← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 237

Sashe 52

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

GWADABE:.
Bayan saukar su Baba Magaji a abun hawan da suka hau zuwa layin Ali ɗan tsoho. Duk inda Baba Magaji ya sauke kafarshi nan Gwadabe yake ajjiye tashi turyan_turyan har zuwa ƙofar gidan Baba Magaji mai ɗauke da cikowar almajirai yara da ƙananu. Almajiran malam suna hango malam magaji, wasu gardawa biyu suka taso suka nufo su.
"Malam maraba da dawowa sannu da zuwa baƙo? Malam baƙin gaddi mu ka yi ne" Baba Magaji yayi Dariya ya dafa wanna gaddi yace.
"Ba baƙin gaddi bane. Ɗan wajen ƙaunata ne cikin ummata. Amman da dare zai zauna ya dinga biɗar karatu, da kuma Asuba. A karɓi jakar hannunshi ku shige dasu wajen Fhatsima." Gwadabe ya bi bayan Gaddawannnan biyu har zuwa cikin gida. A tsakar gida suka tarar da matan malam Magaji su hudu reras ko wacce da abinda take yi. Haka yan matan gidan, wannan na sukola, wannan na girkin abincin siyarwa, wannan na dakan fura, duk dai gasunan.
"Almu baƙi mu ka yi ne, cewar Baba Fhatsima. Wanda ta kira da suna almu yace.
"Malam ne ya tawo da shi ya. Kuma yace mu kawo shi wajenki." Fhatsima ta yi murmushi tace.
"Yaro shiga wannan ɗakin ka zauna. Ke I'ne zo ki kai ma baƙo ruwa ya sha" Gwadabe har ƙasa ya durƙusa ya gaishe da matan Kawun nashi. Babu dai yabo babu fallasa suka amsa mishi, cikin su ukun babu wacce ta yi mishi kallon arziki. Baba Fhatsima tace.
"Tashi yaro kaji ka shiga daga ciki, za'a kawo maka ruwa" Jakar Baba Magaji ya amsa a hannun Almu da ɗan kunshin kayanshi kala biyu wanda Bara'u ya ƙunshe mishi. Ɗakin ya shige da sallama. Wata budurwa tana kwance a ƙaramin gadon bono ta juya bayanta ta yanda mai shigowa ba zai ga fuskarta ba. Kayinta babu ɗankwali sai baƙin madaiaicin gashi mai walƙiya da yai ma kan nata ado. Ba gashi bane mai yawan daya wuce misali ba. Gashi ne wanda bai ko kai tsakiyan bayanta ba, iyakarshi gaba da kafadunta kaɗan. Gashin dai ya sha gyara sai walwali yake yi. Gwadabe ya ɗauke idanunshi daga kallon gashin ya bi ɗakin da kallo, ɗakin ya sha labule mai ɗawisu zagaye da bangon ɗakin dukka. Ga ɗan katakon kwalliyar labule zagaye da ɗakin, a saman labulen an yi jeren kwanukan sulba ƙananu sai ɗaukar idanu suke yi. Ga gadon bono ga gado mai rumfa maulidi, ko wannne gado ya sha lallausan zanin gado mai geza da heart a tsakiya. Kasan ɗakin kafet ne ja mai kwalliya malale takota ina. A gefen gadon bonon an ajjiye babban tulun ruwa mai fenti, an rufe bakin tulun da faifayi. Ga wasu manyan kumbuna da kwallaye anyi ado dasu, banda wata kwaba mai ƙofofin tangaran ita kuma kwabar an ƙawatata da kwanuka da fileti na tangaran nau'i daban daban. Sallamar da Gwadabe ya ji ne yasa ya nutsu ya dena ƙarema ɗakin kallo. Wata farar doguwar yarinyace ta shigo, hannunta riƙe da kofin sulba mai murfi ƙato. A gabanshi ta dure kofin, ta zauna harda lanƙwashe kafarta kamar mai ɗaukar karatu.
"Ga ruwa Yaya ka sha kafin abinci ya nuna sai ka ci" Murmushi Gwadabe yayi mata.
"To nagode ƙanwata" Kofin silban ya buɗe ya kafa bakinshi a kofin ruwan ga sanyi, Gwadabe sai da ya sha fin rabin kofinnan kana ya ajjiye ya rufe kofin.
"Gidanku Malam ya je, ko kaima almajirci kazo yi?" Ta jefo mishi tambayar, kafin ya bata amsa suka jiyo ana kiranta.
"Ine ke dibo fito ku tafi ga musa mai baro yana jiranki" Zumbur ta miƙe ta dubi Gwadabe tace.
"Zan fita tallen abinci, amman ba jimawa nake yi ba. In na dawo ma ƙarashe hirarmu" Da idanu Gwadabe ya bita kawai, ta fita cikin hanzari. Tana fita Baba Magaji ya shigo, Baba Fhatsima na biye dashi. A ƙasa Baba Magaji ya zauna, Baba Fhatsima kuma ta zauna a bakin gadon bono.
"Fhatsima kin gane ɗana Gwadabe kuwa, ɗan wajen ƙaunata Babala, yaro mai yawan ƙuraje?" Baba Fhatsima tace.
"Ohh naji naji, shine haka ya zama babban mutum haka? Oh Gwadabe rabona da saka ga idanuna shekara talatin baya, kana yaro kyatunarka na yawan kawo mana ziyara a lokacin kana goye a bambunta" Gwadabe sai murmushi kawai yake yi yana sinne kanshi ƙasa. Wata budurwace doguwa itama mai jiki ta shigo hannunta da kwanon abinci ta dire mishi a gabanshi.
"Wannan Ƙaunarka ce Habi kenan. Ashirin ga wanga wata za'a ɗamra amrensu su bakwai cib. Habi wannan wankine Gwadabe." Gaisheshi Hari tayi da ladabi, ya amsa cike da fara'a, ta saka kai ta fita.
"To Fhatsima ga Gwadabe na damƙa amanarshi gareki, ki zame mishi uwa tunda kece babba a cikin gidannan. Rigingimu ne na dangi su kai yawa shine na yanke hukuncin tawo dashi in gameshi da su Auwala suna tafiya haƙan zinariya. Sauran bayanin in kwananki ya zagayo zan zaunar dake mu tattauna. Labulen ɗakin aka ɗaga. Wata baƙar dattijuwa mai zanzana ce tsaye ɗayan hannunta riƙe da faranin silba shaƙe da kwanonin silba a kai. Ɗayan hannun kuma riƙe da labulen ɗakin. Dukkansu suka ɗago suna kallonta.
"Abincin É—akin Yaya zaka ci, ko in kai shi turaka?" Babu yabo babu fallasa tayi maganar. Sai da malam ya girgiza kai, Baba Fhatsima kuma tayi murmushi tace.
"In banda abinki kema kinsan ai a turaka zaici. Me zai sa yaci abinci a É—akina ke da ranarki" Guntun murmushi tayi tace.
"To wa ya sani abu a dubu Yaya."
"Ki kai mun turakata gani nan zuwa" Malam ya bata amsa da kaurin murya da halamun ɓacin rai tattare da shi. Tana sakin labulen ya miƙe ya fita. Baba Fhatsima tace.
"Kaci abincin, sai a nuna maka shashen samarin gidan ko?"
"To Baba Nagode " Gwadabe ya bata amsa a dalabce.
MRS BUKHARI B4B GIDAN

3064127935
Buhari Ibrahim Ladan
First bank

Sanya nera 500 É—inki kuÉ—in karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan.
Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun
Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya.

WaÉ—anda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ÆŠANYE)
300 kacal zasu iya kuÉ—in karatu

*Ƴar uwa ina fatan baki mance da kayan ƙamshin Mrs Bukhari gidan ƙamshi ba ko? Ƴar na gata ba take haye ba, Kanuri gidan ƙamshi. Matso kusa ƴar uwa ina da turarukan wuta nau'i daban_daban. Turaren kaya da zaki turare gidanki ƙamshi ya riƙe miki surura, sannan inada kabbasiyya turaren ruwane da ake fesama sutura a yayin da ake turara kaya a kabbasa, kana inada turaren wadrop da ake saƙawa a tsakankanin kaya.
Turarukan wutana kuwa in kika turara gidanki yana sati guda yana ƙamshi. Inada turaren turara jiki gangariya wanda yake kama fata.
Akwai kulaccam ta matan aure mai sirrin rikita maigida, ga gyaran fata. Akwai kuma kulaccam ta gashi, haÉ—e da turaren fesawa a gashi.
Mai gayya mai aiki humrata ta matan Aure mai sirrin ƙara dankon soyayya, kiga oga na shinshinarki kamar mage taji ƙamshin kifi ɗanye.
Inada humrori kala_kala.
Ina da room freshener, da mopping mix mai sirrin ƙamshi.
Kar in ta lissafo muku duk wani nau'in ƙamshin da kikeso in kika samu Mrs Bukhari ƴar mutan Maiduguri kin samu ƙamshi.
( Albishirinku akwai package na musamman dana tanadarma masoya wannan littafi nawa. Package ne mai ɗauke da abubuwa huɗu manya kuma a kan kuɗi ƙalilan karki bari garaɓasarnan ta wuceki zaki ciji yatsa kwasha_kwasha nayi da kayana domunku)*

NAMA YA DAHU...
ROMO ÆŠANYE
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE
Chapter 52 · 0% Book details