Sashe 219
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Hadiza ta fashe da kukan baƙin ciki a tsakar gidan daidai malam ya gama abinda yake yi a ɗaki ya fito.
"Ai baki yi kuka ba wallahi akwai sauran kuka a gabanki. Domin Gwadabe tattarawa zaiyi nan da shekara ɗaya masu zuwa ya koma can Najeriya yanzu haka a ƙauyensu ƴan gundumarsu shi suke son tsayarwa a ɗan takararsu na kansila siyasa Gwadabe ya shiga. Kina nan zaki ga Shafa a Abuja a cikin taron matan gwamnoni ana damawa dasu shashashar kawai.
Isuhun da kika raina a baya kika kasa bashi farin ciki ba ga yadda rayuwa ta warware mishi ba, kece baki da rabon arziki. Shi kanshi Gwadabe rabuwarku ce ta É—aga darajarshi. Duk matar da bata bama mijinta kwanciyar hankali ai ba zata barshi ya nemi arziki ba. Asshi ki dinga nusheta in zata gane"
Baba Asshi ta ce.
"Malam a dai yi haƙuri wannan karon abun ka ɗauka da zafi. Ni ina ganin ka ba Gwadabe haƙuri ya mayar da matarshi ɗakinta dan Allah. Yarinyarnan fa tana son mijinta"
"Babu ruwana ai bani nasata tayi abinda ta ƙure mijinta ba. Dan ɗiyatace bazan bari ta cuta ma Gwadabe ba dan shima ɗanane, yayi haƙuri da'ita ainun"
Yana gama faÉ—ar haka ya fice.
Baba Asshi ta dubi yadda Hadiza take kuka kamar wata ƙaramar yarinya tace.
"Hadiza kuka ba magani bane. Kiyi ƙoƙarin gyara laifinki a wajen Gwadabe tun kafin iddarki ta cika ki samu ya mayar dake. Kar kiyi sake Gwadabe ya kubce miki, mijinkine har yanzu ke kika san logonshi kima share hawayenki kawai"
Sai lokacin Hadiza ta ɗanji sanyi a zuchiyarta harma da yamma ta kintsa ta tafi gidan ƙawarta Chima.
Da sallama ta shiga ɓarayin ƙawar tata gidan babbane sosai. Ai kuwa ta samu Chima a kwance a kujera ta caɓa adon bazin tana kallo ɗakinta sai ƙamshin turaren wuta yake yi.
Sai Hadiza taji tana matuƙar kewar mijinta da ɗakinta har hakan sai da yai sanadin taruwar hawayenta.
"Yau uwargidan Gwadabe ce a gidan nawa da yamma haka, ko dai ɓatan kai dai kika yi ne?
Dariya Hadiza ta ƙwaƙulo tare da zama.
"Wash kya ji dai dashi Chima ni bani abu mai sanyi in sha"
Da sauri Chima ta kawo ma ƙawar tata jus harda shayi da ƙaramin kofin tangaran na shan shayin.
"ÆŠakin kai mai daÉ—i Chima. Mace bata ganewa sai wata kaddarar ta rabata da É—akinta ta koma rayuwar gidansu"
Dariya Chima tayi tace.
"Ƙawata an tuno da zawarci kenan? Hakan yasa na tuno jiya uwar haka kishiyarki ta da matar Isuhu tana gidannan wajen kishiyata. Ta kawo shaddaji daga mali tazo ta kwasa. Ni abinda ya bani mamaki bazin masu geza da shole duk ta ɗiba. Kuma ba bashi ba take ta biya. A bakin abokiyar zaman nawa nake jin labarin ashe har umara suka je dana ɗan doki cikinta"
Wata ƙayar kishi ta miƙe tsaye a maƙoshin Hadiza da ƙyar ta haɗiye yawu tace.
"Ture maganar Isuhu da ƙazamar matarshi nifa an yanka ta tashi aurenane ya mutu Chima. Yanzu haka Gwadabe yana umara da Shafa'
Nan Hadiza ta kwashi labarin komai ta labarta ma ƙawarta kuma bata ɓoye mata kuskuren data aikata ba itama"
"Assha kinyi wawa Hadiza. Kin zubar da girma da mutuncin mata, kin watsama iyayen gida ƙasa a ido. Ko duwatsune Shafa da Gwadabe dole ki kaisu bango.
Mafitar ɗaya ce kiyi duk iya yinki mijinki ya mayar dake ɗakinki, kibi duk hanyar da zata ɓulle ke inta kama ki tsugunna guiwiyinki a ƙasa ma duk kiyi ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba.
Amman kafin su dawo ki zama mace Æ´ar gaske macen da tasan kanta. Kuma ki koyama kanki danne kishinki a koma inane. Ke baki isa kice sai an faranta miki É—ari bisa É—ari ba. Domin kema ba zaki iya kyautatawa É—ari bisa É—ari ba. Ba zaki ce miji sai dai ya kula dake ke kaÉ—ai ba alhalin itama waccan na da nata hakkin.
Kin ganni sau nawa maigidanmu zai kwaso gulmarshi ta maza yazo yana rage murya akan ki siyar mishi da kwana ya kaima kishiya. Ashe in kece sai dai washegari a tsinci gawarki ko?
Ni ko bajewa nake yi in samu baccina lafiyayye ke nifa namiji ko kishiya basu isa sunsa hakkinsu ya kaini wuta ba wallahi. Namiji inya kwaso rawar kanshi ki nuna mishi baki sanma yanayi ba. In kika nuna kina damuwa har ya gane logonki kin shiga uku. Dan na fahimci Gwadabe da gayya yake yin wasu abun dan ya kunnaki. Ke kuma sai ki kunnu. Tunda dan hauka har da tsohuwar matarshi kike kishi. Asa ma ɗiyarki sunanta kinƙi ga Shafa tana cin albarkacin sunan ai. Wato na lura yarinyarnan shafa tana da mugun wayo ne, shi yasa tayi miki fintinkau.
Tun farko me zaima sa in ba Shafa ta mayar dake jarababbiyar miji ba zata ce ta bar miki kwana harna wata biyu. Ke kuma kika amsa, hakanma bai miki ba harda É—aga labulen uwar É—akin kishiya?.
Bazan ɓoye miki ba in da nice kishiya ta buɗe mun uwar ɗakina to tabbas saina mareta Allah. Ai uwar ɗakina sirrinane ko haihuwa nayi ni ɗakin yara nake komawa da zama duk wanda yazo barka ina can, ɗakina da mijina yana kulle. Ke kin taɓa shigarmun ɗakina?"
Hadiza ta girgiza kanta tace.
"A_a ban taɓa shiga ba gaskiya. Iyakacina falo da ragowar ɗakunan"
"To wallahi Hadiza ba yabon kaiba uwarɗakina aljannar duniya ce ta more rayuwa duk wani kayan alatun saka nutsuwa da farin ciki a ciki nake sawa, duk sanda mijina ya shiga uwarɗakina sai ya sauke ajjiyar zuchiya kyau da tsarin kawai na iya sashi nutsuwa. Kullum a cikin siyan zanin gado nake domin sake ƙawata ɗakina. Hakan yasa ko jinyar da yayi ya takurama matan akan shi lallai a ɓarayina zaiyi jinya. Dole suna ji suna gani ya tawo nutsuwa yake nema Hadiza.
Amman ke har a kan gado kishiyarki take shigowa ta same ku. Ke kuma ki bisu ki gansu suna sumbatar juna."
Chima ta ƙwace ta dinga wayar da kan Hadiza. A taƙaice saida ta wanke mata ƙazamin kishinnan nata tas. Kafin Hadiza ta koma gida.
Tun daga wannan rana sai Hadiza ta tattare kayanta da yara ta yi komawarta É—akinta. Malam na dawowa Baba Asshi take sanar mishi ga fa halin da ake ciki.
"A kyaleta. Dama can ya dace ace tayi iddarta. In Gwadabe yaji tausayinta ya mayar da'ita É—akinta shikenan. In kuma yaji bazai sake rayuwar aure da'ita ba ba zan yi mishi tilas ba sam dan na fi son tayi aure a waje can bare ya gasata"
Haka Hadiza ta shiga gyaran É—aki da gyaran jikinta da taimakon Anty Badi'a. Har kayan É—aki da fasalin É—aki saida Hadiza ta canja. Sannan Anty Badi'a taci gaba da bata shawarwarin daya dace. Ta kuma sake ziyartar Chima ta sake É—orata a layi mai bullewa.
Ranar talata da yamma lis Hadiza na kofar kitchen ɗinta tana soya miyar kaji sai ga sallamar su Shafa da Gwadabe da kayan tsarabarsu niƙi_niƙi.
Hadiza ta kalli Gwadabe da kyau. Shi kuwa yana kan amsa sannu da zuwan matan gidanne. Dashi da Shafa duk sun maƙala haƙoran makka.
"Shafa kune a tafe? Maraba lalenku da zuwa. Ina Iyabo ban ganta a bayanki ba?*
Cewar Hadiza data isa inda suke tsaye da fara'arta harda amshe ma Shafa jakar kaya. Ba Shafa da Gwadabe ba hatta matan gidan sun yi mamakin wannan lamari. Cikin dariyar yaƙe Shafa tace.
"Tana najeriya ba da'ita muka tafi ba ai. Ya yaran kuma ina su Toye da ummi?"
"Suna can cikin gida wajen Baba Suwaiba. Gwadabe sannunku da dawowa ku shiga bari in kawo muku abinci"
Shi dai goga bai kulataba Shafa ta buɗe ɗaki suka shiga. Bata ma zauna ba dai ta ɗan soma kakkaɓewa Gwadabe kujera dan ya zauna. Yana zama yaran suka shigo da gudu suna murnar ganin iyayen nasu.
Hadiza ce ta biyosu da katon tire cike da kayan abinci ta dure a gabansu. Sai ta É—auki plate zata zuba musu Gwadabe yace.
"A_a ki bari Shafa zata zuba mun nagode ƙanwata. Baby zuba mun abincin yinwa nake ji"
Yawu Hadiza ta haÉ—iye tare da yin murmushi. Shafa ta zuba mishi farar shinkafa da miya lafiyayye. Ta dure mishi a gabanshi, ta nufi hanyar fita.
"Ina kuma zaki kinsan abinci zanci?"
Shafa ta dubi Hadiza ta dawo da kallonta ga Gwadabe
"Wanka nake son in yi kasan na gaji da yawa Baby"
Dariya Gwadabe yayi yace.
"To jeki amman kar ki daÉ—e in na gama cin abincin zanje inga malam"
Shafa ta tafi wanka Gwadabe ya mayar da kai wajen cin abinci shi. Bai gama ci ba ma Zulƙi ya kira wayarshi nan ya fice ya bar Hadiza a zaune kamar gunki.
Murmushi tayi a ranta taji zafi amman tasan abinda Shafa da Gwadabe su ka yi mata daidai ne ita ta ja ma kanta zubewar mutunci.
Ɗakinta ta koma taci kuka kamar ranta zai fita da ƙyar ta rarrashi zuchiyarta ta tuttura abinci tasha ruwa ta kwanta
Gwadabe kuwa bayan ya gama amsa wayar Zulƙi sai ya shiga makarantar Malam.
"Gwadabe mutanen makka kun dawo? Kai masha Allah sannunku da dawowa"
"Yauwa Malam da fatan na sameku lafiya, ya dalibai?".
Da dariya Malam yace.
"Gasunan wasu ma aka sake kawowa ka gansu nan. Sai ka dawo ka tarar da Hadiza ta koma ɗakinta ko? To bani bane nace ta koma ba. Dama shari'a ta bata damar zaman idda a gidanka. Bayan tafiyarka ta shiga damuwa mai tarin yawa. Ƴan uwan duka sun juya mata baya. Ni daɗina da Allah yasa Fhatsima bata raye wannan abun ya afku da yanzu ta sata a damuwa. Sai kayi haƙuri kaci gaba da ciyar da'ita zuwa lokacin da iddarka zata sauka a kanta."
"Babu damuwa malam. Ni gobe ma zan tafi Takai akwai meeting da za'ayi da mai girma Gwamnan Kano kuma akwai buƙatar zuwan ƴan takara. Gobe asussuba zan kama hanya sai a taya mu da adda'a "
"To to to Allah ya tsare yasa ayi taro lafiya a watse lafiya. Ni ko kasan halin da Iyatu ta jefa gyatumarku kuwa? Fitsararriyar yarku Halima ta kirani tana kuka wiwi ta labartamun halin da ake ciki."
Gwadabe yace.
"Na sani Malam"
Nan ya labarta mishi shi labari.A hakan harda tsarabarta a cikin tsarabar da yayo zai sa Bara'u ya kai mata ba tare da ance shine yayi ba"
"Hakan da kayi yayi daidai tabbas ka haifu Babala abinda ta shuka ne take girba. Kar ka kuskura ka nuna kanka ban amince maka kaje cikin gidannan ba. Kaci gaba da yi mata alherin ɓoyen ladanka na wajen Allah, amman kar ka kuskura kaje inda take. Tashi kaje"
Sum_sum Gwadabe ya fice. Yana fitowa yaci karo dasu Mammada nan fa suka ɓalle da hirar yaushe gamo. Sai da akayi sallar magriba suka samu damar shiga gida.
A daren Gwadabe ya raba tsaraba tsab ya umarci Shafa da ta shirya musu jaka zasu tafi Takai akwai meeting da za'a gabatar. Ai kuwa hakan akayi bayan ta dawo daga kaima Hadiza jakar tsarabarsu ita da yaranta sai ta shiga haÉ—a musu kaya da tsarabar Æ´an takai É—in ma.
Washegari sassafe suka kama hanyar Takai.
Sai da Hadiza ta fito tsakar gida da safe take jin labarin tafiyar tasu a bakin matan gidan. Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba a wannan ranar Hadiza tayi kukan nadama yafi cikin duro.