Sashe 214
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Uwani. "Yaufa abincin Amarya zamu ci" Da mamaki Uwani tace. "Amman dai wasa kake yi ko? Yanzu duk wannan kwalliyar dana rangaɗa sai in shiga kitchen?" Idanunshi ya lumshe yana ci gaba da shaƙar humrar matan auren da uwani ta shafa yake fisgarshi. "To kiyi haƙuri ba haka naso ba, amman kinsan sha'anin kishin mata. Ita Hajiya Mansa ma bata nan suna da biki a family House ɗinsu ita da yaranta kab sun tafi. So abincin ba mai yawa zaki yi ba. Nawa da naki ne saina Sa'a da yaranta. Sai na masu gadi" Murmushi Uwani tayi, ta saki hannunshi ta miƙe. Mayafi ta yafa daidai da kalar kayanta. Da ciro sabon takalmi ta saka ta gangara ƙasa acan babban kitchen ɗin gidan yake tangamemen gaske. A kitchen ɗin ta tadda Laure tana jiranta. "Hajiya barka da fitowa" "Yauwa Laure. To in akwai doya ki fere mun dan Allah, ina fatan ban makara ba dai ko?" Ta ƙarashe maganar tana dariya. Laure ma tayi Dariya tace.. "Baki makara ba dake yaran anyi musu hutun boko, islamiyya kuma sai ƙarfe goma suke tafiya. Nan dai Laure ta taimaka ma Uwani ta soya doya, ta yi miyar ƙwai kana ta dafa tea. Laure ce ta nuna mata durowar da kayanta suke ciki, ta kuma sanar mata ai ko kulolin abincin jiya nata ne a durowarta Hajiya Sa'a ta ciro aka zuba mata abinci a ciki. Nan dai ta nuna ma uwani yadda suke yi. Godiya tayi mata sai wajen taran safe suka gama kammala komai. Uwani ta haɗa nasu a babban tire. Laure ta haɗama Hajiya Sa'a nata. Haka da rana ma Uwani ta fito ta yi girki a lokacin oga ya fita har ya turo mota da daining table mai kujeru shidda an saka ma uwani. Da daddare Uwani tuwo tayi musu miyar ganye taji bushasshen kifi da naman kaza tayi musu jus na kankana. Kafin ƙarfe biyar ma ta sallami kowa ta shalla wankanta ta buɗe ɗakinta da turarukan wutanta tana jiran mijinta ya dawo. A haka har Uwani dai ta cinye kwana ukunta Hajiya Mansa bata dawo ba. Yau sa'a ce da girki Uwani tana kwance tana kallo a tashar zee aflam tana shan jus sai ta jiyo sallamar su ummi sun rako Hajiya ganin waje. "Uwani yau kece a cikin irin wannan duniyar? Allah da iko yake." Hajiya ta shiga kalle_kalle. Uwani tace. "Hajiya ku zauna dai. Bari in sanar ma da Laure zuwanku a haɗo muku abinci. Ina zuwanku. Sauka tayi har zuwa kitchen ɗin gidan. Hajiya Sa'a na ciki Laure na kama mata girki tace. "Hajiya Sa'a barka dai da aiki" Juyowa tayi ta zuba ma Uwani idanu kafin dai ta danne abinda ya taso mata tace. "Yauwa Hajiya Uwani." "Dama Hajiyata ce tazo shine nace bari in sanar muku a saka sanwa dasu" Murmushi tayi tace. "Ayya sai dai ki shigo ki ɗaura musu kinga harna gama girkin dama yanzu Laure zata miƙa miki naki. Nan gaba kya sanar da wuri in zaki yi baƙi ko?" Sai ta juya tana rufe manyan kulolin Oga da za'a kai mishi abinci kasuwa. Murmusawa Uwani tayi ta koma sama. Ruwa da lemuka ta dure ma su Hajiya ta shige ciki ta kira Alhaji ta sanar mishi yadda suka yi da Hajiya Sa'a cikin hikima. Dan tayi ne kamar tana bashi labarin ai girki ma zata sauka taje tayi musu Hajiya Sa'a ta riga ta gama aikin rana. Yayi maza yace. "A_a bari in kirata aba su Hajiyan nawa. Mu ko taliyane ta sake ɓararraka mana. Ina zuwa" Murmusawa Uwani tayi tace. "To Shikenan Alhaji babu damuwa godiya nake" Ya aka ƙare oho dai dole ƙanwar naƙi aka hauro ma da su Hajiya abincin Alhaji. Suka zauna suka kwashi gara. Sai dab la'asar Hajiya tace su ummi su taso su tafi. Har ɗakin Hajiya Sa'a Uwani ta kai Hajiya. Ta tarbeta da kyau babu laifi ta ɗanyi musu nasiha dai haka kafin uwani ta rakosu bakin get. "Gashi Hajiya wannan kuyi na mota. Saina shigo nima. Ummi a kula dai da shagon dan Allah" Nan su kai sallama Uwani ta koma sama abinta. Ana idar da sallah sai ga Alhaji ya shigo. Ya samu Uwani na shan fura ai sai ya gyara zama aka shanye furarnan dashi, suka dai ɗan taɓa hira kafin yayi mata sallama. Ranar da Hajiya Sa'a ta fita a girki, a ranar Hajiya babba ta dawo cikin gidan da ƴaƴanta ta amshi girki tayi. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI