Sashe 191
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shafa na zaune taga Hadiza ta shigo da sauri. Tana isowa kusa da'ita sai kawai ta rufeta da dukan da yaba Shafa mamaki. Jin kafafniyar dukan da Hadiza take yima Shafa ne da faɗin "kar ki je ɗinkinki ya sake ɓallewa Yaya" Yasa matan gidan fitowa kusan mutum huɗune suka shigo ɗakin suka jaye Hadiza tana haki. Duk da sun sha dambe Hadiza ta doku da kyau a hannun Shafa, take Shafa jini ya soma bin ƙafarta halamun ƙaramin cikin dake jikinta ya zube. Duk da haka bata bar Hadiza ba "Wallahi sai kinyi nadamar wannan faɗan da kika takalo. Na dena ragar miki tunda dai ke jahilace mai kishin hauka wawuya marar tunani" Wannan furuci yafi komai ɗaga hankalin Hadiza ainun. Yau ita Shafa ta kira da suna jahila? Jan hannunta matar Mammada tayi ta mayar da'ita ɗakinta. Sai ita ta ƙarashe mata girkin nata ta shigar mata dashi ciki. Ciwo ya dawo mata sabo Ita dai tana kwance ta mugun ƙurama silin idanu, damuwa sun ƙara cunkushe mata zuchiyarta. Ga a Irin wadatar da ta ga Isuhu da matarshi abun ya sosa mata ranta, bawai baƙin ciki take yi mishi ba, ba wai finta matarshi tayi ba ko ɗaya itama tasan mijin da take aure babu raini. Ga Gwadabe yanzu shigar shaddajo masu tsada yake yi sabida yana harka da manyan masu kuɗi sosai, sana'ar magungunanshi tana mugun kai mishi sosai. Ajjiyar zuchiya ta sauke da jiyo muryar Anty Badi'a ta shigo da yaranta suna biye da'ita. "Hadiza ashe ke dai baki da hankali ko? Wallahi kibi lamarin kishi a hankali. Akan Gwadabe dai kike wannan wautar kuma kinsan bazai goyi bayanki ba sai ma yin Allah wadai da abinda kika aikata, gashi a garin shirmenku cikin Shafa ya zube. Kika sake yayunki suka ji abinda kika aikata ranki ne zai ɓaci kinsan Sabitu duka zai yi miki sakarar kawai. Yaran ta barma Hadiza ta yi ficewarta ganin yaran yasa Hadiza haɗiye yawu ta haɗiye damuwarta tace. "Kuzo ku zauna mana ko guduna kuke yi? Babban yace. "Mu gida muke son a mayar damu wajen Babanmu mu ba zamu zauna ba" Gaban Hadiza ya faɗi data ji abinda yaron yace. Ta kuma tuno da roƙon da Isuhu ya dinga mata akan lallai ta tafi da yaranta taƙi fur a ƙoƙarinta na ƙuntatama Amarya tare da kawo musu cikas a cin amarcinsu. Ashe batasan cikinta ta daɓa ma wuƙa ba ita bata sani ba. Ajjiyar zuchiya ta sauke tace. "Kuyi haƙuri kunga dare ya rufa gobe za'a mayar daku gidanku. Kai usmana kaje banɗaki ka yi alwala maza kaje waje kayi Sallah. Ke kuma inya fito sai kije ki ɗauro alwala kiyi sallar anan sai in zuba muku abinci kuci." Ficewa Usmanu yayi, yana fita sai ga Ummi ta shigo ɗakin anyi mata wankan yamma Abba na biye da'ita. "Kai maza jeka ɗakin uwarka karka kuskura ka zauna mun a ɗaki ɗan iska mummuna mai ƙaton kai irinna ubanshi" Abba ya fashe da kuka ya nufi hanyar waje. Ashe Gwadabe na tsaye a bakin ƙofar ɗakin a kunnenshi duk tayi wannan zagin. Abba ya raɓa ya wuce uban da gudu. Kallon kallo ne ya wanzu a tsakankanin Hadiza da Gwadabe. Kai ya girgiza kawai ya saki labulen ɗakin ya dawo falo. Ledar hannunshi ya ajjiye a gefe yana shirin fita usmana ya shigo. Yaron yabi da idanu harya shige uwar ɗakin, har ya sa ƙafa sai fita shi kuma daga falon sai ya dawo dai. Labulen ya sake ɗagawa Hadiza na tsaye tana zirga_zirga tana naushin hannunta. "Yarannan kafin in dawo su bar ɗakinnan dan ban amince su zauna mun ba suna da gidan uba dan ubansu a mayar dasu In kuma kina sha'awar komawa kan ƴaƴanki ne ƙofa a buɗe take zaki iya sanar dani kinga gashi yayi kuɗi" A tsorace Hadiza tace. "Me kake nufi danine? "Bala'i da masifa nake nufi dake. Ke baki sanni bane amman zan nuna miki wallahi nafi ƙarfin gidana kuma ni gidana bazai zama sansanin yaƙi da ƴan ubaba ki sani. Na fiki iskanci da bariki, baduniye ne da kike ganina. Da irin faɗa da tsawar da Gwadabe yake magana ya tsorata Hadiza dan tayi imanin na tsakar gida ma na iya jiyo sababinshi balle Shafa da ga_ ɗaki ga _ɗaki. Labulen ya sake a zafafe ya fice. Yana zage_zage Haka dole Hadiza ta kama hannun yaran ta kaisu ɓarayin Anty Badi'a tare da mata bayanin abinda ke faruwa" "Ai yayi kyau dama mai haƙuri bai iya fishi ba, maza dai ki turkuɗe auren naki ki huta kinga sai a buga miki tambarin ga wacce kishi yake hanawa zaman aure. Kuma Malam kinsan zaifi fishi dake ainun. Ga Sailuba nan ta kula dasu ni asibiti zanje in kaima Babansu abinci in sake dubo Malam ance jikinshi da sauƙi har yana magana." Ajjiyar zuchiya Hadiza ta sauke a sanyaye tace. "Allah ya bashi lafiya dorarriya kya gaisheshi da jikin in kika je." A daddafe Hadiza ta koma ɗakinta ta shiga ta tadda Gwadabe zaune yana cin tuwon Shafa yana ba Abba da Ummi a baki. Ko kallon inda Hadiza take baiyi ba, itama wucewa tayi abunta ciki bata sake fitowa ba sai washe gari da asuba. A falon ta tadda shinfiɗar bargon da take da tabbacin na Shafa ne harda matashin kai. Kai ta girgiza kifiyar kishi ta soketa. Cikin wannan gaba har kwana huɗu Gwadabe na abu ɗaya baya cin abincin Hadiza, baya kwana a ciki sai falo ko gaisuwarta baya amsawa, ga yawan waya da yake yi da Bara'u akan Iyabo harda kuɗaɗen da Gwadabe yace aima Iyabo siyayya Hadiza ta sani, a ranar kasa bacci tayi sai juyi kawai ta riƙa yi har gari ya waye, ta kuwa tashi da ciwon kai mai tsanani, abu ya haɗe mata goma da ashirin. A haka har aka sallamo Malam daga asibiti ya dawo gida ya tarar da abun farin ciki yau ga yaranshi kawunansu a haɗe har an zauna zaman meeting na lumana na farko tare da sake ma juna ta'aziyyar Baba Fhatsima. Yaya Zarah dai da aka gama komai sai ta yi ma kowa sallama ta tattare yaranta suka koma. Hadiza har zuwa wannan lokacin a cikin faɗa suke da Gwadabe ɗiyarta dai tana hannun Shafa, ta kasa tambayar Gwadabe ɗiyarta, ga wajen da akai mata tiyata sai ciwo yake yi mata. Da dai taga abun Gwadabe bana lafiya bane ranar daya dawo ɗakinta ta fito da zummar yi mishi magana ta riskeshi yana waya da Bara'u Sakina ta haihu. "Ah masha Allah to Shikenan zamu tawo kafin suna ko da ni da Shafa ne Hadiza jinya take yi kaga ba tayi doguwar tafiya ba. Kace ina ma Sakina sannu, kaga in muka zo sai mu tawo dasu Toye" Sukaita hirarsu Gwadabe ya dinga jan hirar dan ya baƙantama Hadiza daga ƙarshe dai dole sukai sallama. "Dama dan Allah nazo in roƙeka gafarane a bisa abubbuwan da sukaita faruwa. Sharrin shaiɗanne kuma hakan ba sake faruwa zaiyi ba ni wannan fishin ya isheni" Ƙur Gwadabe yayi mata da idandunanshi yana wani ƙanƙancesu, ita kuwa kanta a ƙasa tana jiran me zaice. "Hmm Hadiza kenan sai yaune kika ji kina son kizo ki bani haƙuri, ai nayi tunanin kinfi jin daɗin zamanki a haka? Harni zaki cema yarona mai ƙaton kai kamata dan iskanci da wulakanci, kina so tun suna yara ki cusa musu mummunar aƙida. Sannan kika dubi tsabar idanuna kika kirani da azzalumi mayaudari mai bibiyar matar Aure " Da sauri Hadiza ta runtse idanunta tare da katse Gwadabe ta hanyar cewa. "Yaya ni dai dan Allah ka yi haƙuri banda tashin tashina" "Rufa mun baki saina gama tsab" Dole ƙanwar naƙi Hadiza ta rufe bakinta ruf Gwadabe yaita tambotsai kafin daga bisani yace ya haƙura amman fa ba har cikin zuchiyarshi ba. "To yarinyar kuma sai yaushe za'a dawo mun da'ita?" Dariya yayi yace. "In dan sabida a dawo miki da yarinyane kika zo ban haƙuri kinyi gwari Hadiza. Yarinya ai kin nuna bakya sone shi yasa kika so ta mutu ki huta. Aikin banza aikin wofi" Ya faɗa tare da tashi yayi ficewarshi sallar Isha. Har gwadabe ya dawo Hadiza na ciki tana kuka, ko daya dawo bai ko nuna ya damu da ganin Hadiza a wannan yanayin ba. Amman a ƙasan zuchiyarshi ya tausaya mata, ga rashin uwa, ga ciwo a jikinta, amman daya tuno halin jarabarta sai yaji haushinta. "Har yanzu baki dena wannan kukan ba wai Hadiza, ko dukanki nayi ne, wannan wanne irin buyagine?" Hadiza ta jima tana ƙoƙarin haɗiye kukanta yaƙi haɗiyuwa sai dai da taci nasarar karya zuchiyar Gwadabe. Hannu yasa ya ɗagota ya mannata da ƙirjinshi ya shiga shafan bayanta. Sun jima sosai a haka ji yayi sonta na ratsa jikinshi. Amman a kashi ɗari na sonta saba'in ya zube tas "Ya'isa haka bani abincin to inci." A kunne yayi mata raɗar, murmusawa tayi taje ta ɗakko mishi abincin ta kawo mishi, kanta na kan cinyarshi yana cin abincin yake cewa. "Gobe zan shiga Damagaran akwai wani babban mutum da aka haɗani dashi zan kai mishi maganin ƙarfin maza yana da rauni ta fannin gamsar da iyali, kuma yayi maganin harma ya gaji. Ga arziki amman babu mace ko ɗaya a gidan duk sun kama gabansu. Shine akayi mishi hanyata gobe zanje sai ki saka ni a adda'a kwana biyu zanyi a gidan nashi akwai dafe_dafen magani da zanyi, in dai yasha da izinin Allah sauƙi zai samu, ki taya ni da adda'a" Murmushi Hadiza tayi tace. "Yana son ya zama jarumi kamarka kenan?" "Au ni jarumine bani da labari?" Ya tambaya yana shafa sumarta. "Me abu da abunshi kura da kallabin kitse. Kullum fa saika ɗibgi magani muna gani" Dariya yayi sosai ya kawar da zancan da cewa. "Sakina ta samu kai yau ta samu ɗiyarta mace. To ana gobe suna in jikinki ya sake yin kyau sai mu rankaya dukka, in kuma baiyi ƙwari ba sai muje da Shafa da yaran duka. Su Toye ma sun dawo daga wajen Gyatumar tasu suna Takai saiki soma shiri ko?" "Allah ya nuna mana lokacin" "To Ameen " Daga haka dai faɗa ya ƙare washe gari Gwadabe da hannunshi ya ɗauko yarinya daga wajen Shafa ya damƙama Hadiza ita, yai musu sallama