Sashe 211
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ya nuna mana lokacin. A daren su Gwadabe suka shirya zuwa gidan Chairman na nan Takai sun shafe tsawon awa uku cib suna meeting. Daga ƙarshe komai ya daidaita ya ɗebo kuɗi ya ba Gwadabe yace ya soma riƙewa a hannunshi na ɗinke_ɗinken suturu. Godiya sukai mishi suka yi mishi sallama. Kai tsaye Zulƙi ya kai Gwadabe gidan shugaban party na nan takai akai mishi rijistar ya zama member. Washegari Gwadabe ya je gidansu Shafa ya ɗauketa suka kama hanya dan jiya a gida ta kwana. Cikin dare sosai suka isa, dalilin da yasa Gwadabe bai je wajen malam ba kenan. Sai da safe bayan ya gama kintsawa harda jakar magungunanshi ya rataya sai ya shiga gidan har turakar Malam. Hadizan tana ciki Malam da su Baba Suwaiba sun tusata gaba anata mata faɗa harda Yaya Tasi'u da Yaya jamilu. "Yauwa Gwadabe shigo ashe ka dawo?" Cewar Malam kenan. A hankali Gwadabe ya shiga ya durƙusa ya gaishesu ɗaya bayan ɗaya kana ya nemi waje ya zauna. "Gata tunda ta dawo ake tuhumarta dalilin dawowarta dan tayi fur taƙi komawa ɗakinta. A ɗakin Asshi ta tare. Yau da safennan Sabitu ya mammaketa da ƙyar iyayensu mata suka karɓeta. Tunda dai gaka ko zaka iya faɗa mana menene ya faru?" Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke yace. "Wallahi Malam tunda dai na auri Hadiza bata barni na shaƙi iska ba. Ƙorafin yau daban na gobe daban. Lallaɓata dai kawai nake yi shi yasa ba'a jin kanmu. Wasu daga cikin manyan abubuwan da tayi kun sansu. Da yawan wanda take yi ko abokiyar zamanta bata sani ba. Nan Gwadabe ya kwashe kab irin rayuwar da suke yi ya faɗa ma Malam da musabbabin abinda ya kawo wannan matsalar da har tayi zuchiya ta kamo hanya. Salati duk mazauna dakin suka kama banda Gwadabe da Hadiza da suke kallon kallo. Sabitu ya fashe mata bakinta har ya ɗan kumbura. Kai malam ya girgiza yace. "Kayi ƙoƙari kayi zumunci, kayi kuma kawaici. Ke kuma Hadiza kin kyauta sosai da abinda kika aikata. Nayi imani da mahaifiyarki tananan da kin gama bata kunya. Gwadabe tun farko abinda na jiye maka kenan game da Hadiza bayan kayi mun bayanin Shafa. Ni ubanka ne bazan so yadda gidana yake a da inso naka gidan ya zama irin nawa ba. Sabida haka ka saki Hadiza ka huta ta huta umarni na baka. Itama sakin take so dan tayi ma Asshi rantsuwar matsawar da Shafa zaka yi tafiyarnan to sai dai ka rabu da'ita. Kuma tunda Shafa ta ciyo tafiya dole ku tafi. Ina taya ka murnar samun damar ziyartar masallacin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da zaku yi. Bata takaddarta" Ai sai kuka. Ɗakin yayi tsit baka jin sautin komai sai sautin kukan Hadiza daya cika wajen. Shin kukan baƙin cikin umarar da za'a tafi da Shafa take yi, ko kukan baƙin cikin rabuwa da Gwadabe ne, koko kukan farin cikin rabuwarne ita ta barma kanta Sani Baba Asshi tace. "Ayi haka Malam ayi tunani kar hakan ya taɓa zumunci gaba" "Babu wani zumunci da zai taɓa Gwadabe dai ɗanane, itama Hadiza ƴatace to wa zan yar cikinsu? Ai ci gaban zamansu ne zai iya raba zumuncin. Dan haka ya saketa ta tattaro mishi ƴaƴanshi ta bashi dan gidan zata bari ma" Da sauri ta ƙarasa gaban malam ta rirriƙe ƙafafunshi tana. "Kaimun rai Malam wallahi inason mijina" "Ko ki cika mun ƙafa ko in kira Sabitu dodon naki ya daka mun ke. Ai wallahi kinji na rantse aurenki da Gwadabe yazo ƙarshe. Kuma in da wannan halin zaki sake shiga gidan aure shima koroki zayyi kinga shikenan kin zama abinda kika zama." Da sauri ta saki ƙafar malam da taji ya soma kiran Sabitu. Matan Malam dai basui yunƙurin sake tausar malam ba dan sunji ya rantse sun san bazai yi kaffaraba. "Na sake ta saki ɗaya" Gwadabe ya furta a sanyaye. Malam yace. "Allah yayi maka albarka maza tafi nema abunka" Tashi yayi ya fita, da gudu Hadiza tazo ta wuceshi Ashe Yaya Tasi'u ne ya biyota da gudu suka burma ɗakin Baba Asshi. Gwadabe ne ya bisu da gudu shima. Da ƙyar Gwadabe ya kwaci Hadiza a hannun Yaya Tasi'u. Ranar dai har Gwadabe ya dawo aiki yanata aikin tunani gami da jin kunyar Malam da su Auwala. Dan yana dawowa Shafa ke sanar mishi Hadiza babu lafiya. Tare suka shirya suka je dubota daga nan suka wuce su ka yi paspo na tafiya. Kwanan Hadiza bakwai aka sallamota a asibiti. Sai lokacin Gwadabe ya durƙusa a gaban Malam yake shaida mai labarin siyasa da takarar da akeson ya fito. Da ciwon da Babala tayi. A lokacin Babala ta warke har an sallameta ma kuma Gwadabenne ya ɗauki nauyin komai da komai nata. Malam yayi murna sosai ya saka albarka a cikin lamarin ya sake da jinjina ma Gwadabe akan abinda yayi ma Babala. "Malam sai maganar Hadiza dai" "Kai ya isheka nace maka. Hadiza ko zaka dawo da'ita ka barta a yanzu ta horu tukunna. Inayin hakanne ɗomin in kawo maka ƙarshen matsalar gidanka. Hadiza in ba da gaske akayi mata ba ba zata barka ka sha ruwa ba, ka bar Hadiza taje ta yi aure a waje. Jibi ne dai tafiyarku Allah ya tsare muku hanya. Kaga sai ka roƙi Allah in wannan kujera alkhairi ce Allah ya baka, in ba alkhairi bace Allah ya maye maka gurbinta da wani babban rabon tashi ka tafi Allah yayi albarka." Tafiya Gwadabe yayi shi ba wai son zama da Hadiza yake yi ba, a_a kunyar Malam da su Mammada yake ji kawai. Bayan kwana biyu jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki. Malam ya shiga gidan ya tadda Hadiza tayi tagumi ta zurfafa a cikin tunani. Abinka da mahaifi sai yaji zuchiyarshi ta karaya. Kuma kaza tana taka ɗanta ne ba dan bata so ba. A ranshi yake hangoma Hadiza irin asarar miji da tayi dan Gwadabe guda da ɓari ne. Hadiza ta ɗago suka haɗa ido da Malam tace. "Sannu da zuwa Malam " Ko kallonta bai kuma yi ba balle ta saka ranta zai amsa mata. Tunda abun ya faru kowa ya juya mata baya a wajen Baba Asshi kawai take jin sanyi. Kullum sai ta gwada mata illar kishi mai zafi. Sabitu kuwa duk shigowa sai ya zunguri kan Hadiza kafin ya fita. Ta rame duk ta lalace decoration kuwa ƙaƙas. To bari in numfasa a han sai jibi kuma in Allah ya kai rayuwarmu.