yanzu ko?" Laila ta kalleni muka haɗa idanu kafin ta koma uwar ɗakin. Babala kuma tace da Gwadabe. "Ga Laila zaka tafi da ita ta zauna a hannunka. In kun daidaita kanku falillahil hamdu, mu haka muke so dama. Kai na ɗauki amanar Laila na ba, sai ka kula da'ita yanda ya kamata. Ka kuma tuna ƴar uwarka ce, gyatumarta ni na saki nono na bata" Ba ƙaramin razana nayi da jin wannan zance mai kamar saukar aradu ba. Meke shirin faruwa dani ni Iyabo a wannan karon? Ta ya za'a bamu riƙon gansamemiyar bazawara irin Laila. Lailan da ada mijina ita zai aura, kuma har yanzu data fito naga son Gwadabe a idandunanta. Tabbas an shirya hakanne dan a nuna mun iyakata, ai mun kora da hali. In zan iya ɗaukar duk irin samfurin wulaƙancin da dangin Gwadabe suke yi mun, bazan iya jurar wannan ba, tabbas sai dai Laila ta mayema Gwadabe gurbina dan tafiyata zanyi gidanmu, abun ya isheni haka" "Babala taya zan iya riƙon Laila ina ƙarami alhalin ga Yaya Hambali, ga Yaya Harisu, sannan ga Sukairaju. A tunanina su yafi cancanta su rike Laila tunda sune a gaba dani. Sannan Babala..." "Ya isheka nace. Na riga da
Chapter 7 · 0% Book details