Sashe 49
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
wata matsalar ta ƙannen miji, wata jarabawarta maƙotane marasa ƙaunarta irina. Wasu dangin mij, wasu matan maƙota, wata ma abokin mijina, ko matar abokin mijinta sune matsalarta, banda kishiya da shegiya facala su ba'a lissafinsu ma. Na tausaya ma Dada aimun. Kuma ya kamata ku yaranta ku haɗe kai lallai ku nema mata takaddarta. Iyabo amman ramar da kika yi da sauyawarki ta ban tsoro" Hawayena na share. Uwani ƙauyene fa sosai can inda na koma. Babu ruwan famfo, sai wata rijiya guda ɗaya jol anan ake ɗiban ruwa, ba wutar lantarki, babu sabis ɗin waya, ba titi, amman suna da makaranta, sai dai al'ummar cikin ƙauyen aikinsu kenan kiyo, matansu kuma tallar Nono, suna da ƙarancin ilimin addini, ai dole ki ganni haka. Kuma jinya nayi magashiyyan sai an ɗaga sai an ƙwantar" Mun jima muna tattaunawa, sai da mu kai sallar isha mu ka ci abinci sannan Uwani ta zura mayafi muka nufi gidan Hajiya Salamatu. "To naji bayaninku. Amman Uwani kin mata bayanin komai da komai dai ko?" Cewar Hajiya Salamatu tana hakimce taci gwala_gwalai kunne da wuya, da tsintsiyar hannu. "E Hajiya na yi mata bayani. Sai dai itama bata da kuɗi kamar dai ni. Amman Hajiya in muka je can za'a cire a kuɗin aikinmu har mu gama biya. Mu ba ma daɗewa zamu yi a can ba shekara uku ya ishemu, dan da ita Iyabo shekara biyu ma tace" Hajiya tayi dariya tare da girgiza kai. MRS BUKHARI