← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 213 OF 237

Sashe 213

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da duk naci irin na Hafizu a bisa tilas ya sararama Uwani dolenshi, musamman daya lura kamar kuttun farin jini ya fashe mata. A wata huɗu da rabuwarsu Uwani ta sake gogewa ta zama cikakkiyar babbar mace, dan da kanta yanzu take zuwa makka siyayyarta bata tsayawa jiran komai. Allah cikin ikonshi a irin wannan tafiye_tafiyen a cikin jirgi Allah ya haɗata da Alhaji Sama'illa. Hamshaƙin ɗan kasuwane dattijo ɗan gaye. Allah ya daidaita tsakaninshi da Uwani kamar dai wasa suka ƙulla mu'amular soyayya tare da alƙawarin aure bugu da ƙari. Muddin Uwani na gari to Alhaji Sama'ila baya rabo da kawo ma Uwani ziyara barenma da yasan ya miƙa sadakinshi gidansu Uwani an tsayar da lokacin aure. Wata ranar laraba Hajiya Uwani tana shagonta tana jera kayayyakin data saro, yaran shago na ta aikinsu, ta faɗaɗa shagon nata an ƙara ƙawatashi ga kaya danƙan. Sai ga Hafizu da yaranta sun shigo. Kallonsu tayi taci gaba da aikin da take yi har saida ta gama ta dubi babbar ƴar tace. "Ummu Kursum lafiya na ganku anan ina makarantar fa? Carab Hafizu yace. "Wallahi Hajiya korosu akayi Uwani, ni kuma a yanzu bani da kuɗin dazan biya musu kuɗin makarantar shine nace musu su zo mu zo mu sameki ko bashine a bani in sha Allah dana dawo daga tafiya zan dawo miki dashi" Uwani ta dubeshi ta sake dubanshi ta dubi yaran duk dai ita suke kallo sai ta haɗiye duk jarabarta. Ana cikin haka kuwa sai ga Alhaji Sama'ila ya parka motarshi a gefen shagon Uwani. Fitowa yayi yaci uwar kwalliya sai ƙamshi yake busawa ya shiga shagon ya nemi waje ya zauna. Hannu ya miƙa ma Hafizu suka gaisa. Dama dai sun san junansu a shagon uwani, kuma Hafizu yasan shi zai auri Uwani "To ku taso anjima ma dawo umma tayi baƙo ko Ummu Kursum" Cewar Hafizu yaran suka gaishe da Alhaji Sama'ila ya amsa da fara,arshi dama ya sansu suna yawan zuwa wajen Uwani cin abinci. Kuɗi ya ciro masu kaurin da zai isa a biya musu kuɗin makarantar ma ya basu. Hafizu ya kama hannunsu suka fice, kai tsaye ya mayar dasu makaranta. Da wannan kuɗin ya biya kuɗin makarantar ragowar kuma yayi cefane ya nufi gida bagazan_,bagazan "Ranki shidaɗe kina ta jera kaya a shago. Ni na faɗa miki wannan shagon kasuwa zai koma can idon mutane. Na yi tunanin tunda dai bikin namu baifi wata ɗaya ba nayi tunanin ma ba zaki buɗe dilar ba har sai an samu shago uhm?" Murmusawa tayi tace. "Ai da ni nayi tunanin wannan ɗin in barshi aci gaba da kasuwancin tunda dai an saba kuma ana samun ciniki ko su ummi sa dinga lurarmun dashi. Sai a sake buɗe sabo a kasuwar ma." Idanu ya zuba mata yana murmushi yace. "Hakan ma wata dabarar kasuwanci ne. Amman kina da kuɗin da zai isheki saro kayan da zaki cika shi shagon na kasuwarne da girma shagunan kasuwa?" Dariya tayi yace. "Za'a gagganɗa ayi abinda ya dace, ko dila biyune zan harhaɗa kuɗin harda na aminiyata in saro kayan in yaso na dinga cire mata riba. Kuɗaɗen hayar gidanta suna nan jingim a hannuna. Allah sarki Iyabo alkhairin Allah ya kai miki a duk inda kike haƙiƙa munyi babban rashi, ko in mijin baiwar Allahn nan ya dawo ya zai ɗauki wannan babban lamari sai Allah" Ajjiyar zuchiya ta sauke ta shiga damuwa lokaci guda harda hawayenta. Alhaji Sama'ila ya shiga aikin rarrashinta. "Gaskiya akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninki da Iyabo a haɗuwata dake na fahimci hakan tun kafin ki bani labari a kanta. Fatanmu shine Allah yasa ta faɗa hannu na gari. Allah ya dawo da'ita cikin ahalinta shine. "Ameen Ameen." "To ni batun kayan lefe ne ya kawo ni ma Shin kuɗin kike da buƙata, ko kuwa a haɗo akwatunan wanne kika ga yafi?" Ɗan murmushi tayi tace. "Zan fi buƙatar kuɗin gaskiya. Suturu kam Alhamdulillah a cikin ɗinkasu ake. Akwai abubbuwan da ban ƙarashe ba na kayan ɗaki to kuɗin zai taimaka sosai" "To Shikenan dubu ɗari biyu yayi miki?" Ya tambaya yana kafeta da idanunshi. "Sunyi sosai ma, nagode sosai Allah dai ya tabbatar da Alkhairin shi. Sannu da ɗawainiya." Hira dai suka taɓa kafin yayi mata sallama shi kam zai tafi zuwa gobe zaije banki ya ciro mata kuɗaɗen a haka suka rabu. Dubu ɗari biyun da mai daraja fa ba irin ta yanzu ba ehe. Washegari kuwa kamar yadda yayi alƙawari sai gashi da wannan kuɗi. Uwani ta harhaɗa da kuɗaɗenta tai ma kanta kayayyakin ɗaki na fitar raini. Kayayyakin kitchen kuwa dama daga saudiyya duk ta siyo abunta. Turarukan wuta kuwa show glass guda Uwani ta siya a wajen Mrs Bukhari gidan ƙamshi ( Ina iyayen amare, ina amaren, da zauwara ina haɗa turarukan wuta na amare na musamman har show glass duk ina siyarwa mai cike da kwalabe da turarukan wuta da humrori kala_kala. A sauƙaƙe inayin adashe domin samama iyayen yara sauƙi sai ki zuba kuɗin a hankali kafin zuwan lokacin biki aikinku ya kammala da izinin Allah. Iyayen gida ma inayi muku taku show glass ɗin ta turaruka da humrori domin burge mazajenku, ki sani ba Amarya bace kaɗai take da buƙatar show glass ta turaren wuta ba kema kina da buƙata) Uwani ita taima kanta komai da komai. Ta samu manyan kaya kala goma ta ɗinkesu. Ana biki saura sati biyu Alhaji Sama'ila ya kirata yake sanar mata an samu wani danƙareren shago mai ƙofa biyu a kasuwa ya kama mata. Sauran ya rage nata zuba kaya da buga kantoci. A wannan karon haɗa kuɗaɗen tayi ta tura ma Faty, ragowar kuɗaɗen hannunta ta biya masu buga kanta suka soma aikinsu. Sati biyu na zagayowa fa aka ɗaura auren Uwani da Alhaji Sama'ila. Da daddare aka raka amarya gidanta dake unguwa uku. Falon uwargidan Alhaji Sama'ila cike da ƴan uwanshi da ƴan uwanta aka shigo da Amarya idanta a buɗe fes babu wanda ya ma riƙeta. "To ga Amarya mun kawo miki Hajiya Mansa. Sai ayi haƙuri da juna dan Allah a zauna lafiya" Cewar yayar Hajiyan Uwani kenan. Hajiya Mansa tace. "Allah ya bamu zaman lafiya. Ubangiji Allah yasa da Alkhairi ta shigo. Ɗakin Hajiya Sa'a yana sama in kun haura kusa da ɗakin Amaryar." "To mun gode ƙwarai Allah ya haɗe kawunanku baki ɗaya" Nan ƴan rakiyar Uwani suka fita daga ɓarayin uwargida sarautar gida. Zuwa ɓangaren da yake gidan sama mai hawa biyu. Hawan farko anan ɗakin Uwani da ɗakin Hajiya Sa'a yake. Saman kuma turakar ogan da kanshi ne. Gidan fa akwai girma arziki da gani ya zauna da ƙafafunshi. Hajiya Sa'a ma babu laifi ta tarbi su Uwani babu yabo babu fallasa sai dai ba kamar yadda Hajiya Mansa tayi musu ba. Falukan gidan danƙama_danƙamane ko wacce ɗakinta cike da kayan alatu. Ajjiyar zuchiya Uwani ta sauke data shiga nata falon taga babu raini, ga wasu irin manyan frames dake mammanne a bango da suka ƙara ma falon kyau da tsari. Ƴan rakiyar Amarya basu daɗe ba sukai ma Uwani sallama su ka yi gaba. To ita ba yarinya ba, bayan ta gama zagaye ɗakunan nata sai ta dawo ta zauna a falo ta kunna tv. "Oh Allah mai iko ni Uwani yau nice a cikin irin wannan daular, a tsakankanin hamshaƙan mata masu ji da kuɗi da kyau? Iko sai Allah wallahi Allah kuɗi yayi a rayuwa. Ya Allah ka baiwa yaranmu mazaje masu rufin asiri suje su huta suma. Ya Allah ka kaɗe fitina a wannan auren Allah kana ganin irin azabar da Hafizu ya dinga gana mun Allah kasa Alhaji Sama'ila ya riƙe ni da kyau" Sallama ta jiyo daga bakin ƙofar falon nata. Ta taso da yanga ta buɗe. Hajiya Sa'a ce tafe da ƴar aiki hannun ƴar aikin ɗauke da ƙaton tire jere da wasu kuloli na alfarma. Tace. "Amarya ga abincinku nan ke da Alhaji. Wannan sunanta Laure ita ke taya mu aikin girki. Laure shiga ki jera mata in tana da daining in babu kuma ki jera mata a ƙasa" Tana idasa faɗe ta juya. Waje Uwani ta ba Laure ta shiga ciki ita kuma tana tsaye tana murmushi magana ce nan Hajiya Sa'a ta mugun yaɓa mata. Bata sam waye Uwani bane shi yasa. Ta lura da yanayinta dama. Kuma ko suna tare da Alhaji Sama'ila Hajiya Sa'a tafi yawan kiranshi a waya. Hajiya Mansa sau ɗaya tak ta taɓa kiranshi suna tare. Kenan dai Hajiya Sa'a itace ta gaban goshin Alhaji Sama'ila tunda itace Amarya kuma ba wata babba bace itan bata wuce shekarun uwanin ba. Saɓanin Hajiya Mansa da take dattijuwa mai samari da ƴan matan ƴaƴa. Laure ta gama jera kayan abincin a kafet ta fita. Uwani ta dawo ta zauna. Sai kuma ta tuna ai ya kamata ta kunna burner ta saka turaren wuta. Ai kuwa haka akayi ta harhaɗa turarukan wuta kusan kala goma ta kunna a bona ɗakin take ya karaɗe da wani sassanyan ƙamshi na kece raini. ( Akwai mix turaren wuta wanda ya haɗa duk itacen turarena fin kala goma a cikin kwalba ɗaya. Wannan wani babban sirrine na musamman wanda in kika riƙe duk ƙwaƙwar mai ƙwaƙwa bai isa ya gano da wanne itacen turare kike amfani ba. Yananan a babbar kwalba mai cin 1 litter haka na zuzzubasu. Siyan jagari) Alhaji Sama'ila ne ya kwankwasa ƙofar yana ƙwala kiran honey " Murmushi Uwani tayi ta daka tsallen murnar wai yau itace da miji mai kuɗi miji wayayye ɗan gaye har yake kiranta da Honey. Sannu a hankali ta isa bakin ƙofar ta buɗe mishi. Tayi saurin amsar ledojin hannunshi ta shigar dashi. Ɗakin yake ta ƙarema kallo yana yaba kyau da tsarin ɗakin" "Ɗaki yayi kyau mai ɗakinma tayi kyau. Saura abu ɗaya ya rage miki gobe in sha Allah zansa a kawo." To daga haka dai aka ci kaza akayi Sallah. To mai ya rage kuma? Na baku gari ku fasalta wannan dare a ƙwaƙwalenku. Washegari Amarya ta tashi da farin cikin shiga sabuwar rayuwa. Angoma ba'a barshi a baya ba. Amarya dai amaryace ko da kuwa ta buzuzuce. Balle Uwani zagewa tayi ta gyara jikinta ƙaƙas. Kuma da ingantattun kayan matan Ramlex kwamishiniyar buje tayi amfani. Bayan ya dawo masallacine yake sanarma
Chapter 213 · 0% Book details